Tuesday, July 17, 2012

KASAR HADEJIA DA KABILUN CIKINTA


HADEJIA A YAU! Kasar Hadejia tana da kabilu da dama wadanda kuma suke da yarensu daban-daban: kamar 1,HAUSAWA 2, ABORAWA (FULANI) 3, MANGAWA 4, GIZMAWA 5, BADAWA 6, KOYAMAWA.
1, HAUSAWA:- Kabilar Hausawa sune kabila mafiya yawa a kasar Hadejia Domin su babu wanda zaice ga lokacinda suka shigo Kasar Hadejia. kuma tafi karfi a kasar sakamakon dadewar Garuruwansu. kamar Garun Gabas (Biram), Auyo, da Matsa. kuma ko zuwan Bayajidda Garun Gabas yazo ne ya samu Mutanen Garin suna yin Hausanci.

2, ABORAWA (Fulani):- Kabilar fulani sun shigo kasar Hadejia tun a Farkon karni na goma sha biyar (15) kuma sun shigo ne daga yankin Machina wasu kuma daga Katsina, kuma sun Taho ne daga Gabar Kogin SENEGAMBIA wato SENEGAL.sun fara zama ne a Rinde wasu kuma sun Zauna a Jarmari wasu a Marke wasu a Adiyani da Margadu. Kuma ayarinsu ya kasu biyu Inda wasu suka wuce kasar Kano Karkashin Jagorancin Lamido Usman Kalinwama. A Karni na goma sha Tara (19) Wasu fulanin sun sake shigo Kasar Hadejia daga yankin Machina Karkashin Jagorancin Ardo Abdure Dan Jamdoyi. Kuma ance Kafin suzo Hadejia saida suka zauna a Kankiya ta Jihar Katsina. kuma wadannan fulani suke Sarautar Hadejia har zuwa Yau.
3, MANGAWA:- Kabilar Mangawa ko Barebari wadanda mafi yawancinsu suna zaune a Gabas da Hadejia da kuma Arewacin kasar Sun zo ne A karni na goma sha bakwai (17) sun taho ne daga yankin Borno kuma mafiya yawansu sun zo kasar Hadejia ne Tonon Azurfa da Tagullah. Inda kuma daga baya wasu sun shigo kasar Hadejia A lokacinda RaBe yaci Kukawa da Yaki sai suka kaura suka dawo kasar Hadejia, Kamar Birniwa,Baramusa,Kacallari, da Sauransu.
4, GIZMAWA:- Gizmawa suma kamar Mangawa sun shigo ne a Karni na goma sha bakwai (17) kuma suma suna zaune ne a yankin Guri, Marma, Lafiya da sauransu kuma suma yarensu kusan kamar barbarci ne saidai wasu kalmomin da yake canzawa.
5, BADAWA:- Kabilar Badawa basu da yawa a kasar Hadejia, kuma suna zaune ne a Garuruwan Iyakar Hadejia da Bedde, Kamar Gayin, Adiyani, Margadu,da Kadira. wasu sun zauna anan ne tun kafin yakin Gogaram. wasu kuma sunce dama anan suke tuntuni. ganin cewa suna iyaka ne da Kasar Bedde.
6; KOYAMAWA:- Kabilar koyamawa suma basu da yawa kuma Dangin Barebari ne, sai dai zanensu ya bambanta. kuma yarensu ma ba iri daya bane. Kuma suna cewa sun taho ne daga Gabas da Sudan. sannan suna zaune ne a Kasar Kafin Hausa,Bulangu,Yayari, koyamari da sauran garuruwan kasar Kafin hausa.

7; TIJJANAI:- Kabilar Tijjanai fulani ne dake zaune a Yelleman kuma Malamai ne masu bin Darikar Tijjaniyya. shi yasa ake ce musu Tijjanai. Sun shigo kasar Hadejia a shekarar 1903, Daga Malo a yankin Tukolar Senegal. sun taho ne bayan Turawan France sun yiwa Yankinsu Mulkin Mallaka. sun taho karkashin jagorancin Shugabansu Muhammadu El-Bashir, kuma sun fara zama ne a Lokoja. Magajinsa kuma Ahmadu Madaniyyo sai ya sake tasowa daga Lokoja yazo Kasar Hadejia aka basu Guri suka zauna. wato Yelleman Tijjanai. Alhamdu lillahi. Hadejia A Yau.

