Monday, December 30, 2013

TARIHIN KAFUWAR HADEJIA A TAKAICE..

HADEJIA-TARIHIN KAFUWARTA Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, a yawon farauta da yakeyi ne wata rana yana tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo ko da tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi mamakin hakan har ma sai yabi sawunta. Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye suna shawagi a wurin. Sai ya yanke shawarar zama a wannan wurin, kuma hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa yake harbe harben Namun daji kuma yayi suw, wato kamun kifi. In ya kashe namun daji sai yaje ya sayar da fatun. Harma ya dauko Matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan wurin. Sannan mutane sai suke zuwa sayen fatu da nama a wajensa. Duk wanda yazo wurin sai yayi sha'awar zama a wurun, haka nan gari ya fara bunkasa wasu maharba, wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada zango a garin. 

 To kasancewar gari sai da shugabanci ne yasa shi Hade ya zama shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu ko nama sai yace na tafi garin Haden jia. Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia. Kuma bayan zamanin wannan mutumin Hadejia taci gaba da zama gari kuma tare da shugabanci wato mulkin Habawa. Hadejia A yau! Kuma a lokacin akwai kananan Garuruwa masu cin gashin kansu kamar Rinde, yayari, wunti, Anku da dai sauransu. Wadanda suma suna da nasu sarakunan a wannan Lokacin. 

Amma yanzu duk unguwanni ne a cikin garin Hadejia. Kuma Hadejia sunyi sarakunan Habe guda talatin da biyu(32) amma sunan mutum uku ake dasu wadanda sukayi mulki kafin zuwan Fulani.

 1, BAUDE 2, MUSA 3, ABUBAKAR. Kuma a lokacin Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin Hadejia tana karkashin Mulkin Habawa ne, kuma ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman dan fodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune suke sarautar Kasar Hadejia. Hadejia A yau..

Madogara..... 
Assessment report of Hadejia Division 
Eap/blu. Nak/804

Saturday, November 30, 2013

TARIHIN GIZMAWA (NGZIM) DA AL'ADUNSU.

By Comrade Garba Muhd. Hadejia.

GIZMAWA KO NGZIM. Wani sashe ne na Kanuri (Bare-bari) wadanda sukazo daga Borno. Kanuri dai sun kasu gida uku (3), akwai:
Mangawa
Gizmawa
da Larawa.

Mangawa Akasarinsu anfi samunsu a kasar Birniwa da Kirikasamma.

Gizmawa ana samunsu mafi yawa a kasar Guri. A garuruwa irin su Guri, Arin, Dagana, Joriyo, Adiyani, Zugo, Wacakal, Garmaguwa, Garbagal, Margadu,Tukuikui, Dole, Abir da sauransu.

Larawa kuma sunfi yawa a tsakanin Badar, Jigawa, da Bauchi ta kasar Guri. Ana samunsu a Garuruwa irin su: Takazza, Damegi, Gaduwa, Musari da sauransu.

Banbancin da ke tsakanin Gizmawa da Mangawa da Larawa bash da yawa. Kamar banbancin Hausar kano ne da ta katsina ko Hausar sokoto da ta Hadejia. Amma ko wanne yana fahimtar kowane tsakaninsu, wato banbancin a karin harshe ne, kuma a haka suke gane wannan kabilar Ba gizme ne ko Bamange.

Su kuma Kanurin Kadira sun sha bam ban da Gizmawa Larawa da Mangawa. Domin su suna Barbarci ne irin na Borno. Saboda haka ko tsarin zamantakewarsu da sarautarsu ya sha banban.

A bangaren al'adu da zamantakewa basu da bambanci da juna. (Gizmawa Mangawa da Larawa). Tsarin Addinin Musulunci da cudanya da Hausawa ta sa Al'adu da dama na Gizmawa sunyi watsi dasu. Kamar kidan Bango; Rawar Dimas; Rawar biki da al'adun Aurensu duka yanzu ba sosai ake yinsu ba da yawa Hausa ta kwace su.

Wani zaiyi tambaya me yasa aka samu kashe kashen kanuri har gida uku? Dalili shine, zamantakewa da ta bambanta aka samu watsuwarsu a kasar Hausa.

Rabewar Daular Kanem-Borno da Zuwan Rabeh ne yasa wasu daga cikinsu suka tsinci kansu a Daular Usmaniyya, wadda take cike da Hausa Fulani. Kanurinda suke yankin Masarautar Hadejia Musamman ma kasar Guri, sun gauraya da Badawa da fulani da Auyakawa. Hakan tasa karin sautin muryarsu ya sha bamban da kanurin Borno da Yobe. Sannan Al'adunsu sun jirwaye da na Hausawa.

Sannan tsarin Sarautarsu yasa dole suke Amfani da Bulama Maimakon Mai ko Lawan. Amma kuma har yanzu a garin Kadira zaka Iske Kanuri ne suke rike da sarautar garin tare da Badawa da kuma Hausa-fulani kadan.

Sannan ba'a iya bambance Bagizme ko Bamange ko Balare a fuska, domin daga cikinsu zaka iya samun Abubuwa kamar haka:-
*Zube (zane)
*Sutura
*Karin harshe
*Al'adun Aure
*Sana'a
*Tsarin Auratayya
*Addini
*Zamantakewa
*Sunaye
*Son girma
*Kishin yare
*Gardama
*Bajinta
*Ki fadi.

Zane a fuska ya danganta da tsarin iyayen mutum, wadansu iyayen suna da Sha'awar a yiwa 'ya'yansu zube, wasu ko basu da ra'ayin hakan. Saboda haka a cikinsu ana samun mai zube ana samun marar zube.

Barebari ______ Borno

Bamange______ Kirikasamma
Birniwa.

Bagizme________ Guri, Adiyani, Zugo, Gabargal.da sauransu.

Balare__________ Gaduwa, Musari, Takazza, Margadu.da sauransu.

Hadejia A yau.

Sunday, November 24, 2013

TARIHIN HARUNA UJI DA WAKOKINSA. KASHI NA BIYU (2).

Hadejia A yau!



Littafin Muhd. Aji Hadejia.

A kashi na farko kunji cewa Alh. Haruna Uji ya ci gaba da kidan Gurmi gadan gadan.

A lokacin Gwamnan Kano Abdu Bako, sai yaji labarin Haruna Uji, sai yasa aka nemoshi domin yayi masa waka akan wayar da kan Al'umma akan Noma. Saboda haka Gwamna Abdu Bako sai ya hadawa Haruna Uji kayan wasa, kamar Amsa Kuwwa (Loud speaker) da Abin Magana wato (Microphone) da Injin wuta, wato Generator.
Wannan shine lokaci na farko da Haruna Uji ya fara waka da kayan wasa na zamani, kuma ya kama yin waka gadan gadan a matsayin sana'a.

Wakar da yayi a lokacin Itace wakar Noma. Anyi wakar ne da nufin wayar da kan Talakawa su koma Aikin gona.

3.0. WAKOKIN HARUNA UJI NA FARKO.

Alh. Haruna Uji yayi wakoki masu tarin yawa, kuma a cikin Jerin wakokinsa ga wasu daga cikin wakokin da ya fara yi.

*Wakar Naira da kwabo sabon kudi.

*Wakar Gudaliya.

*Wakar Shamuwa.

*Wakar Noma.

*Wakar Bakar Rama.
Wadannan sune kusan Shahararrun wakokin da ya fara yi.

3.1. Ajin Haruna Uji a tsakanin Mawakan baka.

A cikin wani Littafi da Ibrahim Yaro Yahya da Abba Rufa'i suka tsara, Mamuda Aminu ya kawo rabe-raben Mawakan baka zuwa rukunai kamar haka:
*Mawakan Sarakuna
*Mawakan 'yan mata
*Mawakan Jama'a
*Mawakan Mafarauta. Da sauransu.

Ya kawo misalin Mawakan Jama'a shine wanda zai yiwa Sarakuna da 'yan kasuwa da 'yan mata da Masu kudi da talakawa waka. Misali Mamman shata da Haruna Uji da sauransu.

Hakan ta nuna cewa Haruna Uji ya kasance a cikin Mawakan Jama'a, domin ya tabo duk abinda aka zayyana a sama. Wato yakan yiwa kowa waka.

3.1.1 Dangantakar Haruna Uji da Mawakan Baka.

Alh. Haruna Uji yana da kyakkyawar dangantaka da sauran 'yan uwansa mawakan baka, yana girmamasu shima suna girmama shi, sannan ya hori wasu suma sun zama shahararrun mawaka a kasar Hausa. Yayiwa wasu waka kuma shima wasu sunyi masa. A cikin mawakan da suka masa waka har da Alh. Mamman shata, kuma shima Haruna Uji yayi wa Alh. Garba sufa wakar Ta'aziyya bayan ya mutu.

3.1.2 Jerin wasu daga wakokin Haruna Uji.

Bayan rukunin wakokinsa na farko, ga wasu daga cikin wakokin da yayi.

*Wakar Dankabo
*Wakar Alh. Sani Likori
*Wakar Direban Chiyaman
*Wakar (Air vice marshal) Ibrahim Alpha
*Wakar (kwamishinan 'yan sanda) Daudu Gwalalo
*Wakar Haruna karamba
*Wakar Adamu Hassan Abunabo
*Wakar Ahmed Aruwa
*Wakar Asabe Madara
*Wakar Amadu koloji makwallah
*Wakar Bako Inusa kano
*Wakar Balaraba
*Wakar Jimmai Aljummah
*Wakar Birgediya Abdullahi shalin.
*Wakar Dankamasho
*Wakar Fulanin Jebbi fulato
*Wakar Idiyo Mai kayan Babur
*Wakar Kainuwa.

SAURAN WAKOKIN KU DUBA LITTAFIN.

Ka duba kashi na uku (3)

Thursday, November 21, 2013

TARIHIN HARUNA UJI. DA WAKOKINSA. KASHI NA DAYA (1).

Alh. Haruna Uji Hadejia.

Hadejia A yau! An haifi Alh. Haruna Uji A Unguwar Gandun sarki dake cikin garin Hadejia, a shekarar (1946). Sunan Mahaifinsa Mallam Ibrahim, Malami ne kuma shine Limamin Gandun sarki. Sunan Mahaifiyarsa Zainabu itama mutumiyar Unguwar ce. Anan ya tashi yayi wayo. Yana kimanin shekara shida mahaifinsa ya sakashi a makarantar Allo dake kofar gidansu, a gun wani Malami da ake kira Mallam Alhaji.

Haruna Uji ya shafe wajen shekaru uku yana wannan Makaranta a Gandun sarki, daga nan suka tashi da malaminsa zuwa garin Birniwa wanda take gabas da Hadejia, mai nisan kilo mita 45. Sun kwashe shekaru kamar biyu suna karatu da sauran Almajirai, anan Uji ya samu karatu mai dama.

Bayan nan suka bar Birniwa suka dawo Hadejia suka ci gaba da karatu a Gandun sarki. Wannan yasa ya samu karatu mai dama fiye da sauran yara musamman wadanda suka zauna a gida basu fita wani guri neman Ilmi ba. A wannan lokaci Mallam Alhaji yakan sa Uji ya kula da yara tare da koya musu karatu. Haruna Uji ya bar makarantar Allo yana dan shekara goma sha biyu, bayan ya samu karatu mai dama.
Hadejia A yau!

1.1, ASALIN INKIYAR HARUNA UJI..
Sunansa na yanka Haruna, yaci sunan wan Mahaifinsa, wato Mallam Haruna. Mallam Haruna mai sunan Uji yana da mata mai suna IYA KURA, Lokacin Uji yana karami matan kanin Babansa suna masa wasa suna ce masa Mijin Iya Kura, Mijin Iya Kura' A wannan Lokacin yara kannensa basu da baki, sai suke ce masa, Ujin Iya Kura. Maimakon Mijin Iya Kura. Wannan shine Asalin inda Haruna Uji ya samo Inkiyar Uji. Tun ana danganta sunan da Iya Kura har aka daina ake cewa Uji.

1.11, SIFFAR HARUNA UJI.
Haruna Uji baki ne, mai matsakaicin tsawo, yana da jiki matsakaici, ga farin hakora da bakin gashi, yana yawan barin gashin baki, ga magana (Idanu) haka kuma, ma'abocin barin suma ne, yana da Murya mai zaki da kauri kadan, kuma Gwanin Ado ne, da manyan kaya na sarauta. Kuma yakan saka 'yar shara, musamman lokacin zafi.

Alh. Haruna Uji mutum nd mai fara'a da kyauta, domin abin hannunsa bai rufe masa ido ba. Yana da raha sannan kuma bashi da wata nakasa a fili.

2.0, SANA'OIN HARUNA UJI..

2.1, Farauta da Noma.
Bayan Haruna Uji ya bar makarantar Allo, ya fara zuwa Daji da nufin farauta. Wadda itace sana'arsa ta farko, wanda ya fara, kuma ta sanyashi jarunta inda ya zama bashi da tsoro. Kuma a nan ne ya samu tambaya wato lakani na tsare kai.

Bayan farauta Haruna Uji Manomi ne, ya fara aikin gona ne da taya mahaifinsa, domin neman tabariki, wannan tasa yasan harkar noma wanda har yake noma gonar kansa.

2.2, Sana'ar Tukin Mota (Direba)
Alh. Haruna Uji yayi Sana'ar Tukin mota, wanda ya fara da Yaron mota a gun Mai gidansa wanda ake kira da suna Jibrin Dan Amingo. Jibrin Dan Amingo dan Asalin Danbatta ne ta Jihar Kano. Haruna Uji ya shafe shekaru da dama yana sana'ar yaron mota. Tukin mota ne sana'arsa ta farko da ta fara fitar dashi wani gari da nufin zama. Suna aiki ne tsakanin Kano da Hadejia.

