Saturday, December 20, 2014

ZIYARA DA AMFANINTA.

a.

r">
Ziyara wani Nau'i ne na zumunci wanda mutane suke aiwatar da ita domin sada zumunci ga 'yan'uwa da abokan Arziki. zumunci wata irin halayya ce ta kwarai wacce ke sadar da dangantaka ta nasaba tsakanin ’yan'uwa ko bare. Zumunci ne ke kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da fahimtar juna tsakanin al’umma.

Ta hanyoyin da mutum zai bi ya inganta zumunci shine, kaiwa ziyara ga 'yan'uwansa kamar kaka, uba kokuma kanin mahaifi ko kanin mahaifiya da sauransu. Ta haka ne mutum zai gane irin yadda Alaqarsa take da 'yan uwansa na nesa ko na kusa. Haka kuma kowa yana da iya kimar zumuncin da zai gudanar a tsakaninsa da wani. Kamar yadda Hausawa suka ce zumunta a kafa take, to wannan gaskiya ne,domin
kuwa daya daga cikin manyan ginshikan zumunta shi ne ziyartar juna. Idan ka kula da zumunci shike sa mutum ya niki gari zuwa gidan abokinka ko wani dan'uwanka, ko bare musamman domin ganin yadda yake. Wannan ziyara kawai, ita ke haddasa kauna da mutunci mai dorewa a tsakanin al’umma.

A shekarun baya kamar shekara kamar goma zuwa sama,saboda muhimmancin ranar Juma'a,iyaye sukan je da 'ya'yansu gidajen 'yan'uwansu da Abokan Arziki domin gaisawa wanda hakan yana nuna ana nusar da yara ne da kaiwa ziyara ga 'yan uwansu. Harma yara suke kiran wannan ziyara da yawon Juma'a. Amma saboda shagaltar da zuciya irin ta shaidan tasa wannan kyakkyawan Aiki na ziyara ya fara ja baya ga yara harma da manyan a wannan zamani,domin shi bubba yana tunanin ai in yaje zai bada kudi, sannan yaro yana tunanin kar yaje ba'a bashi kudi ba.

Wednesday, December 3, 2014

TAKAITACCEN TARIHIN HASHIM UBALE YUSUF..

Hadejia A yau!

An haifi Hashim Ubale Yusufu a Garun Gabas da ke cikin yankin Karamar Hukumar Mallam Madori ta yanzu, A ranar 21 ga Satumba na shekarar 1956. Ya fara karatunsa a makarantar firamare a nan Garun Gabas inda ya fita da kyakkyawan sakamako a matsayin dalibi mafi kwazo da hazaka Daga nan ya wuce zuwa Sakandaren gwamnati dake Birnin Kudu inda ya yi karatu daga 1969 zuwa 1973, lokacin da ya rubuta jarrawar makarantun sakandare ta Afirka ta Yamma wato WASC.

Ya halarci Makarantar Koyon ilimi mai zurfi ta Kano, wato College of Advanced Studies daga 1973 zuwa 1975, inda ya fita da babbar takardar shaida, wato Higher School Certificate. Daga nan kuma ya sami shiga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya yi karatun digiri a fannin ilimin harhada magunguna (wato pharmacy) wanda ya gama a shekarar 1981.Bayan ya kammala karatun jami-a, sai sai ya tafi aikin bautar kasa a jihar Imo inda aka tura shi Federal Polytechnic da ke garin Afikpo -Okposi inda ya yi aiki a matsayin mai bayar da magani na wannan makarantar da kuma koyar da darasin chemistry daga 1982 zuwa 1983.Hashim ya fara aiki tun daga matakin karamin ma'aikaci inda a tsawon shekaru ya taka matakai daban daban har zuwa matsayin darakta a hukumar kula da tsaftar abinci da magunguna a Nigeria, da kuma bubban sakatare wato permanent secretary.

