Wednesday, March 21, 2012

TARIHIN HADEJIA A TAKAICE!

HADEJIA A YAU - TARIHIN KAFUWAR HADEJIA Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, shi dai wannan Mutumi Maharbi ne kuma yana yawon farautarsa ne ya taho yankin Hadejia. Kuma a yawon farautar da yakeyi ne wata rana yana tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo har tazo bakin Kogin hadejia, bayan ta sha Ruwa kuma ta shiga ta jika jikinta. ko da tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi mamakin hakan har ma sai yabi sawunta. Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye suna shawagi a gurin. Sannan kuma ya rinka jin kukan Namin Daji, Sai ya yanke shawarar zama a wannan gurin, kuma hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa yake harbe harben Namun daji kuma yayi su wato kamun kifi. In ya kashe namun daji sai yaje ya sayar da fatun. Da kuma Naman. Harma ya dauko Matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan gurin. Koda maharba 'yan-Uwansa suka ga Gurinda yake akwai Namun daji da abubuwanda suke bukata sai sukayi shawarar suzo su zauna dashi, sai gurin ya zama Gari Kuma mutane suna zuwa sayen fatu da naman dabbobi a garin. Duk wanda yazo garin sai yayi sha'awar zama a gun, haka nan gari ya fara bunkasa wasu maharba, wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada zango a garin. To kasancewar gari sai da shugabanci ne yasa shi Hade ya zama shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu ko nama sai yace na tafi garin HADEN-JIA. Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. To sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia. Kuma bayan zamanin wannan mutumin Hadejia taci gaba da zama gari a Karkashin Daular Biram (Garun Gabas) kuma Sarkin Gabas shine ya Nada Dan-uwan Sarkin Machina Algalfhati ya zama shine Sarkin Hadejia, Shekaru da Dama bayan Hade ya Mutu. Wadannan sune Sarakunan Habawa. Kuma a lokacin akwai kananan Garuruwa masu cin gashin kansu kamar Rinde, yayari, wunti, Anku da dai sauransu. Wadanda suma suna da nasu sarakunan a wannan Lokacin. Amma yanzu duk unguwanni ne a cikin garin Hadejia. Kuma Hadejia sunyi sarakunan Habe guda talatin da biyu(32) amma sunan mutum uku ake dasu wadanda sukayi mulki kafin zuwan Fulani. 1, BAUDE 2, MUSA 3, ABUBAKAR. Kuma a lokacin Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin Hadejia tana karkashin Daular Borno, kuma ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman dan fodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune suke sarautar Kasar Hadejia.

A GABA ZAN KAWO MUKU TARIHIN SARAKUNAN FULANI DA DALILIN KARBAR TUTA DA YADDA SUKA TUNKUDE SARAKUNAN HABE DAGA SARAUTA.

No comments:

Post a Comment