Kuma a wannan lokacin suna zaune ne a garin kano a Tudun wada. Amma duk abinda ya taso a gida dashi akeyi, musamman aikin gona da bukukuwa da sauransu.

2.3, Sana'ar Waka.
Haruna Uji bai gaji waka ba, domin Mahaifinsa Malami ne, kuma ko a wakarsa ta Gurmi ba Haramun ba yana cewa:-
"Ni Haruna dan Mallam nake, Waka ta ba ta gado bace"

Saboda haka tun farko Haruna Uji ya riki waka ne a matsayin nishadi, domin ba wanda ya koya masa waka a matsayin Sana'a.

Haruna Uji ya fara ganin Gurmi ne a gun wani ma'aikacin titi wanda sukayi aiki a hanyar Mallam madori zuwa Gumel, wanda ake kira Dan-mato, a gun Dan-mato Uji ya fara ganin Gurmi da kidansa, shi Dan-mato yana kada Gurmi ne a yayinda suka samu hutun aiki. Yana kadawa yana waka, lokacin Uji yana Matashi, duk lokacinda sukaje kallon aiki sai su tsaya suna ganin kidan Gurmin Dan-mato, wannan tasa kidan Gurmi ya shiga ran Haruna Uji, idan ya dawo gida sai yakan nemi gwangwani da tsirkiya ya hada Gurmi yana kadawa. Har Dan-mato suka hada aikin hanya bai koyawa Uji Gurmi ba, sai dai Uji yana zuwa yana ganin yanda yake kadawa. Wannan tasa Uji ya dinga kwaikoyon Dan-mato tun bai iya ba har ya koya.

Wannan yasa idan yana gurmi yara sukan tsaya suna ji da kallonsa, Wannan shine Asalin koyon Gurmin Haruna Uji. Daga nan sai ya fara tunanin ya samu sanda, da lilo da butar Duma da fatar Damo da Zobe domin ya hada bubban Gurmi.

Farkon lokacinda ya fara Gurmi idan an bashi abu baya karba, don yanayi ne saboda Nishadi. Kuma sau da yawa idan ya fito hira ko ana wani biki na samari da 'yan mata, yakan kada Gurminsa yana waka, samari da 'yan mata suna kallo.

A wancan lokacin yana Gurmi yana aikin Mota, wannan yasa ya fara Gurmi a garuruwa daban daban na Arewacin Nigeria.

Daga nan Uji ya bar tukin mota ya koma kidan Gurmi Kuma ya nemi mataimaka don sunayi su biyu.

Karashe a kashi na 2.
Littafin Muhd. Aji Hadejia

Tuesday, November 19, 2013

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KUDANCIN GURI. (KASHI NA 2)



BY COMRADE GARBA MUHD HADEJIA


A lokacin da makiyaya su ka fara yin ta'adi a gonakin mazauna yankin ba a gayyaci kowace hukuma a cikin al'amuran ba, ganin cewar matsalar karama ce a wancan lokacin. Kuma su manoman basu san hakikanin irin fulanin da suke yin wannan ta'adin ba. Har su kan yi tunananin cewar wai shin fullo-Hadejia ne ko Zamfarawa?


Faruwar hakan ta ja hankalin shugabannin mazauna yankin (manoma) wadanda suka hada da Dagatai,Bulamai, Lawanai (Bade), Mai (Gizimawa) don tattauna matsalar da shugabannin Fulani irinsu Lamidai da Hardawa. Irin wannan tattaunawa ta yi ta faruwa har hukuma ta shigo cikin sabgar don rushe dukkan wani yunkuri na barkewar rikici. Saboda abin ya na faruwa duk shekara musamman ma da kaka. Duk da shigowar hukuma cikin lamarin, bai hana daukar fansa daga manoman ba, saboda kai su bango da makiyayan suka yi na cinye musu amfanin Gonakinsu.


A duk shekara a kan asarar rayuwa daga kowane bangare. Duk da kasancewar jami'an tsaro kala-kala; yan sanda, mobile police, wani lokaci har da sojoji don sasanta tsakanin manoma da makiyaya. Suma jami'an tsaron daga bangarensu sun rasa da yawa daga cikin mutanensu. Wasu an harbe su da kibiya, wasu an sassarasu da arda sun mutu wasu an lagarta su, saboda hukuma bata basu damar harbi ba.


A kwai shekarar da har jirgi mai saukar ungulu (Helcopter) aka kai yankin don shiga surkukin dajin da ke wannan yankin. Daga cikin matsalolin da jami'an tsaro su ke samu daga wannan yankin, shine rashin basu umarnin daukar mataki na kare kansu daga dukkanin wanda zai yi yunkurin harbinsu ko sararsu. Haka tasa suke janye jikinsu daga shiga cikin rigimar gadangadan. Daga bangaren gwamnatocin siyaya an samu da yawa da suka taka rawa don ganin an shawo kan matsalar amma idan shekara ta zagayo sai an yi.Haka kowace gwamnati take yi.


A lokuta da dama akan kafa kwamatoci na musamman wanda zaiyi bincike akan matsalar, amma daga karshe sai a kasa cimma komai. Su kan nemi zama da kungiyar manoma da makiyaya da shugabannin kowane bangare don kowa ya jawa mutanensa kunne amma daga karshe sai abin ya bi iska. A wasu lokutan korafe-korafe su kanyi yawa daga bangarorin biyu na zargar junansu da laifin tayarda rigimar. Makiyaya su kan ce laifin manoma ne da suke noma makiyayar dabbobi da burtalai, su kuma manoma su ce laifin makiyaya ne da baza su yi hakurin barinsu su tare amfanin gonarsu ba.

Haka dai ake ta maganganu a kai. Daga lokacin da gwamnati mai mulki a yanzu ta hau. Ta yi kokarin lallai kowane makiyayi ya tsaya a makiyayarsa. Sannan ta tabbatar da kowane burtali da makiyayar dabbobi ba a nomashi ba. Sai dai wani abin mamaki har yanzu abin bai chanja ba, domin wannan rigimar bata mutu ba. Ko shekarar da ta wuce ma an sami rikici a wasu garuruwa irin su Gagiya da Garin Mallam. wadanda su ke kudancin Guri. Ko a wannan lokaci da ka ke karanta wannan rubutun ma, an sami wadansu daga cikin makiyaya suna shiga gonakin manoma suna cinye musu Amfanin gona. Wannan matsalar ta kawo ci baya gagarumi a kudancin Guri. Domin manoma da yawa sun hakura da noman shinkafa, Alkama, Wake da kankana. Abin da ya rage kawai sai gero da dawa, wanda a yanzu a kansu ake yin wannan rigimar domin shi din ma yana neman fin karfinsu.

Babban dalilin da ya sa manoman su ka hakuri da noma wadansu daga cikin amfanin gonar shine. Yawan zubda jinin al'umma da ake yi sakamakon kare dukiyoyinsu. Saboda wasu lokutan har garuruwansu (manoman) ake binsu don a halaka su. Wata shekara akwai garin da aka kona kurmus; tare da abincinsu, da dabbobinsu da dattijai da kananan yara wadanda ba za su iya guduba. Daga karshe, ina kira ga duk wanda ke ziyartar wannan dandali mai albarka, kuma ya kasance mai iko, da ya isar da wannan sakon ga hukumomin da abin ya shafa su duba al'amarin wadannan bayin Allah don kawo masu karshen wannan matsalar.


Sannan 'Yan majalissu na tarayya da na jiha da su kalli wannan abin ta hanyar janyo hankalin gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen warware wannan matsalar. Abin da gwamnati ya kamata ta lura da shi, shine wannan matsala ce ta cikin gida tsakanin manoma da makiyaya. Kuma suma wadannan makiyaya (fulani) 'yan uwanmu ne musulmi, sannan mun zo daga bangare daya, kuma tare muke zaune, kasuwa da ya muke ci da su ga auratayya ta hada mu.

Saboda haka ba sai da bakin bindiga za a sasanta ba, a'a akan tabarma za a zauna tare da kwararru a fannin warware rikici wadanda suka karanta (conflicts Resolution) da malaman addini da sauran masu fada a ji a cikin al'umma don a tabbatar da adalci tsakanin manoma da makiyaya. HADEJIA A YAU.

Sunday, November 17, 2013

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KUDANCIN GURI...(1)


BY COMRADE GARBA MUHD HADEJIA.

CIWON CIKIN BAREWA A DAJI.

Zamantakewa wata aba ce wadda ta ke kasancewa tsakanin kowane jinsi, na mutane, aljannu, dabbobi da tsuntsaye da sauran halittu. kowane jinsi daga cikin halittu yana da irin kalubalensa na neman cika jakar ciki da sauran bukatu wadanda dole sai an cimma su za a samu dorewar rayuwa, sannan rayuwa ta bada zaman lafiya.

Idan ko ya kasance wani ko wasu daga cikin wannan jinsi zasu fifita bukatunsu fiye da na 'yan uwansu, to za a iya samun barkewar rashin jituwa, wanda shine zai yi sanadin barkewar rashin zaman lafiya a tsakanin wannan jinsin.

Dan Adam, wanda ya kasance mafi hikima a cikin sauran halittu,saboda wadansu ni'imomi da ubangiji ya yi musu. Shi kadai ne ya ke da tunanin ya noma abin da zai ci, don samun dorewar rayuwa, da nisanta daga galabaita da zai yi a yayin da ya nemi abinci ya rasa a muhallinsa. Daga cikin
abin da ya noma har da tunanin tanaji don gaba yayi amfani da shi.
Kasancewarsa mai hikima (Dan Adam) Allah ya bashi ikon sarrafa wasu daga cikin dabbobin gida, kamar su shanu, awakai, tumakai,rakuma da sauransu.

Daga cikinsu (Yan Adam) akwai wadanda suka zabi kasancewa da dabbobi a matsayin dukiya. Wanda hakan ya sa dole su ka kebe kasu daga cikin jama'a don su samu damar kula da dabbobinsu ta hanyar ciyar da su da shayar da su daga ciyayi da ganyayyaki. Hakan yasa wasu daga cikinsu ko noma ba sa samun damar yi, sai dai su sayi abinci daga manoma ko a kasuwa daga kudaden da suka samu a yayin da suka sayar da dabba ko nononta.

Wani lokacin sukan yi bulaguro daga wani yanki zuwa wani yanki don samarwa dabbobinsu abinci, musamman a lokacin rani ko damana su kan tashi daga yankin da bai da ni'ima zuwa yankin da ya ke da ni'ima.

Haka ta sa ake ganinsu a mutanen da ba su da takamaiman gari, kasa ko nashiya.


Kudancin Guri ya kasance mafi ni'ima idan aka hada shi da sauran yankuna na masarautar Hadejia. Domin albarkatu na daji, fadamu, gurin kiwo, kifi, tsuntsaye, da sauran albarkatun noma. Haka shine ya sa makiyaya suke da yawa a kudancin Guri.

Idan aka ce kudancin Guri ana nufin Gundumar Kadira ko muce (Kadira Distric) sun hada da manyan garu-ruwa irinsu Kadira, Abunabo, Musari, Gaduwa da Galdimari, Garin Mallam, Gagiya,Garmaguwa daSauransu.

Wannan yanki ya hada yaruka (kabilu) masu yawa sabanin sauran yankuna na Masarautar Hadejia. A wannan yanki za ka samu Mangawa, Gizimawa, Badawa, Fulani, Larawa, sai kuma Hausawa Auyakawa wadanda ba su da yawa.
Daga shekara ta 1980 ne aka fara samun shigowar makiyaya (Fulani) a wannan yankin.

Fulanin da suka fara zuwa sun kasu kashi hudu, akwai:
Aborawa, Zamfarawa, Udawa, Fullo-Hadejia da Wuddurawa.

Wadanda su ka fara zuwa sune Aborawa. A wancan lokacin sukan zo a lokacin da ruwa ya gama cin dajin ciyawa ta fito sannan su yi kiwo. A wannan lokacin ya kasance a kwai wani ruwa da ake kiransa da suna Ruwan Dukuku; shi wannan ruwa idan ya zo ya kan mamaye dajin gaba daya, ya zamanto babu makiyaya. Hakan yake sa dole makiyayan su yi hijira zuwa kasar Yobe (Bade) don yin kiwo kafin ruwan ya janye su dawo.

Haka aka yi ta tafiya har Udawa su ka fara zuwa don yin kiwonsu a wannan daji kamar yadda Aborawa su ke yi. Su ko mazauna yankin su kanyi nomansu iri-iri, tare da sana'a ta kamun kifi.
Daga cikin Aborawa da Udawa aka samu Fulani mazauna wanda ake kira da Fullo-Hadejia. Sun kafa garuruwa irinsu; Safami, Maidashi, Matarar kano, Dolewa,Askandu da sauransu. Su kan zauna tare da dabbobinsu a rigagensu kuma su kan yi noma a guraren. A yayin da ruwan dukuku ya daina cin Dajin.

Daga nan sai zuwan zamfarawa.
Zamfarawa sun shigo kudancin Guri ne sakamakon fitintinu da ke yawan afkuwa a yankunansu na Zamfara.
Sakamakon haka ne ya sa su ka yi Hijira daga can suka zo kudancin Guri. Sun kasance ba mazauna guri kawai ba, sukan yawata zuwa sauran yankuna na Guri har sukan zuwa makwabta irinsu madaci, marma da sauran guraren da ake noman shinkafa don yin kiwo.

Haka zamantakewa ta ci gaba da kasancewa tsakanin wadannan al'ummah har zuwan Wuddurawa wadanda su ka zo daga kasar
Katagum da sauran yankunan jihar Bauchi. Domin kudancin Guri ya yi iyaka da Bauchi.