Ya fara aiki a shekarar 1974 a matsayinsa na Mataimakin Jami'in gandun daji a karkashin sashen kula da gandun daji na tsohuwar Jihar Kano, sannan daga bisani ya canja aiki zuwa bubban Asibiti na Kano (wanda aka fi sani da asibitin Murtala a yanzu) inda yayi aiki amatsayin jami'i mai bada magani na wucin-gadi a cikin shekarar 1981 da 1982, inda kuma a shekarar 1983 aka daukeshi aiki a karkashin Sashen Kula da ayyukan lafiya kuma aka tura shi Asibitin Murtala da ke Kano a matsayin Jami'in bayar da magani mai daraja ta daya. Daga 1985 zuwa 1987, ya yi aiki a cibiyar sayar da magani ta Lafiya Pharmacy dake garin Hadejia, wadda ta kasance daya daga cikin cibiyoyin sayar da magani da aka bude a wancan lokacin. Bayan daukar lokaci yana aiki karkashin gwamnati,sai ya tsallaka zuwa ma'aikatu masu zaman kansu inda ya yi aiki a kamfanonin sayar da magunguna na NAMCO da kuma ANHEL das u ke cikin binin Kano daga 1987 zuwa 1989. Haka nan ya yi aiki a da hukumar bada tallafin cigaba ta kasar Amurka wato USAID a matsayin jami’in gudanar da ayyuka na kasa karkashin shirin Inganta Lafiyar Iyali (wato Family Health Services).

A shekarar 1989, ya rike mukamin Mai bada shawara a gandun daji na tsohuwar Jihar Kano, sannan daga bisani ya canja aiki zuwa Babban Asibiti na Kano (wanda aka fi sani da asibitin Murtala a yanzu) inda ya yi aiki a matsayin jami'i mai bada magani na wucin-gadi tsakanin 1981 da 1982, inda kuma a shekarar 1983 aka dauke shi aiki karkashin Sashen Kula da ayyukan lafiya kuma aka tura shi Asibitin Murtala da ke Kano a matsayin Jami'in bayar da magani mai daraja ta daya.

Wednesday, October 29, 2014

HADEJIA TOWN WALLS AND GATES.

BY: SULEIMAN GINSAU HADEJIA A YAU!HADEJIA TOWN WALLS AND GATES "Hadejia was a large town with 5 town gates and excellent walls about 30ft (9.14m) high, and 30ft (9.14m) thick " (Captain Philips 1909)

Hadejia Town walls had a long history dating back to the pre-jihad period. The walls were built to provide security to the people, and to serve as fortification against external invasion. Though mostly in ruins now, with a great proportion having completely disappeared, the walls were intact up to the time of the colonial invasion in 1906. Hadejia A yau!

The construction of the walls was done by direct labour using local building materials. Over the years, the walls have been taken subjected to several phases of development. Expansions and reinforcements were made to accommodate a growing population or to enhance security against attack by powerful enemies. The walls were invariably complimented by gates whose history could be linked to that of the walls. The gates provided the only entry points into the town. They were made extremely strong, thus making it very difficult for an enemy force to break into the town through them. Hadejia A yau.

The gates were manned by gate-keepers or porters (sarakunan kofa) appointed by the Emir. These keepers used to close the gates everyday from dusk to dawn, thus controlling the movement of people in and out of the town during these periods. Visitors or strangers were not allowed in unless with the express permission of the Emir. It was reported that one Emir ordered the gates to be left open permanently, confident that no enemy force would dare attack the town.

The first town wall in Hadejia was believed to have been built during the pre-jihad period. Though the exact date of its construction cannot be determined due to lack of proper records, its perimeter is marked by certain well-known local pits: Mai kilabo in the west, Atafi in the south, and Dallah in the East. It was said to be one mile in circumference, and had four gates. The second wall was built by Sarki Sambo in the early years of the Jihad. It was wider than the previous wall, with its perimeter approximately put at 2 miles 170 yards. It had 5 gates. The present wall, which was the third, was also built during Sambo's reign. It was built at a time when Hadejia was at the centre of a bitter rivalry between Sokoto caliphate and Borno Empire. As such it was much stronger and wider than the previous walls. An extension to this wall was later made on the Eastern side during the reign of Sarki Haruna (1865 -1885) encompassing a large space to harbor fugitives from surrounding villages in times of war.

