Sunday, June 17, 2012
KOWA YA GYARA YA SANI
HADEJIA A YAU!
Assalamu Alaikum! Bayan gaisuwa da fatan
Alkairi Ga 'yan wannan Masarauta, Muna
kara godiya ga Allahu subhanahu-wata'ala
da ya bamu ikon Rubuta wannan wasika.
Domin da Ikonsa ne Komai ya kasance da
kuma abinda zai kasance! Bayan haka Ina
kira ga shugabannin Hadejia da su taimaka
su Inganta mana Muhimman guraren
Tarihinmu na kasar Hadejia. Sakamakon
Lalacewa da suke kokarin yi. Kamar Tsohon
Gidan yari, Gulbin Atafi da Ramin zaki, bariki
wato Gidan Rasdan da na D.O., kabarin
Captain H.H. Phillips wato Mai Tumbi, Kofar
Kudu (chediyar kyalesu) da kuma kofar
Gabas. Wani mutum yazo daga BIDDA ta
jihar Niger yace min Yana so na kaishi
Kabarin Captain phillips, sai nayi shiru Ina
tunanin wanene captain phillips? Sai na tuna
lokacin muna yara In munje kanya muna
zuwa kabarin Mai tumbi. Kuma a jikin
kabarin an rubuta captain H.H.phillips! Sai
nace masa Muje ko da mukaje sai na fara
Gabatar masa da Bariki cewa a nan Turawa
suka fara zama. Sai yace dani A'a ai sun
Zauna a can Gaba kafin suzo nan. Nace Eh
hakane. Koda mukaje Kabarin Mai tumbi sai
muka ga Ginin duk ya rushe kabarin yana
nema ya bata. Sannan sai yayi kira ga
Hukumomi su rinka kawata Guraren Tarihi
Irin wadannan. To muma muna kira ga
wadanda abin ya shafa da su Gyara guraren
tarihi ba sai kabarin Mai tumbi kawai ba.
Sannan yace In kaishi Fantai Inda Gidajen
Sarakunan Habe suke. Ko da yake munje
Amma bamu samu Dagacin Mandara a gida
ba amma mun Dauki Hotunan Gidajen nasu
da kuma Tsangayar Gwani Gambo a cikin
'Yankoli. Sannan Muka Zarce zuwa Mai-
Rakumi mukayi Ziyara ga kabarin Sarkin
Hadejia Sambo. Bayan mun dawo Mukayi
sallama da Bako ya wuce Gogaram Ta Bade
Yace daga nan Zaije har Ngazargamu. Nace
Allah ya kiyaye hanya. Sannan sai na fara
tunani Ashe tarihi yana da muhimmanci? Sai
na tuna Ai malamin History yace:- History is
the systematic Account of past and present
Event. Zan baku Karashen Labarin anan
Gaba. Hadejia A yau.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Wannan Gurbin ina ne? Na kasa Gane wace Unguwace. Daga Ibrahim Ahmed mai kanwa.
ReplyDeleteNan kofar Garin kudu ce! Wato Cediyar kyaleta. Ko kofar Kogi.
ReplyDeleteMuna so a bamu tarihin kofar yamma da kofar Arewa. Kuma Allah ya kara basira.
ReplyDelete