Zumunci tsakanin mazauna yankin da makiyaya (Fulani) ya ci gaba da kulluwa, sakamakon cudanya ta cinikayya da sauran al'amura na yau da kullum ya sa har auratayya ta fara kulluwa a tsakaninsu. Wannan ya sa duk auran da za a yi a Rigar fulani sai ka ga daya daga cikin mazauna yankin ya halarta haka suma fulanin.

Ku biyomu a kashi na biyu (2).
Hadejia A yau.

Wednesday, November 13, 2013

KASIDAR MALAMAN MAKARANTA.

Hadejia A yau! 1, Madallah da Mallam Usaini Sulaiman Malamin makaranta.

2, Bismillah mu fara da sunan Allah wanda yayi halittu, shi yayi malamin makaranta.

3, Allah shi ya shirya halitta, yayi ruwa wuta rana da wata yayi malaman Makaranta.

4, Shine yayi Malam Usaini, masu prince ta Eco banki kan hanyar zuwa Makabarta.

5, Sabo na gode sarki Allah, wanda ya bani iko na sa 'yata a Prince farar Makaranta.

6, Nagodewa Mallam Usaini, shine Headmastan Prince makarantar nan dana saka 'yata.

7, Ba shi dai ba har malamansa, koda zasu fishi hazaka sun isa malaman makaranta.

8, Nagodewa duk Malamansu, Yarinya a sati biyar ta haddace duk Jihohin kasata.

9, Ga jinjina ga Malam Usaini, da sauran Malamanda suke a Prince kuma kuna zuciyata.

10, Yarinya ta ban mamaki, tun daga A zuwa Zed idan ta zauna zata kawosu 'yata.

11, Lissafi kamar kalkuleta, kai ko kalkuleta ma nasan da kadan fa zatafi 'yata.

12, Burin duk Uba tarbiyya, to Alhamdulillahi Allah shi yayi malaman Makaranta.

13, Iyaye nai kira a gareku, duk mai Da ya kaishi Prince domin yaga fa'idar Makaranta.

14, Ga koyon Handwritting Idan Munje home work suke baiwa 'yata.

Tuesday, November 12, 2013

ZUWAN AMINU ALA HADEJIA.KADDAMARDA LITTAFIN WAKOKIN HARUNA UJI...

Aminu Ala.
Free Web Proxy

1, Mun gode Aminu Ala, Barka da zuwa Hadejia, gun taron kaddamar da littafin Aji kima.

2, Bismillah zana fara waka da yabon gwanina, gwanin kowa a waka lalle Ala babu dama.

3, Nagodewa Ilahi, Nagode Aminu Ala nagode Aji kima.

4, Ranar Asabat a fantai, A filin kaddamar da tarihin Haruna Uji, da wakoki nai masu dama.

5, Haruna Uji Hadejia, ya bada gudunmawa fa, a wakoki da suke kai sako ai nadama.

6, Ko anyi raha a watse, ko a fadakarda kai zaman rayuwarka ina makoma.

7, Taro kuma yayi kyawu, jama'a duk sunji dadi, suna yin jinjina gun shi wannan wanda yayi littafin Aji kima.

8, Ado Ahmed Gidan dabino, dashi da Aminu Ala, Bashir Ahmed blogger, Marubuta baku dama.

9, Yasir Ramadan gwale bai samu zuwa ba saboda nisa, Amma sakonka na san ya iske Aji kima.

10, In zaka fadi fadi gaskiya, wani shafi ne na Yasir, kaje kaga zunzurutun fasaha babu dama.

11, Godiya gun kungiyoyin, facebook na jihar jigawa, shugabannin Dandalin siyasa mun dau sakonku kuma.

12, Gizagawan zumunci, suma ba'a barsu baya, Dandalin marubuta godiya wakilancinku kuma.

13, Dr. Dahiru godiyarmu, bata manta da shi ba, don shine yayi sharhin littafin Aji kima.

14, Ga sakon godiyarmu ga Dr. Abbas na Ringim, shima ya danyi sharhi, jama'armu Ina makoma.

15, Shugaban karamar hukumar Hadejiya Alhajindo, Umar Danjani p.A. Barka da zuwanka kaima.

Alh. Baffa Bura.... Allah yayi ma Mabudi.......
Hadejia A yau.

Sunday, November 10, 2013

SAKON BANGAJIYA DAGA KWAMITIN KADDAMAR DA LITTAFIN TARIHIN HARUNA UJI DA WAKOKINSA.

Comrade Aji Kima Hadejia!
Free Web Proxy
HADEJIA A YAU!
Assalamu Alaikum! Bayan gaisuwa irinta Addinin Musulunci, muna meka sakon godiya da ban gajiya ga wadanda suka halarci taron kaddamar da Littafin Tarihin Marigayi Haruna Uji da Wakokinsa. Wanda akayi a
Ranar Asabat 9th November 2013, a Dakin Taro na sakandare fantai.

Muna Meka sakon bangajiya da fatan Alkairi zuwa ga Shugaban karamar hukumar Hadejia, Alh. Abba Haruna. Da mai baiwa Gwamna shawara akan harkokin dalibai Alh Umaru Danjani.

Gaisuwa da fatan Alkairi ga
Shugaban kwalejin Ilimi ta jihar Jigawa Dr. Dahiru Abdulkadir. Da shugaban Makarantar koyon aikin Alkalanci ta Ringim Dr. Abbas A. Abbas.

Gaisuwa da fatan Alkairi ga
Babban mai kaddamarwa;

Pharm.Hashim Ubale Yusufu

Muna meka sakon godiya ga kungiyoyin facebook da kuma kungiyoyin Marubuta da Mawallafa na Jihohin kano da jigawa.

Sakon godiya da bangajiya zuwa ga Alh Aminu Ladan Ala
da Ado Ahmed Gidan Dibino.

Muna Meka sakon Jinjina da bangajiya zuwa ga Alh Baffa Bura FNICPR.

Muna meka sakon Godiya ga Iyalan Marigayi Haruna Uji da jama'ar Unguwar Gandun Sarki.
Gaisuwa da godiya ga Jami'an tsaro da 'yan jarida da ma'aikatan yada Labarai.
Allah ya huci gajiya.

Tuesday, November 5, 2013

TARIHIN MARIGAYI HARUNA UJI DA WAKOKINSA. MUHD. AJI HADEJIA...

Comrade Aji Kima Hadejia!
Free Web Proxy
HADEJIA A YAU!
Muna gayyatar yan uwa da Abokan Arziki zuwa wajen kaddamar da littafin da na
rubuta wanda na kira
"Tarihin Alh Haruna Uji da Wakokinsa"

Za'ayi Taron kamar haka:

Rana=Asabat 9th November 2013 Guri=Dakin Taro na sakandire fantai Hadejia Jigawa state Lokaci=10am

Baban Bako na musamman;

mai girma gwamnan jihar jigawa Alhaji Dr sule Lamido con.

Uban Taro;

Mai Martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje Con.

Shugabannin Taro;

1.Alhaji Suleman Baffa
2.Alh Muhammadu Daguro

Masu Masaukin baki:

1.Mai girma shugaban karamar hukumar Hadejia Alh Abba Haruna
2.mai girma dan majalissar jiha mai wakiltar Hadejia Alh Aminu Abus
3.Mai girma mai bawa gwamna shawara akan harkokin dalibai Alh Umaru Danjani.

Bako mai jawabi;

Mai girma kwamishinan Ilimi na jihar Jigawa Farfesa Haruna Wakili.

Mai bitar Littafi;

Shugaban kwalejin Ilimi ta jihar Jigawa Dr. Dahiru Abdulkadir.

Babban mai kaddamarwa;

Pharm.Hashim Ubale Yusufu

Mataimakan masu kaddamarwa

1.Mai Girma shugaban jam'iyar PDP ta jihar Jigawa Alh Salisu Mamuda.
2.Mai Girma kakakin majalissar dokokin jihar jigawa Alh Adamu Ahmed
sarawa.
3.Mai Girma mataimakin kakakin majalissar dokoki Abdu Alh Dauda Karkarna.
4.Masu Girma Ciyamomin Hadejia da Auyo da k/Hausa da Kaugama da m/madori da Guri da birniwa daKirikasamma.
5.Masu Girma yan majalissar Hadejia, Auyo. K/hausa, Kaugama, M/madori da Guri da Birniwa da Kirikasamma
6.Mai Girma kwamishinan matasa da raya al'adun gargajiya Alh Babandi Muhammad.
7.Alhaji Salisu Sambajo MFR

Masu Rera Waka;

1.Alh Aminu Ladan Ala
2.Fati Niger
3.Saddiq zazzabi
4.Surajo mai Asharalle
5.Dan Kwamarado

Masu Gabatar da Taro

1.Alh Baffa Bura FNICPR
2.Alh Umar Kiyari Jitau Madamuwa
3.Salmanu Adamu Rishi.

Allah ya bada ikon Zuwa.

Tuesday, October 22, 2013

KA SAN KANKA DA KANKA! (TAMBAYOYI 50) DAGA HARUNA AMINU HARUNA.

Hadejia A yau!

Muna cikin wani zamani, da mutane, sunfi damuwa da bayani akan wasu fiye da kansu, sunfi binciko laifin wasu fiye da nasu


Sayyadina Umar yace kuyi wa kanku hisabi kafin ayi muku, Abubawanda suke jawo tsira, Bautawa Allah shi kadai da Iklasi, akan sunnar Manzon Allah, a cikin Akida, da Ibada, Da mu'amalah, da Halaye masu kyau, yiwa kanka tambaya, hamsin don kasan matsayinka :


Allah yasa mu dace :

1- waye ya yika ?

2- mai yasa ya yika ?

3- kai waye ?

4- A ina kake ?

5- mai kake yi ?

6- Ina zaka ?

7- mai zai faru ?

8- mai kafi so a rayuwarka ?

9- mai kafi ki rayuwarka?

10- Duk abinda kakeyi, kana da hujja a sharia?

11- su waye abokanka?

12- Yaya zamanka da iyayanka?

13- Yaya zamanka yake da iyalanka?

14- Wace kungiya kakeyi don me?

15- A kwai wani yanzu haka da bakwa shiri da shi?

16- Tsakaninka da Allah ka taba cin amanar wani?

17 Kanayin karya?

18- Kana Dun guma ashariya?

19- Yaya zamanaka da makotanka?

20- Wace shedar ilmi kake dauke da ita?

21- kana salloli a Jam'i musamman a masallaci?

22- yaya alakar ka da danginka take ?

23- shin kana sada zumunta?

24- shin kana bayar da sadaka ?

25- shin kana karanta Alkur'ani mai girma?

26- kana azumin litinin da Alhamis?

27- kana sallar Shafi'i da wuturi?

28- kana zuwa asibiti domin ziyarar marasa lafiya?

29- Kana yawan saba alkawari ?

30shin kana azumtar kwanaki masu haske, ranar
sha uku, sha hudu, sha biyar?

31- shin kana kiyamul- laili?

32-kana umarni da kyakyawa da hani da mummuna?

33- kana zuwa aiki akan kari kuma ka tashi akan lokaci?

34- kana zuwa gaban malami domin daukar karatu?

35-ka tabbatar abinda kake ci halal ne?

36- kana kuwa damuwa da halin da yan uwanka musulmi suke ciki?

37- kana taimaka marayu kuwa?

38- salati nawa kake yiwa Annabi saw kullum?

39- Istigfari nawa kakeyi kullum?

40- kana zuwa makabarta domin tuna lahira?

41- kana zuwa taaziyya da sallar Jana'iza?

42- ka taba yin kuka saboda tsoran Allah?

43- shin kana yiwa dukkan musulmi sallama ko
kuwa sai wanda ka sani?


44- kanayin rantsuwa akan karya kuwa?

45- kana shan taba ko wiwi ko giya ko hodar iblis?

46- kana jin kade- kade, da wake- wake?

47- kana aske gemunka?

48- ka taba karbar cin hanci?

49- kana kyautawa iyalanka?

50- kana gaba da wani kuwa?

Allah yasa mu dace.

Wednesday, September 18, 2013

CIWON KODA A KASAR HADEJIA! DAGA PHARM. HASHIM UBALE YUSUF.

Hadejia A yau! Daga pharmacy Hashim Ubale Yusufu


Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu Alaikum.

CIWON KODA A KASAR HADEJIA: A bisa kididdiga, kimanin mutane miliyan talatin (30million) ne ke dauke da cutar Koda a tarayyar Nigeria. (National Association of Nephrology). Yawancin wadannan mutane na mutuwa kuwa katsam daga cutukan da suka shafi makwarar jini da zuciya, wanda ke da danganta da ciwon kodar. Wannan ya nuna cewa kimanin mutane ashirin bisa dari (20%) na ‘yan Nigeria na fama da wannan ciwo, wanda ana ganin alama daga yawan karuwar masu neman tace jini (dialysis). A wasu asibitocin zaka iske kimanin mutane 200 zuwa 300 ke zuwa neman tace jininsu a rana.



Cututtuka da dama na iya jawo ciwon Koda. Manyan dalilan dake hassada wannan ciwo anan karkarar sun hada da ciwo tsutsa (infections), kishirwa da kuma shaye shayen magunguna kai tsaye, Hawan Jini, shan taba da makamantansu.
Ita koda tana taimakawa jikine wajen tace dattin da kan taru a jikin mutum, sannan kuma tana taimakawa wajen tsotse ruwa, da sukari da sauran sinadaran gina jiki dake yawo a jini domin kar su bi fitsari su fice. Kenan zamu iya gani cewa idan har Koda bazata iya yin wannan tatar ba, to kuwa akwai matsala. Babban abun dazai faru kuwa shine, dattin na iya tare kofofin da jini da fitsari zasu bi, daga nan sai a fara kumbura, da kuma samun zazzafan ciwo na fitar hankali a hanyar da fitsari yake bi.