The Habe settlement of Fantai, which hitherto was outside the wall, also became sheltered in the new extension. This brought the wall to its present size of 4miles 135yards, with 5 gates, namely:
Kofar Gabas (also known as Kofar Gwani) Kofar Arewa KofarYamma Kofar Kyalesu (also Known as Kofar Kogi) Kofar Mandara (also known as Kofar Talata) Apart from the Kofar Mandara gate, which was destroyed by the British in their attempt to gain entry into Hadejia town in 1906, the other gates are still standing in their original positions.

They have, however, undergone several modifications over the years, the latest being in1985 which saw the total re-construction of Kofar Arewa and Kofar Yamma. The Hadejia town gates now stand as historical monuments rather than as security outposts. HADEJIA A YAU BY: SULEIMAN GINSAU -- Sent from A. Sabo note fad. HADEJIA A YAU!

Monday, September 29, 2014

TARIHIN RAYUWAR GALADIMAN KANO A TAKAICE! Alhaji Tijjani Hashim.

Hadejia A yau!<p>An haifi Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim a cikin garin Kano, a shekarar 1932. Mahaifinsa shine Turakin kano Hashim dan sarkin kano Abbas jikan sarkin Kano Ibrahim Dabo. Ya fara karatun Elementary  a garin Bebeji a cikin shekarar 1944. sannan ya shiga makarantar Middile ta Kano inda ya kammala a  shekarar 1951.

A shekarar 1952 Galadiman kano ya fara aiki a  hukumar N. A. (Native Authority) ta Kano a matsayin Malamin Dabbobi, mai kula da tsafta da lafiyar dabbobi. A 1956 aka zabe shi  a matsayin dan majalissa mai wakiltar Sumaila a majalisar dokoki ta Arewa dake kaduna.

A zaman sa a wannan majalisa ne ya rike mukamai da dama ciki har da shugaban hukumar bada kwangila ta Kaduna sannan ya rike shugaban kwamitin tabbatar da jamiyyar NPC ta lashe zabe a lardin Sardauna. Sannan ya rike mukamin Ministan Ayyukan cikin gida na Jihar Arewa. Yayi Kwamishinan lardi mai kula Lardin Kabba wandda yana kan wannan mukamin ne sojoji suka yi juyin mulki.

Bayan ya dawo gida sai  Sarkin Kano Ado Bayero ya nada shi sarautar Dan-isan Kano kuma kansila mai kula da ayyukan gayya da taimakon kai da kai.

A cikin shekarar 1976 ne ya samu karin girma zuwa sarautar Turakin Kano da bashi kulawa da gundumar Kumbotso. sannan A 1980, ya sami canji zuwa kansila marar ofis saboda yawan  harkokinsa na kasuwanci. A shekarar 1989, ya samu karin girma zuwa sarautar Dan-iyan Kano, kuma ya ci gaba rike mukamin kansila marar ofis.

A shekarar 1992, ya samu karin girma a sarauta inda aka nadashi Galadiman Kano kuma shugaban kwamitin kudi na majalisar Sarki. A shekarar 2012 Sarki ya kara masa aikin hakimcin birnin Kano. Wannan aiki ya ke rike dashi har Allah ya masa rasuwa.

Galadiman Kano Tijjani mutum ne mai hakuri da juriya da Alkairi. Kuma yana da daraja a Idanun mtane sakamakon amfani da yayi da damarsa ya kafa mutane a Gwamnati. kuma babu inda zai nemi Alfarma a gwamnati bai samu ba, wannan tasa ake masa Laqabi da GAJERE WAN GWAMNATI.

