Rahotanni daga Damaturu babban
birnin jihar Yobe dake Arewacin
Najeriya, sun ce mazauna unguwanni
da dama ne suka tsere daga gidajen
su, yayin da wasu karin suka
kauracewa unguwannin su domin
samun mafaka.
Wannan dai ya biyo bayan tashin
bama bamai da karar bindigogin da
aka rika ji ne ba kakkautawa a
yammacin yau.
Rundunar Hadin Gwiwar Samar da
tsaro a jihar Yoben ta tabbatar da
abkuwar lamarin, sai dai ba ta
bayyana adadin asarar rayuka da
jikkata da aka samu ba a sakamakon
wannan hari.
Harin na Yoben dai na zuwa ne
kwana daya bayan wasu hare haran
kunar bakin wake da aka kai kansu
coci-coci uku a garin Kaduna da
kuma Zaria.
Hare haran da kungiyar Ahlisunna
lidda'awati wal jihad da ake kira
Boko Haram suka yi ikirarin kaiwa.
No comments:
Post a Comment