Sau tari zaka tarar mutane na aikin dake sa su zubad da gumi mai yawa, amma babu ruwa a kusa dasu. A kauyuka da rugage, zaka samu rijiyoyi sun kafe, ko kuma zasu sha ruwa gurbatacce, saboda ba inda zasu samu ruwan mai kyau su sha. Wannan bala’i ne.
Sannan kuma, yanzu wani abu wanda yake kamar gasa shine shaye shayen magunguna babu dalili ko kuma babu neman shawarar masana.




Wannan ka iyasa shan gurbatattun magunguna ko na jabu wadanda zasu iya cutar da ita kodar ta daina aiki. Haka kuma shaye shayen maganin gargajiya na daya daga cikin abubuwan da ke jawon wannan ciwo.
Akwai gazawar kayan aiki a asibitocinmu na tace jini da musayar koda, wanda hakan na jawo matsalar kai marasa lafiyar kasashen waje don warkarwa. A inda kuwa babu halin haka, sai addua kenan.

Tuesday, September 17, 2013

MARIGAYI SARKIN DOGARAI DA SAURAN MARIGAYA...

ALLAHU AKBAR! A Satinda ya Gabata ne Masarautar Hadejia tayi Rashi Bubba wanda Tarihi bazai Manta da wannan Rashi ba.


A cikin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar Hatsarin Mota a Hanyar Kano, Mutum goma sha daya ne! A wannan hoto kuma akwai Sarkin Dogarai da Galadiman Dogarai da Madakin Dogarai da Wamban Dogarai da Makaman Dogarai da Magayakin Dogarai da Garkuwan Dogarai da Chiroman Lema da Shitu Dogari da
Manu Mai Hoto.



Ya Allah Muna Rokonka da sunayenka tsarkaka Allah ka Gafarta musu. Amin.
Hadejia A yau!

SARKIN DOGARAN HADEJIA
Free Web Proxy
WAMBAN DOGARAI.Free Web Proxy
Galadiman Dogarai Free Web ProxyMadakin DogaraiFree Web ProxyFree Web Proxy Free Web ProxyImage Hosted by ImageTitan.com[URL="http://img4.imagetitan.com/img4/small/8/8_s.dogarai.jpg" border=0 alt="Image Hosted by ImageTitan.com">Image Hosted by ImageTitan.com KOLI DIREBA
Free Web Proxy SHITU DOGARI
Free Web Proxy

Sunday, September 8, 2013

****TAURARINMU HADEJIAWA PART SIX(6)****

Free Web Proxy
Hadejia A yau.. Daga Muhammad Idris.
A ci gaba da kawo muku Tarihin wadanda Suka baiwa Kasar Hadejia Gudunmawa, yau Mun Tabo kadan daga Tarihin Marigayi Shatiman Hadejia Alh. Hassan Abbas.
****SHATIMAN HADEJIA ALHAJI HASAN ABBAS*****

Marigayi Shatiman Hadejia yana daya daga cikin dattijan arewa,manya a jihar kano da jigawa.Ya fara aiki tun daga Native Authority(NA) daga nan ya koma tarayya.Ya rike mukamin karamin ministan fetur a zamanin IBB. Shatiman Hadejia mutum ne mai kishin kasa da rikon addini. Shi ne sanadin aikin mutane da yawa a kaduna kuma har ya rasu akwai mutane da dama a zaune a gidansa.


Shatima ne ya fara gina katafaren gida domin saukar bakin kunya a Hadejia. Shi ya dauki dawainiyar
gyaran masallacin juma'a na lokaci mai tsawo.


Ya dauki nauyin sayen likkafani ga mamata har tsawon rayuwarsa. Arzik insa ya amfani 'yan uwa da sauran jama'a matuka domin akwai wadanda ya dauki nauyin ba su albashi har ya koma ga Allah subhanahu wa ta'ala.Muna addu'a Allah subhanahu wa ta'ala ya ji kansa ya albarkanci zuriyarsa.
Daga Muhammad Idris.

Wednesday, August 28, 2013

DANGANTAKA TSAKANIN BIRNI DA KAUYUKAN KASAR HADEJIA. DAGA M. HUSAINI SHEHU..

Hadejia A yau!
Daga M. Hussaini Shehu


DANGANTAKAR BIRNI DA KAUYE

Dangantaka tsakanin birni da kauye a kasarmu ta Hadejia tanada tsohon tarishi. Yana da wuyar gaske kasami bahadeje ko bahadejiya dake birni ko kauye da bashi da gidan yan’uwa ko gonar gado a daya daga wadannan wurare dana ambata.DA

Bukukuwan sallah-: shekarun baya zakaga kowane gida cike da baki yan’uwanmu na kauye sunzo cikin Hadejia domin sada zumunci da juna da kuma kallon buku kuwan sallah.

Wannan al’ada tamu tataimaka wa kasarmu sosai wajen jaddada hadinkai a tsakaninmu , kuma tataimaka wajen kawarda kyama tsakanin junanmu. Yanzu a wannan zamani irin wannan kyakkawar al’ada tamu tazama tarishi, sai ayi bukukuwan sallah a
gama bazakaga kowa a gidajenmuba. Kai koda wakilan kananan hukumominmu dawuya kasami guda uku daga cikin takwas sunzo domin sada zumunci kamar yadda akeyi a shekarun baya.


Kuma abin mamaki saika iske sauran masarautu bahaka sukeba, zakaga kowane shugaban karamar hukuma yazo sun hallara domin tattauna matsalolin wannan masarauta.




Shin minene yajawo
hakan? Nomi jide-: Inna tsammanin wannan al’ada tamu itace tasa ake cemana “Hadejia tsintsiya madaurinki daya”. Watau dadama daga cikin mutanan dake cikin Birnin Hadejia a shekarun baya sunada gidajensu nagado dakuma gonaki a kauyuka, aduk lokacinda damina ta sauka sukan koma gidajensu dake kauyuka
domin yin noma. Bazasu dawo gariba sai bayan damina. Zan iya tunawa mahaifina wata shekara muna shira game da wannan dabia tamu, sai yace mini: aduk cikin lokonmu gidanmune kawai yake ragewa da mutane idan damina ta sauka. Sauran makwabta kowa yakan koma kauye dominyin noma.


Saboda haka yan’uwa tayaya idanba hudubar shedanba zamu banbanta mutumun birni da kauye? Amsata shine duk mutumin kauyen Hadejia Dan Garin Hadejia ne sannan kuma duk mutumin Birnin Hadejia dan kauyen Hadejiane.


Tambaya anan itace idan Maganar danayi a baya gaskiyace, shin akwai maana idan mukayi maganar rabuwar kawuna tsakanin mutumin kauye dana birni?


Ga-manda-: wannanma wata tsohuwar al’adace tamu ta Hadejiawa da take kara nuna mana karfin dangan taka tsakanin kauye da birni. Bayan al’adar Nomu jide wanda kamar yadda nafadi a baya take nufin zuwa kauyukanmu da damina donyin noma, idan mungirbe mu kwaso amfanin zuwa gidajenmu na birni. Ha’ilayau mutumin birni musamman ma Mata sukan je ziyarar yan’uwa kauyu kammu bayan an kawo amfanin gona gida.


Ayayinda zasu tafi sukanyi guzurin
kayan miya wanda baa fiya samunsu a karkaraba, sukuma ayayin da suka gama zayararsu, yan’uwanmu na kauye sukan basu
amfanin gona kamar su: gero, dawa, wake dadai sauransu domin yin guzuri. Inna tsammanin wannan alada tamu haryanzu tananan anayinta tsakaninmu, to kaga kuwa ashe idan akwai wadannan dagantaka to ashe gaba dayanmu Hadejiawa yan’uwan junane. Saboda haka miye dalilin rabe raben kawuna tsakanin kauye da birni?




Sarauta-: Kowa yasani Sarautarmu ta Hadejia dama ta sauran kasashen Hausa ana nada Mai sarauta watau hakimi ko dagaci daga cikin yayan sarakai dake cikin gari a turasu kauyukammu domin yin mulki. Sannan ayayin
da hakimi zai tare kasarsa yakan tafi da sauran yaransa wadanda zasu tayashi mulki yazuwa kauye. Kuma dadama daga cikinsu idan sukaje zasu auri mata acan daganan sunzama yan can kauyen.


Shiyasa duk wani mai sarauta ko yaran mai sarauta a kauye idan aka binciki tarishinsu zaka iske zuwa yayi tare da hakiminsa ko dagacinsa Watau mutumin birnin Hadejiane, musamman ma da ya kasance al’adarmu ta Hadejiawa ta banbanta data Kanawa maana duk wanda fada ta tura kauye domin wakilci to zai zauna ne dindindin watau babu canji. Shiyasa idan shekaru sukayi yawa bama iya gane cewar zuwa mukayi donyin sarauta ba a nan muke ba shekarun baya. To amma abin mamaki saika iske yaron hakimi ko dagaci yana korafin nuna banbanci tsakanin birni da kauye. Shin akwai ma'ana a wannan dabia?


Allah yasa mugane.

Sunday, August 11, 2013

JAWABIN ALH. BAIDI GAJO YELLEMAN A BUBBAN TARO DA AKAYI DON HADIN KAN Al'UMMAR MASARAUTAR HADEJIA. (KASHI NA DAYA 1)

Free Web Proxy
Jamaa Salamu Alaikum. Na tsaya gabanku ne a game da izinin da aka mani akan in yi bayani gameda “Cusawa matasa kishin masarautar Hadejia”. Shi dai kishi wani kauna ne da mutun yake dashi na wani abu, ko Kasa, Addini, Mutum da sauransu. Misali Kishin da mutum yakewa kasarsa, Mace da take game da mijinta, mutum yake game da addinsa. Wannan tsanannin kishin zai iya sa mutum yayi dukkan abinda zai iya domin yaga cewa ya amfani abinda yake kishin kuma yakare
martabarsa. Kakan yi amfani da kishi don ka cimma kyakkyawar manufa mai amfani.


Wani babban alamarine da zai sa kayi duk abinda zaka iyayi iyakar karfinka domin shi wanda kake kishin ko abinda kake kishin.


Kasar Hadejia al’ummace da Allah Yayiwa dimbin albarka ta fannoni daban daban na rayuwa Kamar dimbin masu Ilimin addini dana zamani, Manyan Sarakuna, Attajirai, Manyan yan siyasa, Manyan Maaikata tun shekaru aru aru. Idan nace kasar Hadejia ina nufin Hadejia, Auyo, Birniwa, Guri, Kafin Hausa, Kaugama, Kiri kasamma da Malam Madori.


Bari muga yanda maganar kishi ta shigo a harkar jamaar Hadejia. Sanin kowane cewa yakamata ace Hadejia ta wuce inda take dinnan kasancewarta Mai sarautar daraja ta daya tun shekaru aru aru, kuma mutanenta ne suke mamaye aikin Gwamnati tun Kano State har yanzu a Jigawa State sannan kuma a gwamnatin tarayya. To amma har yanzu mun san akwai sauran abubuwa da yawa da muke bukata don mu cimma burinmu na samarda abubuwan more rayuwa ga jamaarmu. Su
wadannan abubuwan more rayuwa kuma suna samuwane ta hanyoyi daban daban. Jamaa zasu taru su hada karfe da karfi don su
samarda wadannan abubuwa.


Amma almuhimmi shine abinda zaa samowa jammaa daga hukuma, wato Gwamnati.
Hanyoyin samu wadannan abubuwa shine zai nuna tsananin kishin da zakayi na samosu daga hukumar da abin ya shafa. Babban
maaikacin Gwamnati zai iya samawa matasa aiki a gwamnati, zai iya kawo Maaikata (Project), ko Makaranta, Titi, Asibiti. Ko ruwansha a bangarensa. Dan Siyasa zai iya amfani da mukaminsa yakawo duk abubuwan da na lissafa a sama. Attajirai zasu iya kawo kamfanoni. To idan wadannan suka hada karfe da karfi, nan da nan zaka ga
abubuwa sun bunkasa ta kowane fanni kuma jammaa sun sami biyan bukata. Ina tunanin ko muna da irin wannan tsananin kishi da nake nufi anan. Idan kuma muna dashi, to ina tunani ko muna amfani dashi yanda yakamata don ciyarda alummarmu gaba.


In Ciyaman Local Government bashi da kishi, ina zaiyi aiki?


Idan Dan Majalisa bashi da kishi, ina zai yiwa jamaa kyakkyawan wakilci?


Idan babban maaikacin gwamnati bashi da kishi, ina zai kawo ayyuka (Projects) garinsu?
Da sauransu.


Anan ina so inyi wasu yan tambayoyi: MU HADU A KASHI NA BIYU (2) DON JIN TAMBAYOYIN.

JAWABIN ALH. BAIDI GAJO YELLEMAN A BUBBAN TARON HADIN KAN AL'UMMAR MASARAUTAR HADEJIA. (KASHI NA BIYU 2)

Free Web Proxy Hadejia A yau.


Anan ina so inyi wasu yan tambayoyi:


1. Kana da kishi ne sai ka jira Mai Martaba Sarki ya tura ma tawaga a gaya maka jamaar Hadejia suna bukatar abu?


2. Kana da kishi ne sai ka jira har jamaa sunyi zanga zanga kafin ka biya musu bukata?


3. Kana da kishi ne baka son zuwa garinku ko cikin jamarka?


4. Kana da kishi ne kake yiwa garinka shigar dare kuma a mota mai tinted glass don kada a ganka?


5. Kana da kishi ne zaka rike mukamin gwamnati har kayi ritaya baka kari jamaarka da komai ba? Da sauransu.


Shi kishi ne zai sa kayi abu ba sai an sa ka ba, kuma in kayi ba sai an gode makaba. Rashin wakilci mai kyau duk rashin kishi ne yake kawo shi. Saboda haka idan dai muka dore akan wadannan abubuwa biyar da na lissafa a sama, to gaskiya babu inda zamu.


