Tuesday, February 21, 2012

WAKOKIN MALAM AMADU DAN MATAWALLE HADEJIA!

AMSHI- Hakane malam Amadi na idi ka sake shiri duniya ta Allah ce malam Amadi.


1, Ku saurara jama'a zana baku labarin wani shi hakimi wanda bazai iya saukarmu ba.


2, Akwai wani dan sarki anyi mar sarauta shi buri ya cika, gaba daya ya baza yaran gidansu bubba da yaro duk sun tafi.


3, Naje kasarsu na samu hakimi wani mai siffar mujiya, da fadawa da mutanen gari suna ja mar Allah ya isa.


4, Jemage ba tsuntsu ba yai kamar tsuntsu sai halin tsiya, ga tsuntsu da hakora kamar mutum ni ban gane kanka ba.


5, Agarnana masu kahonnin karo, mai zafin rayi sai kace na karya in taso haihuwa.


6, Wanda tuwo yafi karfinsa in ya samu tuwo shima sai yaci, wannan in aka tuka ka bashi tare da fadawan zasuci.


7, Yautai dan yawon duniya, shi aka baiwa sarauta ya kama mulki bai san girmansa ba.


8, Ungulu komai namanki ne, ya hana 'yan mata dan irin wasan nan da ake dandali.


9, Bera mai ta'adin gayya shi haram da halak ma bai sansu ba.


10, Yautai dan yawon duniya, ya shiga tsuntsaye 'yan uwansa an rasa mai ganewa dashi.


11, Kyawun dan sarki ai a sanshi mai kyauta ga mutanen gari.


12, Shi gogana ai nasuma yake karba yayi chacha dashi.


13, Ai ni in baka ban naka ba, nawa fa shima ba naka ba.


14, Dumau nake ba fashi ko cikin sa'a daya bani da dadin gamo.


15, Bangon dutse in kaki masu sarawa da diga sa gaji.


16, Shaho birkita kaji na sidi malam baka da dadin gamo, bauna wanda ya dosheta babu maduhu sai wani ba tasa ba.


18, Tamat wa bi hamdu ilallahi zan yi ban kwana waka ta cika.



DAGA ISMA'ILA A. SABO HADEJIA.

No comments:

Post a Comment