A ranar28/september/2014, Allah ya yiwa Galadiman kano rasuwa ya rasu ya bar 'ya'ya da Matan Aure da 'yan-uwa da dama. Muna Addu'a Allah ya gafarta masa.

Friday, August 15, 2014

Thursday, March 20, 2014

TARIHIN SARAKUNAN FULANIN HADEJIA (Kashi na daya 1)

TARIHIN SARAKUNAN FULANI A HADEJIA...



BISMILLAHIRRAHMANIR'RAHIM.

. Kamar yanda aka sani kasar Hadejia ta koma karkashin mulkin fulani bayan da suka hambarar da mulkin Habawa a karni na goma sha biyar (15). Fulani sun shigo kasar Hadejia ne a farkon karni na goma sha biyar (15), a karkashin jagorancin Ardo Abdure dan Jamdoyji, sun fara zama ne a Jarmari kusa da garin Hadejia, har tsawon wani lokaci. Bayan rasuwar Ardo Abdure a shekarar (1788) sai Dansa Sarkin fulani Umaru ya yanke shawarar su dawo Rinde da zama, yamma da garin Hadejia. kuma Sarkin Hadejia na Habe Abubakar ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia a cikin karni na goma sha takwas (18).

SARKIN FULANI UMARU... Shine sarki na farko a jerin sarakunan fulanin Hadejia, kuma a lokacinsa aka samu labarin jihadin Shehu Usman Danfodiyo. A lokacinda sarkin fulani Umaru yaji labarin jihadin shehu sai yayi shawara da 'yan uwansa da suje suyi Mubaya'a da Da'awar Shehu. Sai ya tashi dan uwansa Sambo yaje ya meka mubaya'arsu ga Shehu da kuma nuna goyon baya ga da'awarsa ta Addinin musulunci.Sambo ya kai chaffarsa ga Shehu a cikin shekarar 1807-1808. A wannan shekara ne jama'a daga garuruwa daban daban sukayi mubaya'a ga shehu, musamman Fulani wadda sune suka taimaka masa wajen jaddada Addinin Musulunci a kasar Hausa.

Bayanda Umaru ya tura Sambo zuwa ga Shehu, sambo ya tafi da  kaninsa Laraima da kuma sauran fulani 'yan uwansa. Shehu ya zabi Sambo da ya zama shine shugaban jaddada jihadi a kasar Hadejia saboda dama Sambo yana daga Dalibansa. Bayan sun dawo Hadejia sukaci gaba da jaddada Addinin Musulunci a ciki da wajen kasar Hadejia.kuma dukda basu samu turjiya da yawa a cikin garin Hadejia ba, Sarkin fulani Umaru da magoya bayansa sun samu turjiya da yawa musamman a yankin Gabas iyakar Hadejia da Nguru da kuma yankin Auyo. Fulanin Hadejia sun fara jaddada jihadinsu ne a Wajen Hadejia, inda suka fara da kauyukan da suke kusa da Rinde kamarsu Akurya da kadime da sauransu


Monday, March 17, 2014

JARMAN HADEJIA ALH. ABBA SAMBO (DAGA NA GABA PART FIVE 5)

TAKAITACCE TARIHIN MAIGIRMA JARMAN HADEJIA ALH. ABBA SAMBO!!

Daga Muhammad Yawale.


An haifi Alh. Abba sambo a shekara ta 1943 a cikin garin hadejia, ya fara karatun allo a matakin karatunsa na farko sannan lokacin ya isa shiga makarantar boko.
Ya fara da hadejia junior elementary school dake dalla wanda a yanzu ake kira
Abdulkadir primary school a shekarar 1953-1957 a garin hadejia.

Bayan ya kammala wannan makarantane ya samu shiga middle school a cikin shekarar 1957-1959, daga nan bayan kammala middle
school ya koma makarantar horan malamai ta wudil/bichi teachers collage a shekarar 1960-1965.

Bayan kammala wannan karatune ya samu zama headmaster a garin gabas primary school a shekara ta 1966-1971, ya koma karin karatu a advance teachers collage zaria a cikin shekara ta 1971-1974 wanda ya samu certificate in education (NCE).