A duniyarmu ta yau, da wuya wani ya dafa maka abinci ya sa ma a bakinka. Kai ne zaka yunkura ka nemowa kanka yancinka ko kuma abinda zai amfaneka. Sabida haka dole musa kishi a zukatanmu don mu samowa lardinmu abinda yakamata daga gwamnatin Jiha har gwamnatin tarayya.
Babban burinmu shine mu sami Jiha (Hadejia State). Domin idan ka sami jiha, to duk wasu abubuwa na ci gaba zasu zo da sauki.


To amma kafin mu sami jihar, yakamata muci gaba da amfani da dimbin arzikin da Allah Ya bamu na masu ilimi, Sarakuna, maaikata,
manyan yan siyasa da yan kasuwa domin cimma duk wani cigaba da muke bukata.


Alhamdulillahi muna da Manyan maikata kamar Directors Permanent Secretaries, Ministoci, Soja, Yan Sanda da sauransu. Idan muka hada karfe da karfi muka sa kishi a alaamuranmu babu inda bazamu kaiba. Tarihi ya nuna akwai inda mutum daya mai kishi ya kawowa jamaarsa cigaba.
Saboda haka kara jaddadawa iyayenmu da yayyenmu da kuma musamman matasa manyan gobe gameda duk abinda zasuyi su sa kishi da hadin kai a gaba. Mu zama tsintsiya madaurinki daya muna haduwa da juna muna tattaunawa muna tsaida shawarwari kuma muna daukan dukkan matakin da yakamata don muga cewa mun cimma burinmu.
Matasa kune kunnenmu, kuma kune idanunmu. Saboda haka duk abinda yakamata Jamaa su sani, ku yakamata ku jaddadashi domin a dauki mataki. Har abada yin shiru baya warware matsala sai dai ya kawo rashin jituwa marar amfani Allah Yasa wannan taro ya zama dalilin samarda hadin kai da cigaba ga alummar Hadejia da Jigawa baki daya.

Wednesday, August 7, 2013

HAWAN SALLAR AZUMI NA 8/8/2013 ALHAMIS.

Hadejia A yau. Daga Muhd Yawale Hadejia >


kamar yadda Aka sani Hawan sallar Azumi yana da tarihi mai tsawo a cikin Garin Hadejia, wannan sallar ma A bisa al'adar masarautar hadejia ranar sallah maimartaba sarki zai fito daga gida da safe, akafa tareda sauran mutanan fada domin zuwa filin idi. Dukda cewa za'ayi sallar ne a Bubban Masallacin Juma'a na cikin gari. Sakamakon ruwan sama da akayi kuma yayi ta'adi, Mai martaba sarki ya dage Hawan sallah domin Jajantawa ga wadanda ruwa yayi musu ta'adi.


Ga bayanin yanda Hawan sallah yake kasancewa da kuma ta Gurarenda ake bi. Bayan an idar sallar idi liman ya kammala huduba,sai hakimai da sauran mahaya dawaki su hau, sannan maimartaba shima zai hau dokinsa tare da Dandalmu, zai bi ta kasuwar kuda zuwa Titin yahai zuwa makera, sannan zai bi ta makwallah zuwa kofar Liman.


Idan maimartaba sarki yazo daidai kofar liman yakan tsaya domin karfar Jafi daga Hakimai. Wanda hakan ta samo Asali ne Tun Lokacinda Sarkin Hadejia Muhammadu Mai shahada ya dawo daga Yakin Madarumfa, ya tsaya a wannan Gurbin Inda su Jarumansa suke zuwa suke masa Jinjina. Amma a lokacin yana Hakimi ne kafin ya zama sarki. Bayan ya zama sarkin Hadejia sai ya maidata Al'ada wato duk sallar Azumi da Layya zai tsaya Hakimai suzo suyi masa jafi.


Daga nan kuma sai maimartaba sarki ya karasa rumfar manyan baki domin gabatarda jawabin sallah, bayan nan kuma sai maimarta ya karasa gida ya sauka tareda sauran hakimai.


Wannan shine Bayanin Hawan sallar Azumin wannan shekara a takaice da fatan Allah yasa ayi hawa lafiya a sauko lafiya. Allah yaja zamanin maimartaba sarki.

Friday, August 2, 2013

TAKAICACCEN TARIHIN SHEIKH ISAH WAZIRI (WAZIRIN KANO)

HADEJIA A YAU!
Shekh Isah Muhammad Gidado wanda akafi sani da Mallam Isah Waziri.. An haifeshi a cikin garin Kano a shekarar 1925, kuma Da ne ga Wazirin kano Muhammadu Gidado. Yayi karatunsa na Allo a ciki da wajen kasar kano, sannan ya halarci makarantar koyon Aikin Shari'ah a cikin garin kano, daga bisani ya tafi Jami'ar Al-Azhar dake Egypt Inda ya karasa karatunsa. Kuma ya samu ilmin shari'ah da Koyarda Ilmin Addinin Musulunci.




Bayan ya gama karatunsa Sheikh Isah Waziri ya dawo kano inda ya fara aiki a Ma'aikatar Shari'ah ta kano, a matsayin Clerk daga bisani ya zama Registrar. kuma ya fara Tafsirin Alqu'ani mai tsarki a Garin Zakirai ta karamar hukumar Gezawa a wancan lokacin.




Bayan ya bar Aikin Gwamnati Mai martaba Sarkin kano Alh. Ado Bayero ya nadashi Limamin Masallacin Murtala dake kano, kuma anan yaci gaba da Tafsirin Alqur'ani mai girma. Shekh isah Waziri ya bada gudunmawa da dama a cik da wajen kano wajen Daukaka Addinin Musulunci, kuma yayi kokari wajen ganin anyi aiki da Shari'ar Musulunci a kasar kano ganin cewa Mafiya yawansu musulmi ne!




Sheikh Isah Waziri ya samu wannan sunan ne a lokacin yana Makarantar koyon aikin Shari'a Inda wani Malaminsu mai suna Sheikhul-Bashir yake fada masa ganin cewa Da ne ga Wazirin Kano Gidado. A maimakon yace masa Isah Muhammad Gidado, sai ya takaita sunan yake kiransa Isah Waziri.




Bayan da Limamin kano Kuliya ya tafi Aikin Ambasada a shekarar 1998, Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero ya nada Shekh Isah Waziri a Matsayin Bubban Limamin Kano. Sannan daga bisani An nadashi Wazirin Kano bayan da Dan-uwansa Wazirin Kano ya rasu.




A yau Juma'a 2/8/2013 azumi yana 24 Allah yayiwa Sheikh Isah Waziri rasuwa. Muna rokon Allah ya Gafarta masa ya kyauta Makwancinsa. Muma in tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani.

Friday, May 31, 2013

YAKIN SARKIN HADEJIA BUHARI DA SARKIN MARMA...

Image Hosted by ImageTitan.com HADEJIA A YAU! A lokacinda Sarki Buhari ya samu Labarin wani Doki Mai kaho a Marma, sai ya nuna sha'awarsa akan wannan Doki. Sarkin Hadejia Buhari sai ya Rubuta Takarda zuwa ga Sarkin Marma cewa.. Yaji Labarin Dokin nan, yanaso ya bashi kyauta ko ya saida Masa.

Sarkin Marma sai yayi Bankama yace Tunda Sarkin Hadejia Buhari Mayaki ne sai yazo ya kwata, sannan yace ba'a haifi mutuminda zai rabashi da wannan Doki ba!

Koda Jakada ya dawo sai ya sanarda sarkin Hadejia Buhari duk Abinda sarkin Marma ya fada. Hadejia A yau! www.Hadejiawa.wordpress.com Da Buhari yaji Haka sai yace Babu komai ku kyaleshi zamuyi Maganin mai Bankama.

Sarkin Hadejia Buhari ya sanarda fadawa cewa.. Gobe zamuje Marma, sukayi adduah Allah ya kaimu. A lokacinda Mayakan Buhari suka shiga Marma sai suka Dannawa Garin wuta sai mutane suka fara Guduwa suna ta kansu, da Sarkin Marma yaji ana Gudu sai ya tabbatar cewa Sarkin Hadejia Buhari ne yazo. Sai sarkin Marma ya dauki Takobi ya shiga Bargar Dawakansa sai ya sare wuyan wannan Dokin Mai kaho, wanda shine dalilin da yasa Buhari yazo ya yakeshi..

Bayanda Mayakan Hadejia suka kewaye Garin Marma sai Sarkin Hadejia Buhari ya zaburi Dokinsa bai zame ko Ina ba sai kofar sarkin Marma, da yaje sai ya wuce Bargar Dawaki dan ya kama Dokin nan mai kaho sai yaganshi a kwance cikin jini. Hadejia A yau.

Sarkin Hadejia Buhari ya sa aka kamo sarkin Marma yace masa Banyi niyyar Kasheka ba, nazo kawai Na kwace Dokinda kace Inzo in kwata, Amma tunda ka sare masa kai kaima sai an sare maka kai. Sarkin Hadejia Buhari ya kashe Sarkin Marma suka dawo Hadejia. Hadejia A yau.

A gaba zan kawo muku Tarihin Bulalar Sarkin Hadejia Buhari, da yanda akayita da kuma wadda yayita. Hadejia A yau..

Tuesday, May 28, 2013

SARKIN DOGARAI DUMAMUSAU...

Image Hosted by ImageTitan.com HADEJIA A YAU! Buya Mai Komo yana cewa.... Buzuzu baka dadin tauna Dorawa kashe mai zari, yai baki kirin da idanu yai jan idon Barkono, Jakarsa bata rama in ba damo da Macizai. Ya zama Gwanki matattarar 'yan kwari tsumma Madaukar cuta! Shine yakan zama gwanki matattarar Iblisai. Na kumbita kazamin gwarzo, Dan makama ka wuce kushe koda a dajin Gaba. Bawa tsare Sarkinka koda a Dajin Gaba. Baleru baban yaya, Sarkin Dogaran Hadejia, Shine yakan zama Gwanki Matattarar iblisai. Mata kubar kallonsa kayansa babu na zabe. Auya batai laya ba sai malami ya yarda! In malami ya yarda kudi biyan laya ne! Allah ya kyauta Kwanciya...

Saturday, April 27, 2013

TAURARINMU HADEJIAWA (4)

Image Hosted by ImageTitan.comHadejia A yau! Allahu Akbar!

ALH. ABDUL'AZIZ DANMASAGA :- Hakika Tarihin Hadejia bazai manta da wannan bawan Allah ba, yayi iya kokarinsa wajen taimakon rayuwar mutanen kasar Hadejia, musamman Talakawa Masu karamin karfi da Miskinai.

Yayi Amfani da Arzikin da Allah ya bashi ya kyautatawa Jama-ar kasar Hadejia. Allah ya gafarta masa.

Alh. Abdu Danmasaga Mutum ne mai fara'a da son ci gaban Al'umma, baya so yaga mutane suna zaman banza. Hakan tasa yake daukan mutane ya sanyasu Inda zasu koyi sana'a domin su dogara da kansu. Shine mutuminda duk ranar Juma'a ko Lahdi yake raba kudi ga 'yan makarantar Boarding, saboda yasan basa kusa da Iyayensu.

Ga kadan daga Ayyukansa da yayi na Alheri.

(1) yana sayen itace mota mota ana faskarawa a tarashi kuma a saidashi lokacin da yayi wahala akan kudi kadan.

(2) Ba'a fara sayan Itace ba a Makabarta sai bayan mutuwarsa, saboda ya bada fisabilillah. Allah yasa yana Aljannah.

(3) yana saida kalanzir a kankanin farashi musamman lokacinda watan Azumi ya karato ko kuma lokacin Damina.

(4) yana saida fetur a farashi mai sauki yayinda ake wahalar sa. Ko ya zama babu a gari.

(5) shi yake sakawa ayiwa Mahaukata Aski, ya basu Abinci kuma ya dinka musu sabbin Riguna.

Dama ace masu kudi ko 'yan siyasa zasu koyi hali Irin nasa, da kasa ta kwana lafiya!

Allah ya Gafarta masa, Allah yasa mu koyi Hali Irin nasa. Alh. Abdul'aziz Danmasaga. Hadejia A yau.

Sunday, April 21, 2013

TARIHIN SARKIN HADEJIA UMARU DAN BUHARI DA ZUWAN SARKIN DAMAGARAM HADEJIA..

Image Hosted by ImageTitan.comHADEJIA A YAU!



SARKIN HADEJIA UMARU: A SHEKARAR 1863 allah ya yiwa Sarkin Hadejia Buhari rasuwa a Yakinsu da sukayi da Gogaram (bade). Ko da aka dawo Hadejia aka binne shi sai Manyan fadawan Hadejia wadanda akwai Amana tsakaninsu dashi Buhari. Kamar SARKIN AREWA TATA GANA DA SARKIN YAKI JAJI suka jajirce Sai an Nada UMARU DAN BUHARI SARKIN HADEJIA. kuma hakan Akayi!


