Wednesday, February 22, 2012

TARIHIN SARKIN HADEJIA HARU BUBBA

Sarkin Hadeji Haru bubba shine Mahaifin Sarkin Hadejia Muhammadu mai Shahada, wanda a zamaninsa Turawa sukaci Hadejia da yaki. Sarki Haru bubba Malami ne kuma mutum ne mai son zaman lafiya, kuma shine ya gina Masallacin juma'a Na Hadejia. Kuma a zamaninsa Gumel sukayi yaki da Hadejia, wato lokacin sarkin Gumel Abdu jatau. Sarkin Gumel ya aikowa Sarkin Hadejia zai wuce ta kasarsa wato ta kudu a gayawa Talakawa kada su tsorata bazai taba kowa ba. To amma koda yazo wucewa sai ya saba Alkawari don yana sawa ana debe kayan talakawan ana kaiwa Gumel. Koda Sarkin Hadejia ya samu labari sai yasa akayi sirdi aka fita, a wannan yakin aka kashe sarkin Gumel Abdu jatau. Galadiman Hadejia yakuba shine ya sareshi. Dama sarkin Gumel yayi mafarki bazai koma gida ba. Sai ya fadawa kaninsa Abubakar in ya mutu to a kaishi Gumel ayi masa jana'iza, kuma hakan akayi. Kuma a zamanin Sarkin Hadejia Haru ne Dansa Muhammadu Yayi yaki da Maguzawan Mada Rumfa ta Sokoto, inda sarkin musulmi ya masa sarautar Sarkin yakin Sarkin Musulmi. Kafin ya Zama Sarkin Hadejia. Allah yaji kansu.

No comments:

Post a Comment