Bayan kamamala (NCE) bai tsaya ba domin samun degree na farko a fannin physical Health Education (PHE) wanda ya kammala a 1975-1978 ABU Zaria.

Yayi hidimar kasa (NYSC) a federal advance teachers collage dutsinma katsina state daga 1978-1979.

Wasu ayyuka da yayi: (1) mataimakin
shugaban wasannin motsa jiki gwamnatin tarayya (NSSF) 1985-1989 (2) wakili a hukumar ilimi mai zurfi ta jami'ar Ahmadu
bello dake zaria 1988-1991 (3) wakilin tantance jarabawar dalibai na kasashen africa 1995. (4) shugaban wasannin motsa
jiki na makarantun jihar jigawa.

Mukaman da ya rike: (1) shugaban
makarantar primary ta garun gabas.(2) jami'i mai kula da shiyar kudu maso yamma wadda take birnin kudu a jihar kano (3) mataimakin
shugaban kwalejin makarantar horarda malamai dake garin hadejia (4) mataimakin jami'in ilimi na shiyoyin kananan hukumomin gezawa, da minjibir a jihar kano
(5) shugaban makarantar sakandiren jeka ka dawo dake kazaure (6) shugaban kwalejin
horar da malamai ta garki. Da sauransu.

Jarman hadejia ya bar aiki ranar 30th ga watan oktoba, 2001 a matakin aiki na 16/17.
Bayan rasuwar marigayi jarman hadejia Alh. Usman sambo na (2) a ranar Asabat 4 ga watan december 2010, maimartaba sarkin
hadejia Alh. Adamu Abubakar maje Con, ya nada ALH. ABBA SAMBO a matsayin JARMAN HADEJIA na (3) kuma Dan majalisar maimartaba sarki.

HADEJIA A YAU....

Thursday, March 6, 2014

DAGA NA GABA HADEJIAWA (Part four 4)

DAGA MUHAMMAD IDRIS

r;">


FARFESA HARUNA WAKILI...............Farfesa Wakili haifaffen kofar fadar Hadejia ne, kuma kamar yadda sunansa ya nuna mahaifinsa shi ne Wakilin kudun Hadejia [Dandalma] wato mai kula da yankin kudancin garin Hadejia.

Farfesa Wakili shi ne Farfesa na biyu a masarautar Hadejia kuma yana daya daga cikin `yan majalissar dattijai na Jami`ar Bayero ta kano kuma babban Alaramma a tsangayar tarihi ta makarantar, harwayau shi ne Mufti akan harkar tarihi a Arewacin kasar nan dominkafafen watsa labarai da dama na ciki da wajen Nijeriya suna dogara da fatawowinsa wajen warware matsalolin tarihi da suka bujuro musu.Baya da harkokinsa na cikin Jami`a Farfesa Haruna Wakili ya rike Daraktan Cibiyar Nazarin Harkokin Siyasa na Jami`ar wato MUMBAIYA dake Gidan Malam Aminu Kano a Unguwar Gwammajar kano.

" Na zaune bai ga gari ba", wanda bai sanJami`a ba, ba zai san gudunmawar Wakiliba domin a shekaru ashirin da biyar da suka gabata duk dan masarautar Hadejia da ya je Bayero ofishin Wakili ne zangonsa, shi kansa ba zai iya kididdige daliban da ya yi wa hanyar karatu a jami`a ba.

"Mai kamar zuwa kan aika" Yana cikin wannan gwagwarmaya Allah [swt] ya yi masa kwamishinan Ilmi na Jihar Jigawa. wannan mukami nasa duk Bahadeje mai hankali ba zai taba mantawa da shi ba domin baya da ci gaba a gyaran makarantu da samar da aiyuka da matasa da ya yi to kuma a lokacinsa babbar bukatarmu da muka dade muna nema ta neman babbar makaranta ta kai ga biya wato muka samu Jami`ar Kafin Hausa kuma aka gina babbar makarantaraiyukan gona ta Hadejia ta bar lungu ta dawo kan hanya.

Farfesa Haruna Wakili cikakken Bahadeje ne ba ya son raini amma yana da kishin al`ummarsa yana son ci gabansu kuma saboda daga darajar wannan masarauta shi rubutunsa ma na digirinsa na biyu akan wannan Masarauta ya yi.a takaice dai rayuwarsa akan bautawa Ilmi take.Hadejawa suna addu`a Allah Ya ba gwanin yafe gwado.



FARFESA HARUNA BIRNIWA............kamar yadda sunansa ya nuna Farfesa Haruna Birniwa haifaffen garin Birniwa ne kuma yana cikin haular masu mulkin garin.Birniwa shi ne farfesa na farko a cikin wannan masarauta kuma farfesa nabiyu a fadin Jihar Jigawa.

Gaba daya rayuwar Birniwa a kan bautawa Ilmi take domin ya kasance daya daga cikin dattawan malamai a Jami`ar Danfodiyo dake Sokoto na shekaru masu yawa kuma ya rike 'provost' a kwalejin Ilmi dake Gumel sannan ya rike kwamishinan Ilmi a wannan Jiha.

Farfesa Birniwa ya bayarda gudunmawa a fagen bayarda ilmi a Jihar nan matuka domin daruruwan mutane sun ci moriyarzamansa a sokoto domin shi 'admission' a wurinsa kamar mutum ya mari budurwa ne don haka za a ya ce wa shi ne ya budewa Hadejawa kofa a sokoto kuma bai bar sokoto ba sai da ya yi dashe.

Lokacin yana 'provost' ma masu rabo sun samu aiki a wurin.Birniwa ba harkar ilmin zamani kadai ya tsaya ba domin fakihi ne a fannin addini kuma fahintarsa da addini ta kara sa kyawawan halayensa sun kara kyautata domin mutum ne mai hakuri da gaskiya da rikon amana da saukin kai.wani abun sha`awa ga halayensa mai unguwarsa a Hadejia ya ce in dai yana gari duk yadda za a je neman ci gaba da shi ake yi. munaaddu`a Allah ya albarkaci bayansa.

Saturday, March 1, 2014

DAGA NA GABA! HADEJIAWA (PART TWO 2)


DAGA HASHIM AMAR...
MUHAMMAD (ABBAS SECRETARY)- Tsohon Sakataren kananan hukumomin Hadejia, Malam Maduri, SuleTankarkar da Guri; tsohon jami'in kula dajin dadin jama'a, a halin yanzu Akawun Majalisar dokoki ta Karamar Hukumar Guri(Clerk).

Wannan bawan Allah ya taka rawar gani wurin samar wa matasa da dama aikin yia lokacin da yake mukamin Sakatare musamman a Hadejia da Guri. Na san mutane da dama da wannan mutum ya samawa aikin yi, cikin su kuwa har da ni kaina.

HAJIYA SABUWA SHEHU- Shohuwar jami'ar ilmi, tsohuwar shugabar makarantar firamare, tsohuwar Sakatariyar ilmi ta Karamar Hukumar Hadejia; daya daga cikin mata 'yan boko na farko a Kasar Hadejia. Wannan baiwarAllah ta taimaka matuka wurin ci gaban ilmin mata a wannan yanki, ita ce ta dauki mafi yawanmata Malaman Makaranta a Hadejia.

Ta wani bangaren 'yar kasuwa ce da ta samar da aikin yi ga matasa ta wannan bangaren, ita ta kafa shagon gudanar da harkokin sarrafa na'ura mai kwakwalwa (Bussiness Centre)na farko a Hadejia. A yanzu haka 'yar kwamitin kwararru ce masu kula da aiyukan Bankin Duniya a Hadejia. Kuma ta na cikin kwamitin kula da Makarantun Firamare da Bankin duniya suka gina a Hadejia.