SARKIN HADEJIA UMARU NA BIYU an nadashi yana da shekara Goma sha Takwas (18). Kuma manyan fadawan Mahaifinsa sune suke gudanar da Sarautar tunda shi yaro ne. Kuma a zamaninsa Sarkin Damagaram Tanimu ya kawo yaki Hadejia. Kuma yayi sansani a Arewa da Hadejia daga nan har Jigawar Kasim mutanensa ne. saida yayi kwana Arba'in ana yaki amma Hadejiawa basu fasa wasanninsu na dandali ba. Sannan kuma basu fasa duk harkokinsu na kasuwa ba, su kuma mutanen Sarkin Damagaram suna kaiwa farmaki kauyuka suna kwace musu kaya! Sannan sun hana mutanen kauyuka shigowa Hadejia domin saye da sayarwa. A nan kuma sun hana Makiyaya kiwon Dabbobinsu, Sai sarkin Arewa yasa akayi sanarwa a Hadejia cewa: duk mai dabbobi gobe ya sako su za'a kaisu kiwo, kuma hakan sukayi suka saki dabbobinsu Sarkin Arewa da Mutanensa sukaje sukayi kiwon suka dawo. Ta wajen Dan-Rago kusa da Maficin Sarki.

Da Abin ya ishi Mutanen Hadejia sai suka Sanar da Sarkin yakin Hadejia Jaji, sai ya tara Fadawan Hadejia yace Naji ance Sarkin Damagaram yazo, Yau wajen kwana 40, sukace hakane! Sai sarkin Yaki yace so kuke yazo ya koremu daga Garin?

Da safiya tayi sai sarkin yaki Jaji ya hau dokinsa ya dauki Takobinsa ya fita yacewa sarkin Kofa in ya fita ya rufe Kofar Gari, kuma ko an koroshi karya sake ya bude, idan ya bude masa to zai kashe shi. Sarkin yaki Jaji yaje ya fara baza Mayakan sarkin Damagaram yana korasu, saida ya korasu har Rumfar Sarkin Damagaram ya dawo da niyyar Washegari aci gaba da yaki.

Da sarkin Damagaram yaga anyi haka sai ya tara Hakimansa da fadawa yace gobe zamuci Hadejia da yaki. Suka amsa suna Alwashi, bayan an baje sai Chiroman Damagaram ya samu sarki yace masa Shawara nazo in bayar, sarki ya yarda. Chiroma yacewa Sarkin Damagaram duk garin da mukaje musu yaki basu da sukuni saboda suna tsoronmu, Amma yau kwananmu Arba'in (40) Hadejiawa basu fasa duk abinda sukeyi ba! Kuma mun samu Labarin Sarkin Hadejia bai san munzo ba, yacewa sarki Ina ganin ya kamata ko mu shiga mu yakesu ko kuma mu koma Gida!

Wata rana ana yaki Sai aka harbi dokin Sarkin Arewa! Koda ya mutu sai akaje gida aka dauko wani Dokin aka cire kayan wancan Dokin aka sakawa wanda aka kawo. Tata gana ya koma kan doki, kashe gari ana cikin yaki sai Tata gana ya sauko daga Dokinsa yayi alwala ya koma kan Dokin, to ashe Sarkin Damagaram yana kallon su sai yace Lalle Sarkin Hadejia ya Isa ana yaki ka sauko kayi alwala? Jiya ma an kashe masa Doki amma saida akaje aka dauko wani a gari? Sai Zagin Sarkin Damagaram yace ai ba Sarkin Hadejia bane Yaronsa ne! Sai Sarkin Damagaram Tanimu yace to Ina Sarkin Hadejian? Sai zaginsa yace ai ance yana gida tunda aka fara yakin nan bai taba zuwa ba. Sai sarkin Damagarm yace wa fadawansa Gobe zamu bar Hadejia kar mu tsaya ayi ta kashemu. Saboda Sarkin Hadejia ya raina mu kwananmu Arba'in amma bai taba zuwa anyi yaki dashi ba? Wa yasan me zai mana in ya zo? Amma basu san Sarkin Yaro bane. Washe gari suka juya suka koma Damagaram. Kuma lokacinda sukazo Hadejia Da kaka ne! Anyi girbi Manoma basu gama Tare Amfaninsu ba. Shi yasa suka dade a Hadejia saboda akwai abinci da ruwa a kusa dasu.

SARKIN HADEJIA UMARU Mutum ne mai son Nishadi kowane Lokaci yakan fita Bakin kogi ko Gona Domin Debe kewa. Kuma anyi amfani da wannan Damar inda wata rana ya fita sai aka Rufe Masa Kofa. Koda yazo yaga kofa A rufe sai ya juya ya tafi Chamo ya zauna. Aka nada Kanin Mahaifinsa Sarkin Hadejia Wato HARU BUBBA. 1865-1885. Shi kuwa UMARU DAN BUHARI yayi zamansa a Chamo kuma Ya rasu a shekarar 1920. Allah yaji Kansu Ameen.

HADEJIA A YAU.

Friday, April 5, 2013

KHUDUBA DAGA MASALLACIN FANTAI HADEJIA...