Sunday, July 15, 2012

TARIHIN ALH. DANJANI HADEJIA


HADEJIA A YAU! Tun Lokacinda nace zan rubuta tarihin Alh. Danjani Hadejia na samu kiraye kiraye a waya akan cewa ana sauraro na. To matsalar itace muna nan muna tattara Bayanai domin kar muyi garaje bamu kammala ba mu saki. Mai Karatu zaiga na rubuta Tarihin Alh. Danjani Hadejia, Wannan satin in Allah ya yarda zamu Maida Hankali wajen Tarihin Alh. Danjani Hadejia. Da irin gwagwarmaya da yayi. Alh. Danjani yana daya daga cikin Mutanen da suka Daga darajar masarautar Hadejia idan mukayi la'akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ganin Talaka yayi kyakkyawar rayuwa babu Tsangwama daga masu sarauta. Abinda yasa bazamu Rubuta duk tarihin ba sai mun samu Hotonsa wanda yayi da farar riga da bakin takalmi da kuma Jar hula. Hadejia a yau.

Monday, July 9, 2012

TARIHIN KAFUWAR HADEJIA KASHI NA (1)


HADEJIA- TARIHIN KAFUWAR Hadejia Ya
farune daga wani maharbi mai suna Hade, a
yawon farauta da yakeyi ne wata rana yana
tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo ko da
tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi
mamakin hakan har ma sai yabi sawunta.
Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye
suna shawagi a gurin. Sai ya yanke
shawarar zama a wannan gurin, kuma
hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa
yake harbe harben Namun daji kuma yayi su
wato kamun kifi. In ya kashe namun daji sai
yaje ya sayar da fatun. Harma ya dauko
Matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan
gurin. Kuma mutane sai suke zuwa sayen
fatu da nama a wajensa. Duk wanda yazo
gurin sai yayi sha'awar zama a gun, haka
nan gari ya fara bunkasa wasu maharba,
wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai
gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada
zango a garin. To kasancewar gari sai da
shugabanci ne yasa shi Hade ya zama
shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu
ko nama sai yace na tafi garin Haden jia.
Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. To
sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe
sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia.
Kuma bayan zamanin wannan mutumin
Hadejia taci gaba da zama gari kuma tare da
shugabanci wato mulkin Habawa. Kuma a
lokacin akwai kananan Garuruwa masu cin
gashin kansu kamar Rinde, yayari, wunti,
Anku da dai sauransu. Wadanda suma suna
da nasu sarakunan a wannan Lokacin.
Amma yanzu duk unguwanni ne a cikin
garin Hadejia. Kuma Hadejia sunyi
sarakunan Habe guda talatin da biyu(32)
amma sunan mutum uku ake dasu wadanda
sukayi mulki kafin zuwan Fulani. 1, BAUDE 2,
MUSA 3, ABUBAKAR. Kuma a lokacin
Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma
shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin
Hadejia tana karkashin Daular Borno, kuma
ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin
Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman
dan fodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune
suke sarautar Kasar Hadejia.
A GABA ZAN KAWO MUKU TARIHIN
SARAKUNAN FULANI DA DALILIN KARBAR
TUTA DA YADDA SUKA TUNKUDE SARAKUNAN
HABE DAGA SARAUTA.

THE ORIGIN OF FULANI (Asalin Fulani)


