Thursday, June 7, 2012

ZUWAN TURAWA KASAR HADEJIA 1906 (2)

Image Hosted by ImageTitan.comHADEJIA A YAU! A shekarar 1906 Turawan mulkin mallaka suka ci Hadejia da yaki, Inda yayi sanadiyar mutuwar mutanen Hadejia da dama da kuma Turawan. kafin wannan Turawa sun shigo Hadejia ne bayan sun ci Katagum da yaki, koda yake ba yaki sukayi da Katagum ba, sun Meka musu wuya ne.

kuma Turawan sun shigo Hadejia ne ta Iyakar Hadejia da Katagum, Inda sukayi sansani a Mai Goriba kusa da Masama. To basu shigo Hadejia ba sai da suka turo Dan leken Asiri wanda ya shigo Hadejia a Matsayin Balarabe mai saida kayan Sarauta Irinsu Alkybba da sauransu. kuma an saukeshi a Gidan Zangoma Wato sarkin Baki.

kuma a haka yayi ta Kewaya Hadejia har ya gane duk sirrin Garin Haka kuma yana kaiwa Sarki kaya yana saye har yasan Sirrin fadar Hadejia.

Wannan dan leken Asirin da yayi shigar Balarabe shine Captain H. C. B. Phillips, Wanda ake ce masa (Mai Tumbi). Kuma kafin suzo Hadejia an basu labarin Garin da kuma Mayakan garin, dan haka shi Captain phillips ya dinga bin Gidajen Jarumai yana Musu alheri a Matsayinsa na dan kasuwa, hakan tasa ya shiga jikinsu sosai kuma suka Amince dashi.

No comments:

Post a Comment