Tuesday, October 9, 2012

TARIHIN SARKIN HADEJIA UMARU DAN BUHARI (1863-1865).

Image Hosted by ImageTitan.com
HADEJIA A YAU!
SARKIN HADEJIA UMARU: A SHEKARAR 1863 allah ya yiwa Sarkin Hadejia Buhari rasuwa a Yakinsu da sukayi da Gogaram (Bedde). Ko da aka dawo Hadejia aka binne shi sai Manyan fadawan Hadejia wadanda akwai Amana tsakaninsu dashi Buhari.
Kamar SARKIN AREWA TATA
GANA DA KUMA
SARKIN YAKI JAJI suka jajirce Sai an Nada UMARU DAN BUHARI SARKIN HADEJIA. kuma hakan Akayi!

SARKIN HADEJIA UMARU NA BIYU a nadashi yana da shekara Goma sha Bakwai. Kuma manyan fadawan Mahaifinsa sune suke gudanar da Sarautar tunda shi yaro ne. Kuma a zamaninsa Sarkin Damagaram Tanimu ya kawo yaki Hadejia. Kuma yayi sansani a Arewa da Hadejia daga nan har Jigawar Kasim mutanensa ne. saida yayi kwana Arba'in
ana yaki
amma Hadejiawa basu fasa wasanninsu
na dandali ba.
Wata rana ana yaki Sai aka harbi dokin
Sarkin Arewa!
Koda ya mutu sai akaje gida aka dauko
wani Dokin aka
cire kayan wancan Dokin aka sakawa
wanda aka kawo.
Tata gana ya koma kan doki, kashe gari
ana cikin yaki
sai Tata gana ya sauko daga Dokinsa
yayi alwala ya
koma kan Dokin, to ashe Sarkin
Damagaram yana
kallon su sai yace Lalle Sarkin Hadejia ya
Isa ana yaki ka
sauko kayi alwala? Jiya ma an kashe
masa Doki amma
saida akaje aka dauko wani a gari? Sai
Zagin Sarkin
Damagaram yace ai ba Sarkin Hadejia
bane Yaronsa ne!
Sai Sarkin Damagaram Tanimu yace to
Ina Sarkin
Hadejian? Sai zaginsa yace ai ance yana
gida tunda aka
fara yakin nan bai taba zuwa ba. Sai
sarkin Damagaram
yace wa fadawansa Gobe zamu bar
Hadejia kar mu
tsaya ayi ta kashemu. Saboda Sarkin
Hadejia ya raina
mu kwananmu Arba'in amma bai taba
zuwa anyi yaki
dashi ba? Wa yasan me zai mana in ya
zo? Amma basu
san Sarkin Yaro bane. Washe gari suka
juya suka koma
Damagaram.
Kuma lokacinda sukazo Hadejia Da kaka
ne! Anyi girbi Manoma basu gama Tare
Amfaninsu ba.
Shi yasa suka dade a Hadejia saboda
akwai abinci da
ruwa a kusa dasu. SARKIN HADEJIA
UMARU Mutum ne
mai son Nishadi kowane Lokaci yakan
fita Bakin kogi ko
Gona Domin Debe kewa. Kuma anyi
amfani da wannan
Damar inda wata rana ya fita sai aka
Rufe Masa Kofa.
Koda yazo yaga kofa A rufe sai ya juya ya
tafi Chamo
ya zauna. Aka nada Kanin Mahaifinsa
Sarkin Hadejia
Wato HARU BUBBA. 1865-1885. Shi
kuwa UMARU DAN
BUHARI yayi zamansa a Chamo kuma Ya
rasu a
shekarar 1920. Allah yaji Kansu Ameen.
HADEJIA A YAU

1 comment: