Thursday, March 20, 2014

TARIHIN SARAKUNAN FULANIN HADEJIA (Kashi na daya 1)

TARIHIN SARAKUNAN FULANI A HADEJIA...



BISMILLAHIRRAHMANIR'RAHIM.

. Kamar yanda aka sani kasar Hadejia ta koma karkashin mulkin fulani bayan da suka hambarar da mulkin Habawa a karni na goma sha biyar (15). Fulani sun shigo kasar Hadejia ne a farkon karni na goma sha biyar (15), a karkashin jagorancin Ardo Abdure dan Jamdoyji, sun fara zama ne a Jarmari kusa da garin Hadejia, har tsawon wani lokaci. Bayan rasuwar Ardo Abdure a shekarar (1788) sai Dansa Sarkin fulani Umaru ya yanke shawarar su dawo Rinde da zama, yamma da garin Hadejia. kuma Sarkin Hadejia na Habe Abubakar ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia a cikin karni na goma sha takwas (18).

SARKIN FULANI UMARU... Shine sarki na farko a jerin sarakunan fulanin Hadejia, kuma a lokacinsa aka samu labarin jihadin Shehu Usman Danfodiyo. A lokacinda sarkin fulani Umaru yaji labarin jihadin shehu sai yayi shawara da 'yan uwansa da suje suyi Mubaya'a da Da'awar Shehu. Sai ya tashi dan uwansa Sambo yaje ya meka mubaya'arsu ga Shehu da kuma nuna goyon baya ga da'awarsa ta Addinin musulunci.Sambo ya kai chaffarsa ga Shehu a cikin shekarar 1807-1808. A wannan shekara ne jama'a daga garuruwa daban daban sukayi mubaya'a ga shehu, musamman Fulani wadda sune suka taimaka masa wajen jaddada Addinin Musulunci a kasar Hausa.

Bayanda Umaru ya tura Sambo zuwa ga Shehu, sambo ya tafi da  kaninsa Laraima da kuma sauran fulani 'yan uwansa. Shehu ya zabi Sambo da ya zama shine shugaban jaddada jihadi a kasar Hadejia saboda dama Sambo yana daga Dalibansa. Bayan sun dawo Hadejia sukaci gaba da jaddada Addinin Musulunci a ciki da wajen kasar Hadejia.kuma dukda basu samu turjiya da yawa a cikin garin Hadejia ba, Sarkin fulani Umaru da magoya bayansa sun samu turjiya da yawa musamman a yankin Gabas iyakar Hadejia da Nguru da kuma yankin Auyo. Fulanin Hadejia sun fara jaddada jihadinsu ne a Wajen Hadejia, inda suka fara da kauyukan da suke kusa da Rinde kamarsu Akurya da kadime da sauransu


No comments:

Post a Comment