Image Hosted by ImageTitan.comHADEJIA A YAU! Daga Yaya Ilallah.


~~~ZUWA WAJEN BOKA~~~


Alhamdulillahi Rabbil Alamin. Muna farawa da sunan Allah wanda da Ikonsa komai ya kasance, da kuma Abinda zai kasance! Tsira da Aminci su tabbata ga Manzonsa Muhammadu s.a.w. Wanda ya aikoshi da zance mafi dadi wato Alqur-ani.


Alhamdulillahi Yau khuduba daga Masallacin Usman Bn Fodio dake cikin makarantar Fantai daga bakin Mal. Bashir Muhd Baima, ta yi magana ne ga hani zuwa wajen:- BOKA ko YAN TSUBBU. Wadda a lokacin yanzu shedan ya kada gangarsa wajen haska zukatan ashararu daga cikin mutane kamar 'yan siyasa, masu mulkin gargajiya da na gwabnati da kuma masu rike da wasu mukamai.


Manzon Allah s.a.w yace: Duk wadda ya je wajen Boka, ba za a amsa masa Sallarsa ta kwana 40 ba. In kuma ya yi imani da abun da ya fada, to ya kafurta da abun da Annabin ya zo da shi. Wani abu mafi muni da takaici, za ka ga matasa maza da mata na neman taimakon Bokaye wai da sunan Farin jini, neman mulki, mallakar miji da kokarin mallakewa zuciyar abokin soyayya ga samari da 'yan mata.


Haka dabi'ar ta kara watsuwa cikin zukatan wasu jahilai ta yadda in wani abu na musiba ya samesu , sai su tafi ga Boka don gano yadda wannan abu ya faru a gareshi. Ya manta da Allah ne ya Qaddara masa. Toh Allah kyauta.


Masu irin wanga dabi'a Allah shiryesu, mu kuma Allah ya karemu. Amen.

Monday, March 25, 2013

TAURARINMU (HADEJIAWA) PART THREE (3)

HADEJIA A YAU.


DAGA M. MUHAMMAD IDRIS HADEJIA.


SHEIKH USMAN KADUNA *************** ­ Sheikh Usman Kaduna,daya daga cikin manyan malaman Jihar Jigawa,kololuwa­r malunta a masarautar Hadejia, daya daga cikin jigogin "council of ulama" na jihar jigawa, shehi kuma madugun tafiyar Darikar Tijjaniya a masarautar nan. Gaba daya rayuwar malam akan yada ilmin addini ta kare.

Malam ya yi aiki a L.E.A a matsayin babban inspector na Arabiya.Ya sha yin Board Member a Hukumar Alhazai ta jiha.

Gidan malam jami'a ce ta masarautar Hadejia. Malam malamin malamai ne domin duk wani malami mai shekaru saba'in zuwa kasa in malam bai karantar da shi ba to ya karantar da malaminsa. Malam ­ ya yi nisa a fagen bayarda ilmi domin har daga kasashen ketare ana zuwa wannan jami'a tasa.


Almajiran malam ne suka fara kafa Islamiya ta dare domin magance hira marar amfani da matasa kan yi a cikin wannan gari.

Malamyana gabatar da tafsiri a kowane watan azumi a dukshekara wanda ke samun halartar jama'a masu yawa. Bayan karantarwa ta yau da kullum malam yana karantar da hadisi a ranar kowace juma'a tsakanin magariba da isha'i. Allah ya karawa malamlafiya ya kuma ba shi ladan Ayyukanda yake na Alkairi.


ALHAJI HASHIMU AMAR(WAZIRIN HADEJI)*************** ­* Alhaji Hashimu Amar yana daya daga cikin tsofin 'yan bokon wannan masarauta, ajins­u daya da marigayi sarkin Hadejia Alh. Abubakar maje tun daga firamare har midil (Middle).


Alhaji Hashimu Amar a"internal revenue" ya yi aikinsa har ya kai kolokuwawato babban Darakta kuma anan ya yi ritaya. AlhajiHashimu ya dauki ma'aikata matuka a wannan masarauta har ma da wajenta.

Alhaji Hashimu dattijo ne mai gaskiya da rikon amana ya kare mutuncinsa da na masarautarsa matuka don haka wajen daukan aikinsa bai nuna kabilanci ba, babu ruwansa da kusa ko nesa, ko na gari ko kauye.

Wannan ya kara masa mutunci matuka a wannan masarauta. Alhaj­i Hashimu ya zama wazirin Hadejia a lokacin Marigayi Sarkin Hadejia Alh. Abubakar Maje kuma kullum yana hanya domin samo ci gaban wannan masarauta.

Hadejiawa suna masa addu'a Allah ya albarkanci zuriyarsa.

Saturday, March 23, 2013

HADEJIA EMIRATE

HADEIJA A YAU.

Authority : Mr. A. Campbell-Irons.

The Emirate of Hadejia contains an area of 2,768 square miles, and is divided into six Districts. It is situated to the north-east of Katagum, in the Northern Division. It is a disputed point whether in the tenth century.

Hadeija or Gobir formed one of the seven Haussa States. In the Kano Chronicle there is a mention that the son of the Sarkin Machina came to Kano in the reign of Yakubu (1452-63) and was made Chief over Hadeija, with the title of Sarkin Gabbas.

It became a Fulani Emirate at the time of the Jihad, Sambo receiving a flag from Othman Dan Fodio. His elder son Buhari made himself King in defiance of the Sarkin Musulmi's edict in favour of his younger brother ; and, obtaining the support of the Shehun Bornu, defeated all opponents. His reign was one long succession of wars and he was finally killed in battle at Gorgaram about 1863.

Hadeija sent in submission to the British in 1903. In 1904 the British occupied the country, but the fifth Chief opposed their advent and was overthrown and killed in 1906, and Haruna appointed in his place. He died in 1909, and was succeeded by the Chiroma Abdulkadir.

In that same year the Beiyut-el-Mal (Baitilmalu) was started.

The population number some 115,448, and consists of Kanuri, Fulani, Auyokawa, Maguzawa from Kano, Koyamawa, Beddawa, Ngizimawa, Mangawa.

There is a town of historic interest in Hadeija named Garungabas, but which in old times bore the name of Biram, which was originally of great influence. It was founded by Arabs from Bagdaza or Baghdad. One Muktari, or Bayajibda, with his younger brother Biram, Migrated west until they reached Birnin Bornu (Kukawa), where the Shehu gave Muktari a town and his daughter in marriage. Muktari was presently compelled to flee, but left his wife on the road, where she gave birth to Biram, who founded Garin Gabbas, Muktari continuing his journey as far as Daura, where he slew the celebrated serpent and married the Queen.

Another version of the legend is that it was Buram, the younger brother, who founded Garingabas.

A descendant of this Arab family still reigns as Chief. Hadejia A yau.

Tuesday, March 19, 2013

TAURARINMU (HADEJIAWA) Part two (2)

Image Hosted by ImageTitan.com Hadejia A yau! Daga M.MUHAMMAD IDRIS.. A cigaba da kawo muku Takaicaccen tarihin wadanda suka bada Gudunmawa a kasar Hadejia, yau mun tabo Mutum Uku wadanda tarihin Hadejia bazai manta dasu ba!


AIR VICE MARSHAL HAMZA ABDULLAHI(RTD) *************** AVM Hamza Abdullahi. Daya daga manyan hafsoshin soja na kasa, daya daga cikin manyan arewa, tsohon Gwamnan Jihar kano, tsohon ministan Abuja, tsohon ministan aiyuka na musamman. Avm Hamza yayi mulki na wata 18 amma ya yi aiki na mamaki a fadin jihar kano.


Aiyukan da suka shafi masarautar Hadejia sun hada da: ginin hanyar Bulangu da Guri, ginin Asibitin Birniwa, K/Hausa da Bulangu, ginin makarantun mata na kaugama da Birniwa, ginin kwaltocin cikin garin Hadejia da gina fadar Hadejia ta zo daidai da zamani. karin streets light. .


Lokacin yana ministan Abuja ko 'yan kwangila da dama sun samu aiki, manyan mutane da yawa sun samu fulotai, ya samarwa matasa karatu a institute of management ta Abujan.


Avm Hamza bayan ya bar Gwamnati ya ci gaba da bayar da gudunmawa domin ci gaban al'ummarsa ya gina katafaren gida domin saukar bakin kunya, ya gina masallaci na juma'a mahadi ka ture ya kuma tanaji makeken fili a yamma da masallacin domin gina makaranta, yana kawo masu Likitocin ido domin masu larurin ido.


Avm yana daukan yara masu karamin karfi ya kaisu Turkish School in sun gama ya nema musu admission a kasa ko a waje,yanzu haka akwai yara biyu a kasar Turkey wanda shi yake daukan nauyinsu. Tsakanin Avm. da masarautarsa akwai kauna domin ba sallar da za ta zo bai yi ta a Hadejia ba sai in ba ya kasa. Muna masa fatan alheri da karuwar arziki mai amfani.



ALHAJI BELLO IBRAHIM AUYO **************** Marigayi Alhaji Bello Ibrahim Auyo. "Agogo sarkin aiki" tsohon malamin makaranta, gogaggen dan siyasa. Ya fara aiki tun daga malamin makaranta har ya kai mukamin sakataren ilmi.


Ya rike mukamin kwamishinan zabe tun muna jihar kano. Ya yi shugabancin karamar hukumar Hadejia har sau biyu. Shi ne shugaban ALGON na kasa.


Alhaji Bello Ibrahim ya fi kowane shugaban karamar hukuma da aka yi a Hadejia aiyuka na raya gari. Alhaji Bello Ibrahim ne ya gina sakatariyar karamar hukumar Hadejia da ake cikinta, shi ne ya gina Asibitin Kofar Arewa da shagunan bayanta, shi ne ya gina kasuwar jan bulo. Bello ya dauki ma'aikata da malaman makaranta masu yawa a zamaninsa. A zamaninsa matasa masu yawa sun samu muhalli domin ya raba filaye da dama a wurare masu yawa.

Misali shi ya raba filin idi kuma ya sanyawa wurin suna Unguwar Mu'azu Hadejia,


ya bayar a fanisau kuma shi ya sayarwa mutane gidajen fanisau, ya raba a gabari, ya raba a Gandun Sarki.

Bello ya yi ginan magudanan ruwa ba adadi a Hadejia. Yayi aiyuka a Auyo lokacin muna hade da ita.

"Turmin tsakar gida sha gwagwarmaya"
Bello mutum ne mai riko da addini, jam'i ba ya wuce shi, ya rike dangi musamman marayu, da azumi a bakinsa Allah ya karbi ransa. Allah ya sa ya sha ruwa a Aljanna, ya yafe masa kura-kuransa.......



ALHAJI ADAMU KWANO *************** Alhaji Adamu kwano tsohon ma'aikacin lafiya ne wanda ya bayar da gudun mawa matuka a wannan fage. Allah ya yi masa fikira kwarai domin shi ba likita ba ne amma yakan yi aikin da ya gagari likitoci.


Adamu kwano ya shahara akan kaciya domin galibin matasan Hadejia da kewaye daga 'yan shekara 30 zuwa 50 duk yawanci shi ya musu shayi.

Alhaji Adamu kwano attajiri ne mai son ci gaban addini, shi ne ya gina makarantun islamiya ta Hudu da Garko da makarantar sakandire ta Aminu Yusuf.

Adamu kwano shi ne mutum na farko da ya yi kokarin gina Asibiti mai zaman kanta sai dai ba ta fara aiki ba Allah (SWT) ya yi masa rasuwa.

Muna rokon Allah(SWT) ya ji kansa yaarzurta mu da masu hali irin nasa. AMEEN.

Monday, March 18, 2013

TAURARINMU (HADEJIAWA) Part One (1)

Image Hosted by ImageTitan.comHadejia A yau! DAGA MUHAMMAD IDRIS HADEJIA


Shirin Taurarinmu zai Rinka tabo takaicaccen Tarihin Mutanen Kasar Hadejia da Irin ci gaban da suka bata, Domin kaima ka bada taka Gudunmawa. Kuma zamu fara da takaicaccan Tarihin.......


ALHAJI HAMZA TURABU *************** Alhaji Hamza Turabu. Bahadeje mazaunin kano. Alhaji Hamza tsohon ma'aikaci ne a Hukumar Aikin Gona ta Jiha. Yana rike da mukamin Director Forestry tun muna kano har muka zo jigawa kuma akansa ya bar aiki.

Dattijo ya yi wa mutane da yawa hanyar samun aiki musamman a Ma'aikatar Aikin Gona kuma shi ne ya assasa filantaishin masu yawa da muke gani a yau fadin kano da jigawa.

Alhaji Hamza mutum ne mai son ya ga matasa sun yi karatu shi ya sa gidansa ya zama mazaunin Dalibai 'yan wannan masarauta har a yau. Hadejawa suna ma addu'a Allah ya albarkanci zuriyarka. Amin.


SHEIKH MUHAMMAD LAMIN KHAN (MALAM MODIBO YALLEMAN) **************** Marigayi Sheikh Muhammad Lamin Khan yana daya daga cikin dattijon 'Yalleman, daya daga cikin malaman addini na wannan masarauta, shine bubban Limamin 'Yalleman.


Malam Modibo ya zaga kasashen Afirka da dama akan neman ilmin addini kuma ya same shi domin ya karantu a bangarori na addini dabam-dabam. Ana zuwa har daga garuruwan makwabta a dauki karatu a wurinsa.


Bayan kasancewar gidansa makaranta ce shi ne ya assasa Makarantar firamare ta Madani da kuma Sakandiren Madani. Matasa da yawa cikin garuruwan 'Yalleman, Dakayyawa, Hadiyin, Ubba, da kewaye a wannan makaranta suke karatu. Malam Modibo ya hada duk wani hali na dattako da ake so,don haka yake da girma a idon jama'a a ciki da wajen wannan masarauta.


Muna addu'a Allah ya sa kur'ani ya cece shi. Amin.


HAJIYA LAMI AMINU KANI *************** Hajiya Lami Aminu Kani 'ya ce a wurin Sarkin Fulanin Hadejia Alhaji Daudu Saleh. kuma matar na hannun daman AVM Hamza Abdullahi, wato Alhaji Aminu Kani. Hajiya Lami tana daya daga cikin tsofin 'yan boko mata na wannan masarauta.


Hajiya Lami babbar ma'aikaciya ce a hukumar bayar da wuta "PHCN" Kuma zamanta a wannan wuri ya amfanar da wannan masarauta matuka domin idan ka kasa masu aiki a PHCN na wannan masarauta kashi dari Hajiya Lami ce ta kai kashi saba'in daga cikinsu PHCN. Mace mai kamar maza.


Hadejawa sun baki Sarkin Fulanin Mata. Muna addu'a Allah ya kara daukaka. Amin.

Saturday, March 16, 2013

SAKO ZUWA GA MASU AMFANI DA FACEBOOK.



Hadejia A yau!Shafukan INTERNET da Wayar Hannu ta GSM....Bincike ya nuna cewa shafin internet na FACEBOOK da wayar hannu ta GSM suna daga cikin ababen dake kara rura wutar fadan addini a Nigeria.

Hakan yana faruwa sakamakon irin yadda mutane ke amfani da su wajen isar da sako atsakaninsu. Mutanen mu suna da son bayar da labari,Inma ingantacce ko mara inganci don neman addu'ar 'yan uwansu ko don nuna bajintar su ko kuma don wata manufa ta su ta daban.

Wannan yasa dayawa sukan fadi abinda basu da tabbas akansa, ko kuma suyi kari cikin labarin na su.

Ya kai dan'uwana mai son bayarda labari! Kaji tsoron Allah, kada kafadi, ko kada karubuta sai abin da kaji ko kagani kokuma kake da tabbas akansa. kasani za ka amsa tamyar Allah akan abinda kake fadi kokuma kake rubutawa a duniya (facebook), wacce amsa ka tanada?

Ba wani abin birgewa bane afara jin labarin dake tayar da hankali agurinka. Addinin muslunci ya hore mu da yin magana ba tare da ILIMI ba. Mu kiyaye ko Allah (S.W.A) ya kiyaye mu.

Ya Allah! Kakiyaye mu, kabamu zaman lafiya, Amin.

Haka kuma a Facebook zakaga GROUP ko PAGE wadanda basu da Aiki sai watsa Labarin karya. Misali sai a saka Hoton Yarinyar da bata jiba bata Gani ba wai Ace tace tana neman Miji. Wanda kuma Addinin Musulunci bai yarda da hakan ba.

Kuma 'yan mata kuji tsoron Allah duk abinda ya sameku kuke Janyowa kanku. Domin kune kuke yawan sauya Hoto dan ku Birge mutane!

A garin hakan kuma sai a samu wasu bata gari suyi downloading din hoton su dinga Talla daku.

Ko kuma Namiji ya Bude 2go da sunan mace yasa hoton wadda bata jiba bata gani ba. Wai dan ya yaudari 'yan Iska 'yan'uwansa. Allah ya kiyaye mu.

To Jama'a sai mu kula da fadar jita jita, domin karya haramun ce. Allah ya kare mu amin....

Friday, March 15, 2013

KUDUBAR JUMA'A DAGA BUBBAN MASALLACIN HADEJIA.