Who Are the Fulani People? Origins The
history of the Fulani seems to begin with the
Berber people of North Africa around the
8th or 11th century AD. As the Berbers
migrated down from North Africa and
mixed with the peoples in the Senegal
region of West Africa the Fulani people came
into existence. Over a thousand year period
from AD 900 - 1900, they spread out over
most of West Africa and even into some
areas of Central Africa. Some groups of
Fulani have been found as far as the
western borders of Ethiopia. As they
migrated eastward they came into contact
with different African tribes. As they
encountered these other peoples, they
conquered the less powerful tribes. Along
the way many Fulani completely or partially
abandoned their traditional nomadic life in
favor of a sedentary existence in towns or
on farms among the conquered peoples.
The nomadic Fulani continued eastward in
search of the best grazing land for their
cattle. Their lives revolved around and were
dedicated to their herds. The more cattle a
man owned, the more respect he was given.
Today, some estimate as many as 18 million
Fulani people stretch across the countries of
West Africa. They remain to be the largest
group of nomadic people in the world. What
Do the Fulani Believe? Religion and Beliefs:
The Fulani were one of the first African
tribes to convert to Islam and are today
more than 99% Muslim. The devoutly Muslim
Fulani have seen themselves as the
propagators and preservers of the Islamic
faith in West Africa from as early as the
fourteenth century. Historically it was a
Fulani chief named Usuman dan Fodio,
along with nomadic Fulani herdsmen who
were instrumental in facilitating the spread
of Islam across West Africa through
evangelism and conquest. At times they
would wage "holy wars" or jihad in order to
extend and purify Islam. As the Fulani
migrated eastward they spread their Islamic
beliefs. As they became more powerful and
attained more wealth they began to be
more aggressive with their religion. Their
adoption of Islam increased their feeling of
cultural and religious superiority to
surrounding peoples, and that adoption
became a major ethnic boundary marker.
Some settled in towns and quickly became
noted as outstanding Islamic clerics, joining
the highest ranking Berbers and Arabs.

Sunday, July 8, 2012

WAKAR SAUDATU ADO BAYERO



1, Daren jiya ba na yau bane gun kwanan
yaro daban da bubba.



2, Bismillah zana shirya waka sarki Allah
kaban basira inyi wakar saude 'yar nikatau.



3, Ina dada godiya ga Allah sarkinda ya halicci saude.



4, Ga saude sarauniyar kano mai saukin kayi da son mutane.



5,Ga mai fara'a da son mutane Bata gaji tsiya da tsangwama ba.


6, A wajen kyauta fa ba kamar saude 'yar
sarkin kano na korau.



7,Ga mai haske kamar Azurfa Dadin suna kamar Tagullah.


8,Taurari ko suna da haske basu kai hasken farin wata ba.



6, Inda mata suna sarauta a kano mukan
muna da saude.



7, A zaria sunyi Quen Amina muma a kano muna da saude.



8, A gabas na dangana da Borno ba
kyakkyawa kamarki saude.



9, A yamma najeni har Ilorin ni banga ba
wadda tayi saude.



10, ta nan kudu har zuwa Adamawa banga ba wadda tayi saude.



11, A arewa saida na wuce Nijar banga ba
wadda tayi saude.



12, Kai duk matan dake cikin facebook babu wadda tayi saude.



14, Hotonki ana comment akanshi na kirga Comment dubu a yanzu.



15, Ga allurar cikin duhu sai mai zurfin
hankali ka tsinta.



16, Ga saude bakin zare a matoya sai mai
hankali ka tsinta.



17, Ni burina a duniya inga kina mulkin
kano sa'ade.



18, Allah ba yanda bai iya ba a zazzau shi ya bai Amina.



19, Ansa giwa cikin zubo taci guda bakin
rabonta kelau.




20, Allah in yai nufi ga iko nai babu abinda
zai hana shi.

Friday, July 6, 2012

THE ESTABLISHMENT OF SOME OF THE OLD SETTLEMENTS IN HADEJIA EMIRATE


HADEJIA A YAU!
We are severely constrained in the producing a coherent, meaningful and definite pattern of the process of the evolution of Hadejia emirate due to the limitation by our main source-oral tradition. Most of the traditions collected hardly touch on the process of the evolution of Kasar Hadejia. But in spite of this difficulty, we intend to take a second look at the source through a new-interpretation in the hope of coming out with a better understanding of the process of the evolution of Hadejia emirate. Towards this end, we shall attempt to discuss the process of the evolution of certain Old settlement in the emirate, with a view to paving way towards grasping the process of the evolution of Kasar Hadejia as whole.

Prior to the jihadist conquest at the beginning of the 19th century, the territory now known as Hadejia emirate consisted of several separate and distinct Kingdoms whose rulers received titles from and owed allegiance to the Habe Galadima of Borno.

The former Habe Kingdoms included Auyo,Garin Gabas(Biram),Hadejia,Kazura,Gaturwa,Marma,Dawa and Fagi. The process of the evolution of these Kingdoms of seems to be obscure except perhaps for the Kingdoms of Hadejia,Auyo and Garin Gabas.

