Sunday, June 17, 2012

WASIKA DAGA AJI KIMA ZUWA GA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR HADEJIA

Free Web Proxy
Budaddiyar wasika ga mai girma shugaban karamar shukumar Hadejia da yan majalissarsa.
Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci, ina mai farin
cikin rubutoma wannan takardar domin in nuna irin
goyan baya da nake bawa wannan jam'iya da wannan gwabnatin mai albarka, bayan haka ina jinjinama bisa irin kokarin da kake wajen ciyarwa da
wannan karamar hukuma gaba. Ina sake jinjinama da yadda kake gudanarwa da mulkinka cikin
kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Bayan haka ina so nayi amfani da wannan damar na tunatar da kai wasu muhimman abubuwa
wanda idan kayi su zasu taimakama wajen samin sahihiyar
hanyar ci gaba da kuma adana tarihi ko bayan
ranka, wannan abun kuwa sune kamar haka.
Kasancewar garin hadejia babban gari ne mai tsohon tarihi a jeri garuruwan Hausa to ya kamata
ace yau akwai abubuwan da zamu yi alfari da su wajen tarihi kamar yadda ya'u idan kaje Daura zaka tarar da abubuwan da suka faru shekaru dari uku ko hudu
da suka shude kamar yau akayi su.
Ma'ana muma a garin Hadejia muna da irin guraren
nan kamar kabarin mai tumbi, kofar mandara, ruwan Atafi, Rijiyar turawa, mabuga, majema, marina, bariki da sauransu.
Kuma ya kamata ana tunawa da mutanan da suka bawa wannan gari gudunmawa misali saka
sunayensu a titinah,dakin taro makarantu dasauransu. mutane irinsu Alh Haruna uji ya kamata a
na tunawa dasu, amma abin al'ajabi aka saka sunayen mutane a titinah aka manta da Haruna
uji, wanda ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen daukaka masarautar hadejia.
Saboda haka a madadin daliban Hadejia emirate ina
mika wannan sakon ga maigirnma shugaban karamar hukuma da fatan za'a duba. Nagode.
Comrade Aji kima hadejia secretary general Hadejia student Association.

7 comments:

  1. Aji kima ai kune makusantan gwamnati, ku zaku fada musu su yarda. Allah yasa suyi la'akari da wasikarka.

    ReplyDelete
  2. Gaskiya ne! Aji kima ka cika dan siyasa.

    ReplyDelete
  3. Aji kima ya kyauta! Allah yasa chiyaman ya dauki wannan shawarar.

    ReplyDelete
  4. mudai talakawan hadejia tsakaninmu da masu mulki sai allah ya isa, domin sunki yimana magani ambaliyar ruwan damuna, tahanyar yashe magudanan ruwa, ciko, gina filaye masu tara ruwa.

    ReplyDelete
  5. Allah yasa gwamnati taji koken Jibrin Abubakar. ta mana maganin Ambaliya.

    ReplyDelete
  6. Allah ya basu ikon gyarawa. Kamar yanda Jibrin ya ambata.

    ReplyDelete
  7. To muna rokon Allah ya gyara mana shugabanninmu. Ameen

    ReplyDelete