HADEJIA A YAU. A yau malam Na'ibi yi mana kudubace mai taken :- JIN TSORO DAGA AZABAR ALLAH S.W.T. Fassara:- Ibrahim Umar. Yan uwana musulmai Malam ya ja hankalinmune game da jin tsoro daga azabar Allah Mai Girma da Daukaka domin kamun ubangiji ya kasance mai tsananine. Yan uwana kullun mu cigaba da kasancewa daga cikin bayin Allah Madaukaki masu da'a tare da jin tsoron azabarsa. Kada mu kasance daga bayi azzalumai masu zalintar kansu wajen keta Abubuwan da musulunci ya hana. Manzon Allah S.A.W yana cewa "kuji tsoran wuta ko da da tsagin dabino ne" Ma'ana koda abin da zakayi sadaka dashi kamar tsagin dabinone don ka bayar dashi ka kare kanka daga wuta to kayi kokari ka bayar. ALLAHUMMA INNA NARJU RAHMATIKA WA NAKHAFU AZABAK. ya Allah SWT ka karemu daga azabar wuta amin.

Sunday, March 10, 2013

FACEBOOK A KARKARA!

HADEJIA A YAU!Hadejia A yau! Assalamualaikum! 'Yan uwa barkanmu da yau, da fatan Alkairi. muna gaf da fara wani shiri a wannan shafi na facebook. shirin kuwa zai leka ne loko na kauyukan Arewacin Nigeria, domin jin halin da talakawa suke ciki a kauyuka da karkara. domin wasu kauyukanma ba'a kulasu sai an buga gan-gar siyasa. Sanin kowane Talakawa akar-kara suna cikin mawuyacin hali fiye da na biranen Arewacin Nigeriya. Ada sashin hausa na gidan redion b.b.c. yana gudanar da wannan shiri wanda kuma yin hakan na sanya gwamnati ta gyara kura-kuranta. To amma yanzu shiru muke ji ba labari. Hakan yasanya mu yin azama wajen gabatar da wannan shiri ta hanyar fcbk. kasancewar shugabanni na amfani da shafin na fcbk. Duk da ma dai sunsan halinda ake ciki to amma fadawa duniya zai kara sanyasu su gyara. Kaima kema zaku iya shiga wannan shiri ayi da ku domin yin hakan jihadi ne bubba wanda Allah ne kadai yasan ladan da zaka samu. Domin ka yi sanadiyyar fitar miliyoyin alumma daga cikin Kangin talauci. Duk mai bukatar ayi wannan aiki da shi ya Tuntubi Garba Tela Hadejia ta inbox. Ko ya kira lambarsa ko ya masa sakon Wasika (text). 07065540705. Allah ya bada Iko.

Wednesday, March 6, 2013

HUKUNCIN GADO DA MASU CIN GADO. KASHI NA DAYA (1)

HADEJIA A YAU! Assalamu Alaikum! Wannan babi zai yi bayani a kan masu gado a cikin maza, da masu gado a cikin mata. Sannan babin zai yi bayani akan irin bambancin darajojin magada. (1) MASU GADO A CIKIN MAZA Masu gado daga cikin maza, su goma (10) ne! Ga jimlarsu, amma idan aka rarraba su, su goma sha biyar ne, (15) kamar haka:- 1. Da (Na tsatso) 2. Dan da, (Jika har zuwa tattaba kunnansa) 3. Uba (Na ciki) 4. Kaka namiji (Na wajan uba, har zuwa Sama) 5. Dan'uwa shakiki (Na uwa daya, uba daya) 6. Dan'uwa li'abi (Na uba daya, uwa daban) 7. Dan'uwa li'ummi (Na uwa daya, uba daban) 8. Dan dan'uwa shakiki (Na uwa daya, uba daya) 9. Dan dan'uwa li'abi (Na uba daya, uwa Daban) 10. Kanin uba, shakiki (Na uwa daya, uba daya) 11. Kanin uba li'abi (Na uba daya, uwa daban) 12. Dan dan kanin uba, shakiki (Na uwa daya uba daya) 13. Dan dan kanen uba, li'abi (Na uba daya uwa daban) 14. Miji. 15. Ubangijin bawa. Hadejia A yau! MASU GADO A CIKIN MATA Masu gado a cikin mata su bakwai ne (7) Ga jimlarsu, amma idan aka rarraba su, su goma ne, (10) kamar haka:- 1. 'Ya ko Diya (Ta tsatso) 2. 'Yar da, (Na tsatso duk yadda ya yi nisa) 3. Uwa 4. Kaka mace (Ta wajan uba) 5. Kaka mace (Ta wajan uwa) 6. 'Yar'uwa shakikiya (Ta uwa daya, uba daya) 7. 'Yar'uwa, li'abiya (Ta uba daya, uwa daban) 8. 'Yar'uwa, li'ummiya (Ta uwa daya, uba daban) 9. Matar Aure 10. Uwargijiyar bawa ko baiwa. Hadejia A yau! MASU GADO DARAJARSU TANA DA BAMBANCI DA JUNA Masu gado suna da bambanci da junansu. Ma'ana gado ba abu ba ne wanda za a ce a raba shi daidai, a tsakanin magada. Dole ne a raba shi yadda Allah Madaukakin Sarki Ya raba shi cikin hikimarSa. A rabon gado wani ya fi wani rabo. Wani kuma ba ya da rabo in ga wani. Wani kuwa zai tashi daga wani rabo ya koma ga wani rabo, saboda samun wani tare da shi. Wani kuma zai kada wani; wani sauran dukiya yake kwashewa. Saboda haka za mu bi su dalla-dalla, domin mu yi bayaninsu, in sha Allahu. MASU FARALI Za mu fa ra da bayanin abin da ake nufi da masu farali. Masu farali su ne wadanda Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci rabonsu a cikin Alkur'ani Mai girma. wadannan su ne kamar haka: 1. 'Ya (Ta tsatso) 2. 'Yar da (Na tsatso) 3. Uwa 4. Uwar uwa 5. Uwar uba 6. Dan'uwa li'ummi (Na uwa daya) 7. 'Yar'uwa li'ummiya, (Ta uwa daya) 8. Miji. 9. Mata. MASU ASIBCI Za mu fara bayani a kan abin da ake nufi da asibi. Asibi shi ne wanda idan a ka zo wajan rabon gado, zai tsaya har a fitar wa masu farali, farilinsu, sannan abin da ya yi saura ya kwashe, za mu jera su kamar haka: 1. Da (Na tsatso) 2. Dan da (Na tsatso) 3. Dan'uwa shakiki, (Uwa daya uba daya) 4. Dan'uwa li'abi, (Na uba daya) 5. Dan dan dan'uwa shakiki (Uwa daya uba daya) 6. Dan dan dan'uwa li'abi, (Na wajan uba) 7. Kanin uba shakiki (Uwa daya uba daya) 8. Kanin uba li'abi, (Uba daya uwa daban) 9. Dan kanin uba shakiki, (Uwa daya uba daya) 10. Dan kanin uba li'abi, (Uba daya uwa daban) 11. Wanda ya 'yanta bawansa. 12. Wadda ta 'yanta bawanta. MASU ASIBCI WANI LOKACI WANI LOKACI SU KARBI FARALI Wadanda ke yin asibci wani lokaci, wani lokaci kuma su amshi farali, su ne kamar haka: 1. 'Yar'uwa shakikiya (Uwa daya uba daya) 2. 'Yar'uwa li'abiya (Uba daya uwa daban-daban) MASU ASIBCI WANI LOKACI WANI LOKACI SU KARBI FARALI WANI LOKACI SU HADA DUK Wadanda ke yin asibci wani lokaci, wani lokaci kuma su amshi farali, wani lokacin kuma duka gaba daya, da asibci da farali. Sune:- 1. Uba. 2. Kaka namiji. MASU GADON NISFI Kafin mu yi bayanin masu gadon nisfi, ya kamata mu san mene ne nisfi? Nisfi kalmace ta Larabci. Ma'anarta rabi (1/2). Idan an raba wani abu biyu, kowane daya daga cikinsu ya zama nisifi ke nan. Masu gadon nisfi (Rabi), su biyar ne kamar haka: 1. Miji. 2. 'Ya (Ta tsatso) 3. 'Yar da (Na tsatso) 4. 'Yar'uwa (Ta uwa daya, uba daya) 5. 'Yar'uwa (Ta uba daya, uwa daban) Wadannan su ne masu nisifi. Za mu bisu daya bayan daya; mu yi bayanin su dalla- dalla, ta hanyar da za a fahimta, in sha Allahu, domin ko wanensu yana da sharuda. Alhamdulillahi.

Tuesday, March 5, 2013

WA YA KAMATA YA TSAYA A BAYAN LIMAN?

Hadejia A yau! Assalamu Alaikum! Godiya ta tabbata Ga Allah wanda ya Halicci Mutum da Aljannu dan mu bauta masa.

Tsira da Aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu, wanda Allah ya Aikoshi da Alqur'ani da Salloli guda Biyar (5).

Bayan haka Al-ummar Musulmi Musulunci yana da tsare tsare wanda Idan ka bisu zaka rabauta! Hakika Tsayuwa a bayan Liman a yayinda ake sallah ba na kowa bane na Masana ne! Domin Idan Liman yayi kuskure a sallah sune suka san Irin abinda zasu fada masa dan ya gyara.

Idan wanda baida Ilmi ya tsaya bayan Liman kuma aka samu akasi Liman yayi Kuskure kana tunanin zai iya gyara masa? Bazai iya ba, saidai ya sake batawa.

Manzo (s.a.w.) yana cewa :- An sanya muku Liman dan kuyi koyi dashi, Idan yayi Ruku'i kuyi Ruku'i, Idan yayi Sujudi kuyi sujudi.

Danme zakayi abinda Liman baiyi ba?

ZAN BAKU LABARIN MUJRIMI... Mujrimi wani Balaraben Kauye ne! Yazo Birni kuma Sallah ta Magriba ta kamashi sai yazo yayi Alwala ya tsaya a bayan Liman. Sai akayi Sa'a Liman ya karanto Ayar nan da take cewa:-

Alam Nukhliqil Awwalyn? (Fassara) shin bakuga yadda muka Halakarda Mutanen farko ba? Sai Balaraben kauye ya fice daga sahun farko ya koma sahu na biyu.

Sai Liman ya sake karanta Summa Nutbi'uhumul-Akhiriyn. (fassara) sannan haka muka aikata ga mutanen baya. Sai Balaraben kauye ya koma sahun Karshe.

Sai Liman ya kara karanta Kazalika Naf'alu bil- Mujrimiyn. (fassara) sannan haka Muka aikata ga Mujrimai.

Sai Balaraben kauye ya fita a guje yace Ni ake Nema. Domin yaji an ambaci kamar sunansa. To dan Allah me ya janyo haka? Allah yasa mu Gane.

Monday, February 18, 2013

KASAR HADEJIA DA KEWAYENTA.

Hadejia A yau Muna farawa da sunan Allah Mai kyauta
Magamiya a Duniya, ya baiwa musulmai da
kafirai baki daya! Mai jin kai Kebe Gobe
kiyama. Ni'imarsa ga wanda yayi Imani take
Ranar Alkiyoma. Tsira da Aminci su Tabbata
Ga shugabanmu Annabi Muhammadu (s.a.w.)
wanda Allah ya aikoshi da shiriya ga
Mummunai.

Kasar Hadejia kasa ce wadda Allah Ya
Albarkaceta da Ni'imomi daban daban kamar
Kasar Noman Rani da Damina, Kiywo, da
sauran Albarkatun cikin Ruwa da na Kan
Tudu. Kuma kasar ta kafu tun a Karni na 17
wasu kuma sunce Karni na 15. Daga Gabas
tayi Iyaka da Daular Kanem Borno daga
yamma tayi Iyaka da Masarautar Kano. Haka
kuma daga Kudu tayi Iyaka Da Wuddiri wato
kasar Katagum. Sannan daga Arewa tayi Iyaka
da Masarautar Gumel da Daular Damagaram.

Kuma Hadejia tana daya daga cikin Hausa
Bakwai dukda cewa Fulani ne Suke Mulkinta.
Hadejia A yau.
Abinda nakeso na fada shine... Cikin Hikimar
Ubangiji da Ikonsa ya bamu Manyan mutane
Masu Kaunar Ci gaban Wannan yanki.


Wadansu 'yan Kasuwa ne wasu kuma
Ma'aikatan Gwamnati, wasu kuma 'yan Siyasa.
Kullum kokarinsu da Tunaninsu shine yaya
zasu samawa Kasar Hadejia Mafita? Yaya zasu
kawowa yankinsu ci Gaba? Yaya zasu rage
zaman banza ga Matasa? Yaya zasu Hada kan
Al'ummar Kasar Hadejia su kalli Alkibla Guda?

Allah ya saka musu da Alkairi.
Saboda haka ne wasu daga Cikinsu suka fara
Gina Masana'antu da kamfanoni domin
samarwa da Matasa aikin yi. Zamu fara da
Kamfanin shinkafa wanda ana nan Ana aiki
ba dare ba Rana. Sannan kamfanin Suga
wanda shima ana kan Aikinsa.
Haka nan Masana'antu Gasunan wasu ana
aikinsu wasu kuma tuni suna aiki kamar
Sambajo Gen. Enterprises da sauransu.
Sannan Idan kazo titin Maje Road zakaga
wasu Gine gine masu Hawa biyu (2) suma
anayinsu don kyautata Rayuwar Al'ummarmu.

Muna Addu'ah Ga 'yan kasuwarmu da
Ma'aikatan Gwamnatinmu da 'yan siyasarmu
Allah ya saka musu da Alkairi. Allah ya karfafi
zuciyarsu. Amin.

(1) A.V.M. Hamza Abdullahi
(2) Alh. Salisu Sambajo
(3) Alh. Hashim Ubali Yusuf
(4) Alh. Lawal A.A.
(5) Alh. Muhd. Daguro Adamu
(6) Comrade Umar Danjani
(7) Danmasanin Hadejia Alh. Dr. Muhd. Lawwal
(8) Magayakin Hadejia Alh. Muhd. Umar
(9) Professor Haruna Wakili
(10) Alh. Sarki Kafinta Mallam Madori.
Hadejia A yau.

Wednesday, February 6, 2013

SANA'AR WASAN KURA DA BIRI

Easily Upload Your Images To Myspace
As.HADEJIA A YAU!
Sana'ar wasa da kura wata sana'a ce wadda ta samo asali tun lokacin Maguzawa, har ta kawo ga wannan karni da muke ciki. Inda zakaga mai wasa da kurar ya sanya mata camfu a bakinta kuma yana rike da ita da sasari.

Yakanyi ta mata kirari yana zungurarta ita kuma kurar tana kugi duk don a birge masu kallo. Sannan masu wannan sana'a suna tafiya da abu biyu, wato bayan wasa da kurar suna saida magani musamman wanda ya shafi yara.
Zakaga ana kaiwa yara ana dorasu a kan kurar wai don karsuyi tsoro. Wasu kuma ana dorasu ne domin maganin fitsarin kwance.

To kowane mai wasa da kura zai fada maka dadin sana'ar da kuma wahalarta, to ko menene wahalarta? Wani mai wannan sana'ar ya tabbatar min cewa wahalarta tana da yawa musamman ma wajen yanda zaka samo kurar tun tana karama, kayi kiwonta har ta girma. To ko menene Hatsarinta? Yace hatsarinta yana da yawa Amma Allah bai taba hadasu da hatsarin ba.

Sannan shima wasa da Biri yanzu zakaga masu wasa da kurar sune sukeyi, Kuma ya kara min da cewa suna hada wasan kura da na biri ne domin kawata masu kallo.
Allah ya kyauta.

Tuesday, February 5, 2013

ME YA HADA ALMAJIRCI DA BARA?

Image Hosted by ImageTitan.com
Hadejia A yau. Ko da kaga wadannan yara kasan su waye? Wadannan su ake cewa Almajirai, ko menene Ma'anar Kalmar Almajiri? Kokuma waye Almajiri?

Almajiri ana nufin Dalibi mai neman karatun Alqur'ani kokuma Ilmin Addinin Musulunci. Domin ya zama malami mai karantarwa! Malamai sune ake yiwa take da :- Masu tsantsanin Duniya saboda kiyamah,
Masu zuyyina Adon Qur'ani.


ALMAJIRI- Idan akace almajiri a kasar Hausa ana nufin mai Neman Ilmin addini.Wadanda idan sukaji Labarin malami a duk Inda yake zasu tashi suje domin neman Ilmi.
Haka kuma Iyaye suma sukan kai 'ya'yansu domin su samu Haddar Alqur'ani ko makamancin hakan.

To a yanzu labarin ya sanja domin Iyaye suna kaiwa 'ya'yansu Almajirci ne don bazasu iya ci dasu ba, zakaga yaro baifi shekara biyar ba (5) an kawoshi wai Almajirci. Anya yaron nan ba gamuwa yayi da ragon Uba ba? Babu ruwansu da'ya'yansu sai damina ta fadi zasu debosusu tayasu Noma.

Zakaga Almajiri ya sato karfunan bakanikai ya kaiwa Makera su saya, Almajiri ya sato gwangwanaye ya kai Jaribola, Almajiri yanzu har kasuwar tsaye! Sun gamu da ragagen Iyaye su dama baburinsu karatu ba, sudai suga babu waninauyi a gabansu.


Allah ya kyauta. Dukda wasu zasuce Ai da sokoto ma kiskadi ce Amma babu wanda ya baka tarihin In sun tashi daga karatu bara suke zuwa. Muma Nan Mai-rakumi ai kiskadi ce da sauran garuruwa.

Amma bamuji cewa suna zuwa bara ba.

Tuesday, January 15, 2013

TARIHIN RAYUWAR SIR. AHMADU BELLO (SARDAUNA) 15/01/2013.

Easily Upload Your Images To Myspace
Hadejia a yauAn haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan
Sokoto, a ranar 12 ga watan Yuni na 1910 a
garin Rabbar na jihar Sokoto dake Arewacin
Najeriya.
Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda
na daya daga cikin wadanda suka kafa
daular Sokoto, kuma dane ga marigayi
Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.


Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin
Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar
horas da malamai ta Katsina.
Kafin daga bisani Sultan ya nada shi malami
a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan
Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da yayi
na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi.
Ya kuma halarci kasar Ingila domin yin
karantu kan harkokin mulki a shekarar
1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-
gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda
har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar
dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama
ministan ayyuka da raya kasa.
Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa
daga shekarar 1954 zuwa 1966.
Sannan ya jagoranci jam'iyyar NPC ta lashe
kujeru da dama a zaben da aka gudanar
bayan samun 'yancin kai.
Bayan kammala zabe, ya zabi ya ci gaba da
kasancewa Firimiya, inda ya nada Abubakar
Tafawa Balewa ya zamo Fira Minista.

Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin
Arewacin kasar wanda keda kabilu mabiya
addini daban-daban, da kuma aiwatar da
ayyuka na ci gaban kasa.


An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan
Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin
mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo suka
jagoranta.