At the time of the foundation of Hadejia,a number of small settlements were said to have existed in the territory that came to be known as Hadejia emirate. For example,on the North-eastern side of Hadejia town, there was Madagwaigwai, whose present site is near Rubban Dakata a village about 10kilometres east of Hadejia Kiri kasamma road. While on the eastern side of the town was Maskangayu (kulunfardu), a village said to have been established by Damagarawa immigrants whose ancestors now live in Hadejia (ILALLAH).

The old site of Kulunfardu was located near Tandanu, just by the valley of River Hadejia, about 15kilometres from TURABU.
There was a tradition in Turabu which said that, at the side of kulunfardu, there was a large Tamarind (Tsamiyar linzamai) whose branches were said to have bent due to the weight of the Luggage of soldiers of Mai Ali of Borno when they camped there on their way to attack Kano during the reign of Sarkin Kano Muhammadu Kambari Dan shariff(1731-1734) By the western side of Hade's camp was KADIME (still located to the site) which was about 9kilometre from Hadejia. By the Northern side of Hadejia was Majeri a few kilometre from Mallam madori, and by the southern side were Auyakayi(Tunawa), Unik(Arki), Majawa and Auyo.

These settlement were clearly established in the surrounding areas much earlier than Hadejia town.
End of page One.
A short History of Hadejia 1800-1906. By Musa Usman Mustapha.
Ana saida shi a k.liman.

Thursday, July 5, 2012

SARKIN HADEJIA BUHARI DA WAZIRIN SOKOTO A KATAGUM


HADEJIA A YAU! Wannan Bindigar Sarkin Hadejia Buhari ce. A lokacinda Sarkin Musulmi Aliyu Bubba ya turo Wazirin Sokoto Abdulkadir Gidado Gurin Sarkin Hadejia Buhari, Wazirin Sokoto shine wakilin sarkin Musulmi a yankin Gabas sai ya taho Hadejia daga Kano Amma sai ya wuce Katagum, Ya turo Jakada zuwa Hadejia yana So su Gana da Sarki Buhari. Buhari yayi tunanin ya tafi shi kadai daga baya sai ya canza shawara kawai ya Tafi Katagum Da Mutanensa. zasu gamu da Wazirin Sokoto a can. Lokacinda suka isa Katagum Sarkin Hadejia Buhari ya tsaya a Kofar Garin Katagum sai ya tura a fadawa Waziri Ya Iso Wazirin Sokoto da Sarkin Katagum suka zo sai sukace Buhari ya Biyosu amma shi kadai tunda Shawara zasuyi. Sarki Buhari ya bisu Har ya shiga Kofar Garin Katagum. Sai Mawakinsa wato DAN FATIMA ya fara masa waka yana cewa:-

1, Abubakar Garba Mijin Maza,

2, Buhari kai ke da Nutso Kai ke da Hankali.

3, Don Allah yayi ka Uban Jama'a

4, Kuma kai Allah ya baiwa shugabancin Gidan Sambo

5, Ba dan na isa ba, In ka yarda ga Aike ka shiga dashi

6, Fasa Maza Gagara gasa Aiken shine

7, In ka sauka lafiya ka gaida Na Lara Sarkin Auyo

8, Ka gaida Bello Sarkin Dutse

9, Na Sambo sai ka dawo.

Abinda Dan fatima yake Nufi Sarkin Auyo da Sarkin Dutse duk Buhari ya kashe su. Dan haka shima In ya shiga Katagum Lalle Bazai fito ba. KodaSarki Buhari yaji Wannan Waka ta Dan fatima sai ya juyo da baya, Wazirin sokoto da Sarkin Katagum da suka fahimci Buhari ya juya sai suka Biyoshi da Ihu Su da mutanen Katagum Suna ce masa Kafiri yaki bin Umarnin Sarkin Musulmi. sai da suka biyoshi har Unik Iyakar Hadejia Da Katagum. kuma sun kashe wasu daga mutanen Buhari. koda yazo Unik sai ya yanke Shawarar ya yi sansani a nan ya koma ya yaki Katagum. kuma mutanensa suka koma suka Karkashe Mutanen Katagum karkashin jagorancin Barde Risku. Daga nan Rashin Jituwa Tsakanin Hadejia da Katagum ya Fara har bayan shekara Goma sha biyu bayan Mutuwar Buhari. ((1863). daga nan Aka samu wasa tsakanin Hadejia da Katagum. koda Katagumawa suka juya sai Wazirin Sokoto ya sake Gyyato Mutanen kano suka Hadu da Na Katagum zasuzo su yaki Buhari. da sarki Buhari yaji wannan Labarin sai shi da mutanensa suka bar Hadejia suka tafi Shabawa Iyakar Hadejia da Gumel Sukayi sansani a can. da Buhari ya bar Hadejia sai Wazirin sokoto ya nada Wansa Ahmadu Sarkin Hadejia. A shekarar (1850).Wanda dama saboda shi suka Takurawa Sarki buhari.