Wani abin sha'awa ita ta samar da filin ginin daya Makarantar (Shagari Community), ta nemi filin a hannun Karamar Hukumar Hadejia a  madadin LEA, filin yana hannun ta fiye da shekaru goma. Hajiya Sabuwa ta bayar da tsohongidan ta kyauta ga hukumar ilmi (LEA Hadejia) don gina Makaranta, gidan na unguwar Chadi. Allah Ya saka mata da alkhairi, ya yawaita mana irin ta.

Wednesday, February 19, 2014

DAGA NA GABA! HADEJIAWA...(part one 1)

Daga Muhammad Idris..

;
*****Ciroman Hadejia Sambo da ne ga Sarkin Hadejia Abdulkadir.Yana daga cikin 'yan boko na farko a Arewa kuma mutum na farko da ya fara zuwa England a Masarautar
Hadejia.Ya rike mukamin Dan Majalissar tarayya a zamaninsa kuma shi ne Babban Dan Majalissar Sarki (senior councillor) a
wannan masarauta.Idan aka yi Tarihin ci gaban kasar Hadejia ba a sanya Ciroma Sambo ba tamkar an yi tuya ba a sa albasa ba ne.

Ciroma Sambo dan ajinsu Sardauna ne Sir Ahmadu Bello kuma amininsa ne don haka Sardauna ya yi masa tayin mukamin
minista amma ya ki saboda ya ce "idan na bar Hadejia to ba za ta ci gaba ba"A takaice dai ciroman Sambo shi ne kashin bayan ci
gaban Hadejia, a zamaninsa ne aka yi gagarumin fashin layi wanda ya zama sanadin titunan da muke gani a cikin gari a yau kuma zamaninsa ne aka fara ginin rumfunan kasuwa na bulo.

Zamaninsa aka fara gina asibiti aka ofisosin gudanarwa da muke da su,a dai lokacin aka kawo wayar tangaraho a Hadejia da Malam Madori kuma Saboda hangen nesa da sanin muhinancin ilmi ciroma ya tursasawa jama'a su sa 'ya'yansu makaranta wanda wannan ce ta sa
wannan gari ya yi fice a fagen ilmi har a yau.Wato ba za mu iya kididdigewa aiyukan marigayi ciroma sambo ba saboda aiyukansa
ya hade masarautar baki daya.

Ciroma sambo shi ne ya koyawa Sarkin Kano Sunusi Turanci saboda zamani. Allah ya albarkanci
bayansa domin har yau Hadejia tana cin gajiyar 'ya'yansa da jikokinsa.Marigayi ciroma sambo masanin ilmin addini ne da
na zamani,rumfa sha shirgi,mai hannun kyauta,mai dimancaccen tunani, mai kishin Hadejia na farko.An haifi marigayi a 1909 Ya
rasu a 1958 wato yana da shekaru arba'in da tara a duniya kenan. Allah ya sa jannatil firdausi ce makomarsa. Amin.

FARFESA MUHAMMAD IBRAHIM YAKASAI
*************** Farfesa Muhammad Ibrahim Yakasai haifaffan kasar Garin Gabas
ne ta karamar Hukumar Malam Madorin Hadejia.Ya samu lakabin Yakasai saboda ya yi karatunsa a gaban yayarsa da ke aure a
unguwar Yakasai ta kano.

Muhammad Ibrahim yana daya daga cikin manyan 'yan boko na wannan Masarauta kuma shi ne
Bafulatani na farko da ya samu darajar farfesa a wannan masarauta.Yakasai ya fara malamin makaranta a sakandiren wunti da ke Hadejia na gajeren lokaci sannan ya samu
koyarwa a Jami'ar Bayero da ke kano.

