Friday, February 10, 2012
HADEJIA A SHEKARUN BAYA!
Hadejia a yau! A shekara arba'in da ta Gabata Hadejia tana da masallacin juma'a guda daya ne, wato masallacin cikin gari. wanda kuma ana zuwa sallar juma'a daga kauyukan kusa da Hadejian a wancan shekarun. kamar Kadume,Arawa,Yamidi,Ganuwar kuka,Hadin mai dan karofi, da sauransu. Da yake zamani juyawa yake kuma jama'a karuwa suke yau a Hadejia akwai masallatan juma'a kusan goma wanda kuma duk wanda kaje kai kace duk jama'ar garin suna can ne. To muna kara godiya ga Allah wanda da ikonsa ne komai yake gudana. Allah ya karo mana alkairi da zaman lafiya. a gaba zan baku labari akan kasuwar Hadejia duk a filin Hadejia a yau.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Hakane! Zamani mai canjawa.
ReplyDeleteit is great
ReplyDelete