Wednesday, June 27, 2012

TARIHIN SARAUTAR SARKIN HADEJIA NA (16)

Image Hosted by ImageTitan.com

Sarkin Hadejia, Zan baku Tarihin Sarautar sa
zuwa Yau!
Ranar Asabat 3-january-1999, Mai martaba
sarkin Hadejia Alh. Abubakar Maje Haruna ya
Nada Alh. Adamu Abubakar A matsayin IYAN
HADEJIA, NA FARKO. Kuma Ranar Laraba 11-
september-2002, Allah ya yiwa Mai martaba
Sarkin Hadejia Rasuwa. Alh. Abubakar maje
Haruna.
TO A SAKAMAKON AMINCEWA DA GWAMNATI
TAYI DA ZABEN 'YAN MAJALISSAR SARKI WATO
(KING MAKER'S) Suka zabi Iyan Hadejia Alh.
Adamu Abubakar maje a matsayin sarkin
Hadejia, Na Goma sha shida (16). kuma an
nada shi Ranar Asabat
14-september-2002. Bisa Al'ada ba'a kwana
uku ba tare da an nada Sarki ba.
KUMA HAWANSA NA FARKO A MATSAYINSA NA
SARKIN HADEJIA SHINE Hawan sallar Azumi
wato A watan Disamba 2002. Sannan sallar
Layya February 2002 Bai Hau ba saboda yaje
Saudiyya.
29-March-2003.
A YAU ASABAT 29-March-2003 ANYI BIKIN
BADA SANDA! An baiwa sarkin Hadejia Sanda
a Karkashin shugabancin Gwamnan Jigawa
ALH. IBRAHIM SAMINU TURAKI! A STADIUM TA
HADEJIA.
Kuma bayan an Bashi Sandar jagorancin
Kasar Hadejia A karkashin Tutar Shehu
Usman Dan fodio, Mai martaba sarki yayi
Hawa Guda Uku Wadanda suka Kayatar da
jama'ar Hadejia.
1, BIKIN GASAR ALQUR'ANI A SECONDARY
FANTAI
2,TARON DA AKAYI A MAKARANTAR KOFAR
AREWA
3,SAI HAWAN GANDU WANDA SHIMA YANA DA
TARIHI A MASARAUTAR HADEJIA.
Kuma Hakiman da ya fara Nadawa sune 1,
DAN GALADIMA Alh.babbaji Adamu Hakimin
waje 2, SARKIN DAWAKI Alh. Umar Ibrahim
Hakimin kiri kasamma.
3, KATUKAN HADEJIA NA (2) BIYU Hakimin
Turabu. A gaba zan kawo muku Labarin
Fitar sarkin Hadejia Rangadi da yayi da kuma
Hakiman da a Nada.

6 comments:

  1. Sarkin Hadejia magajin sambo allah ya ja zamanin sarki.

    ReplyDelete
  2. Allah ya karawa Sarki lafiya. Allah yaja zamanin Sarki.

    ReplyDelete
  3. Babangida No-fighting HadejiaAugust 20, 2012 at 10:06 AM

    Allah ya karawa maimartaba sarki lafiya.

    ReplyDelete
  4. Salam alaikum. Munajin dadin wagga shiri kwarai da gaske. Kuma muna rokon da a Bamu full tarihin daya daga cikin tarihin hakiman da sukai shahada da sarki Muhammadu. Wato madakin hadejia ahmadu kaura. Da kuma Ina descendent dinshi a yau?

    ReplyDelete