Allah ya yi masa nasibi a harkar karatu domin ya kammala karatuttukansa a cikin lokaci
takaitacce.Yakasai yana cikin malamai dake taimakawa 'yan wannan masarauta da ma
jihar jigawa baki daya wajen samun shiga jami'a.Baya da daukansu kuma yakan dauki al'alar taimakawa wajen warware matsalar
da duk wani dalibi ya shiga cikin
jami'a.Yakasai mutum ne mai fara'a,mai saukin kai,mai sanin yakamata,Karatunsa bai sa ya dauki duniya da zafi ba.Muna masa addu'ar zama vice chancellor nan gaba. Hadejia A yau...

Wednesday, February 5, 2014

EMIRE OF HADEJIA ALH.HARUNA ABDULKADIR.

Emir of HADEJIA Alh. Haruna Abdulkadir ruled from 1950, before he was appointed as Chiroma as Distric head of Guri at the age of 12 in 1921, he experienced a poor health for some years, during which the emirate council ischaired by successive Galadimas, the decendent of Jaji on his behalf who takes charge on the administration of HADEJIA town, just like Sarkin Arewa is district head of Birniwa and Sarkin Dawaki administers kirikasamma district.

But while previously, during colonial period, the Tafida administered Kafin Hausa as district head, until more recently when it was given to Chiroma, a son to the Emir. Fallowing Chiroma’s appointment as a chairman of the Kano state local government service commission he was unfortunately obliged to reside at Kano city, leaving Kafin Hausa to be administered by his deputy while he retain the title.

The old emirate council from 1971 – 1975meet more frequently under the chairmanship of the Galadima Yusuf and Adamu, the major responsibilities of that administration rested firmly with Dan’iya,M. abdulkadir Maidugu, himself a grandson a grand of the Emir Abdulkadir and formally Sarkin Auyo and district head of Auyo, he represented HADEJIA inthe Federal House of Assembly. In his return after the abolition of a civilian rule, he was appointed Senior Executive Councillor of the Emirate council in charge of finance, the native administration,works, rural water supplyand community development.

TheTafida alh. Abdulkadir Maigari, another grandson of the emir Abdulkadir was appointed a councillor in charge of Agric and Natural resourses.The Danburan muhammadu Hurdi……………….

.(Culled from “Local Government at Hadejiia 1977” By M. G. Smith)
By Ma'aji I Abubakar.

Monday, January 13, 2014

HAWAN SALLAR GANI (MAULUDI) A HADEJIA 13/01/2014.

HADEJIA A YAU!
Sallar Mauludi ko Gani a Hadejia ya samo asali ne shekara 90 da suka gabata, wato 1910-1925. A lokacin Sarkin Hadejia Abdulkadir aka fara hawan Mauludi ko Gani a Hadejia, kuma ya kirkiro wannan hawa na Gani ne daidai sabuwar shekarar Musulunci, a Inda yake Ganawa da Hakimansa na waje (District heads) domin suyi jawabin Nasarori da Matsalolinda suka samu a kasarsu a shekararda ta gabata.

Saboda bikin yazo daidai da shekarar Mauludin Manzon Allah (s.a.w.) Sarkin Hadejia Abdulkadir sai yakan hau da Yamma tare da Hakimansa kamar yanda abin yake har yanzu. Kuma a ranar da safe akan gudanarda bukukuwa na Nadin sarautar Hakimi idan ta kama. Sarkin Hadejia Abdulkadir yakan yi hawa da hakimansa inda ake zagaya gari kuma a lokacin yakan bi ne ta Unguwanninda suke da Tsangaya domin ya taya Malaman murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (s.a.w.).

Kamar yanda Abin yake har yanzu Sarki zai fito daga fadarsa da yamma, zai bi ta Tudun mabudi ta Kasuwar kuda sannan yabi ta Kasgayama zuwa Kwarin madaki, sai ya fito ta bayi zuwa Magama hudu zuwa Unguwar Dukawa zuwa Hudu, sannan zai wuce ta Tagurza zuwa Majema zuwa bakin kasuwa, sannan sai ya biyo ta Makwallah zuwa Baderi zuwa Kofar Liman. Sannan ya koma fadarsa. Hadejia A yau.