Thursday, June 7, 2012

ZUWAN TURAWA KASAR HADEJIA KASHI NA (2)

Image Hosted by ImageTitan.comHADEJIA A YAU! A kashi na farko Na baku Labarin yanda Turawan mulkin mallaka suka yiwa Hadejia Leken Asiri.

Yanzu zamu dora! Koda yake Sarkin Hadejia Muhammadu ya samu labarin Turawa sun ci Kano da Katagum duk sun koma karkashin mulkinsu yace da yabi Kafiri Gara yayi shahada. Turawa basu fasa ba shima bai fasa ba.

Ranar Talata 1906 Turawa suka shigo Hadejia Gadan gadan akayi ta gwabza fada. to dawakan Hadejia basu taba jin kukan Igwa ba da sunji wannan kukan sai su turje haka nan akayi ta fama da su. jama'ar Hadejia manya da yara kowa yayi shirin yaki haka nan akayi yaki har Zuwa La'asar kuma Turawa suna kara shigowa Hadejia, saboda makaman su ba irin namu bane. An kashe manyan fadawan Hadejia da hakimai:

kamar yanda na fada a baya Sarkin Hadejia Muhammadu saida Mahaifiyarsa tace masa Kada Hadejia ta kare saboda kai. Tukuna ya rusuna har Turawa suka cim masa. Allahu akbar! koda Hadejiawa suka samu labari an kashe sarki sai kowa ya Rusuna. Turawa suka shigo Hadejia suka Fara shirin tafiyar da mulki irin nasu. Hadejiawa sukayi Jana'izar wadanda suka mutu, wadanda kuma sukaji rauni aka kaisu Gidajensu. Turawa suka Nada Sarkin Hadejia Haru mai karamba 1906. To akwai sarkin yaki cilin Yana daga cikin wadanda suka samu raunuka a yakin kuma shi Captai phillips ya sanshi dama can. to kullum sai yaje Gidan sarkin yaki Yana Masa Izgilanci yana ce masa ina yakin? Ashe Sarkin yaki yana jin ciwon hakan. Wata rana sai yacewa matarsa Idan zata Kawo masa Abinci tasa wuka a cikin Tuwon.

haka kuwa tayi. saida captain phillips yazo yana masa Izgili Sai yasa hannu kamar mai cin tuwo sai ya dauko wuka ya Burmawa captain phillips a tumbinsa ya kasheshi. Kabarinsa yana can a Gabas Da Bariki Hanyar Tandanu. Shi ake cewa Kabarin mai tumbi. Wadanda suka rasa rayukansu a yakin suna da dama Amma ga kadan daga Sunayensu. Muhammadu Sarkin Hadejia, Madacima shi suka fara kashewa, Galadima, Ma'aji salihu, Furya, Barwa da Tarno, Bori na Salihu, Kaura Amadu, Mabudi zakar, Jarma warkaci, Sabo jikan Tete, Dandalma, Abdulwahabu sarkin Baka, Sarkin Arewa, Alkali, Farau farau, Sarkin Dawaki Dan gazau, Da dai Sauransu! Allah yaji kansu da Rahma. HADEJIA A YAU.

No comments:

Post a Comment