SARKIN HADEJIA BUHARI DA WAZIRIN SOKOTO A KATAGUM KASHI NA (2)

Image Hosted by ImageTitan.com HADEJIA A YAU!

A kashi na farko kunji yanda Buhari suka kare da Wazirin sokoto da Mutanen Katagum: da kuma komawar sarki Buhari shabawa wato iyakar Hadejia da Gumel da kuma Damagaram.

YAKIN TAKOKO:- Bayan an Nada Ahmadu a matsayin Sarkin Hadejia, sauran Magoya bayan Buhari sai suma suka bar Hadejia suka koma Shafowa inda Buhari yake suka zauna tare. Sarkin Hadejia Buhari anan ya zauna tsakanin Takoko da Shafowa a Arewacin Hadejia da mutanensa kuma yake tafiyar da wannan yankin. Kuma iyakar Hadejia ce da Damagaram da Machina ta Arewa maso Gabas wato yankin Niger da kuma Borno. Kuma Buhari ya bada Gudun mawa sosai a wannan Yankin wajen Maidasu Musulmi. Inda yayi ta jihadinsa a yankin, kuma a wannan zama da yayi a Shafowa Buhari ya samu kyakkyawar dangantaka da Sarkin Machina da kuma Shehun Borno Umar wanda ya mulki Borno a wannan shekara (1835-1880) wannan dangantaka ta kara baiwa Buhari karfin gwiwa.


A shekarar 1851, Sarkin Musulmi Alu Bubba ya yanke shawarar daukan matakin Karshe akan Buhari, saboda yana tunanin Shehun Borno zaiyi amfani da Buhari ya rusa Daular Sokoto saboda ya zame musu Barazana a Arewa Maso Gabas. A wannan lokacin kuma DanGaladiman Sokoto ya hada Mayaka daga Hadejia,Kano,Katagum,Misau da Jama'are zuwa shafowa.

A wannan lokacin kuma Buhari ya fita kudu da shafowa shi da Sarkin Machina yana garin Takoko shida Jarumansa. A lokacinda Dangaladiman sokoto suka fito su yaki Buhari sai ya zabi Sarkin Jama'are Samboli ya jagoranci yakin, saboda shi ya fisu sanin Yankin. A ranar da zasu yaki buhari kuma a ranar Buhari ya shirya mamaye Garuruwanda suke kudu da Hadejia, sai aka hadu a Garin Takoko. Yayin da aka hadu aka gwabza fada Buhari yaci Galaba a kansu duk suka gudu, Sarkin Hadejia Ahmadu yayi kokarin ya Gudu Kasar Kano amma sai Barde Risku ya bishi ya Kashe shi.

Bayan Yakin Takoko yazo karshe kuma an kashe Sarkin Hadejia Ahmadu Amma ba'a son ran Buhari ba kuma aka masa Sallah aka kaishi Hadejia aka binne shi, sannan sai Buhari ya koma Hadejia yaci gaba da Mulki. Sakamakon wannan yakin, dangantaka ta sake baci tsakanin Hadejia da Sokoto, kuma Sarkin Musulmi yaki yarda da ya nada Buhari Sarkin Hadejia. Sai ya nada Tukur Na yayari, kanin Sarki Ahmadu kuma yace ya zauna a Mashama a Kasar Katagum a Matsayin sarkin Hadejia ya Gaji wansa Ahmadu. Amma Tukur bai yarda ya zama Sarkin Hadejia ba saboda yana tsoron Buhari, sai yaga bazai iya yin haka ba. Kuma saboda Gudun kar Buhari ya kasheshi sai Tukur ya Gudu daga Mashema yayi kaura zuwa Kano Lokacin Sarkin Kano Usman Na1(1846-1855) Sai aka Turashi ya Mulki Yayari a Kasar Birnin Kudu. (Yayarin Tukur) Tukur ya zauna acan Har zuwa lokacinda ya Mutu 1909. Buhari kuma yaci gaba da mulkin Hadejia yana kai hare hare a matsayin Jihadi Har saida yakai Gabasawa,Sankara,Ringim da Kuka kwance A Arewa maso yamma. A Kudu saida ya mamaye Kununu,Takalafiya, Kafin baka, Doma, Ruba, Itas da Kwanda. A Gabas kuwa saida ya Mamaye Babuwari, Kazura, Dawah, Gatare da Margadu. Saida Sarki Buhari ya fadada kasar Hadejia tafi Ko ina fadin Kasa a karni na19.

