Monday, July 9, 2012

TARIHIN KAFUWAR HADEJIA KASHI NA (1)


HADEJIA- TARIHIN KAFUWAR Hadejia Ya
farune daga wani maharbi mai suna Hade, a
yawon farauta da yakeyi ne wata rana yana
tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo ko da
tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi
mamakin hakan har ma sai yabi sawunta.
Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye
suna shawagi a gurin. Sai ya yanke
shawarar zama a wannan gurin, kuma
hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa
yake harbe harben Namun daji kuma yayi su
wato kamun kifi. In ya kashe namun daji sai
yaje ya sayar da fatun. Harma ya dauko
Matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan
gurin. Kuma mutane sai suke zuwa sayen
fatu da nama a wajensa. Duk wanda yazo
gurin sai yayi sha'awar zama a gun, haka
nan gari ya fara bunkasa wasu maharba,
wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai
gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada
zango a garin. To kasancewar gari sai da
shugabanci ne yasa shi Hade ya zama
shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu
ko nama sai yace na tafi garin Haden jia.
Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. To
sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe
sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia.
Kuma bayan zamanin wannan mutumin
Hadejia taci gaba da zama gari kuma tare da
shugabanci wato mulkin Habawa. Kuma a
lokacin akwai kananan Garuruwa masu cin
gashin kansu kamar Rinde, yayari, wunti,
Anku da dai sauransu. Wadanda suma suna
da nasu sarakunan a wannan Lokacin.
Amma yanzu duk unguwanni ne a cikin
garin Hadejia. Kuma Hadejia sunyi
sarakunan Habe guda talatin da biyu(32)
amma sunan mutum uku ake dasu wadanda
sukayi mulki kafin zuwan Fulani. 1, BAUDE 2,
MUSA 3, ABUBAKAR. Kuma a lokacin
Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma
shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin
Hadejia tana karkashin Daular Borno, kuma
ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin
Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman
dan fodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune
suke sarautar Kasar Hadejia.
A GABA ZAN KAWO MUKU TARIHIN
SARAKUNAN FULANI DA DALILIN KARBAR
TUTA DA YADDA SUKA TUNKUDE SARAKUNAN
HABE DAGA SARAUTA.

No comments:

Post a Comment