GAMON KAFUR:-

Tuesday, July 3, 2012

DAJIN DUHUN KARO A HADEJIA.



HADEJIA A YAU! DUHUN KARO:-duhun karo wani Daji ne dake kasar Hadejia ko ince Gabas da Hadejia. Kuma daji ne mai Dimbin tarihi wanda duk wanda yake kasar Hadejia zaice maka haka ya taso yaga wannan Dajin. Kuma yana tafe ne da Ruwa a Gefensa. Kuma wannan dajin ya taso ne tun daga Falgore har ya dangana da komadugu ta Jihar yobe. Duk wanda ya saba bin hanyar kano ta Ringim zai ga wannan dajin musamman kwanar Auyo zuwa Hadin mai dan karofi inda nan ne ya fito bakin titi.
Na shiga wannan Dajin kuma banda kukan tsuntsaye da Namun daji babu abinda kake ji. Nayi tafiyar kilo meter takai biyar a cikin dajin, na gamu da wani Bafulatani mai suna Musa kuma na tambayeshi shekarar sa nawa a wannan dajin? Sai yace shima anan aka haifeshi kuma yanzu shima yana da 'ya'ya wadanda ya haifa anan. Na tambayeshi ko zai bani labarin wannan dajin? Sai yace ya tashi yaga Kuraye suna zuwa suna razana musu shanu, kuma yace akwai Namun daji kamar Gada,Barewa,Bauna da sauransu. Amma tunda aka fara sarewa dajin sai sukayi nisa kuma da 'yan farauta da suka damesu. Yace Amma har yanzu akwai kananan Namun daji kamar Zomo, Guza, kuma wani lokacin ana samun Gada. Tsuntsaye kuwa dukda harbi da ake Har yanzu akwaisu da dama.
Dajin in ka shiga cikinsa baza kasan ana rana ba saboda tsabar Inuwa da take ciki kuma ga Ruwa a gefensa. Akasarin bishiyoyin da ke dajin farar kaya ce da kuma Bishiyoyi kamar su Danya,Darbejiya,Kirya,Kanya,Magarya, da sauran bishiyoyi masu Ni'ima.
Kalu balenda wannan Daji yake fuskanta shine Sare saren Bishiyoyi da ake yi a cikinsa da kuma fadada Gonakai da makwaftan dajin sukeyi. Ta wani fannin kuma akan samun wasu suna kunna masa wuta. Amma dukda haka in ka shiga zai baka sha'awa. Na tambayi wani dattijo mai suna Garba Tandanu mai shekara 60, yace wannan dajin yasan lokacin da kuraye suke Hanasu zuwa Hadejia ta Rugar Isa inda sai sun zagaya ta Tuwankalta sannan zasuzo Hadejia Amma yanzu sai dai tsuntsaye da kananan namun daji. HADEJIA A YAU.

Sunday, July 1, 2012

KASAR HADEJIA ZAMANIN SARKI ADAMU




HADEJIA A YAU! Hadejia tana daya daga cikin Garuruwan da ke Karkashin Tutar shehu Usman Danfodiyo! Jama'ar Hadejia Akasarinsu fulani ne da Hausawa da Mangawa. Kuma Suna bin Addinin Musulunci ne. Idan muka tabo Tarihin Hadejia tun lokacin mulkin Habe zamuga cewa dama ko a wancan lokacin Addinin Musulunci ne addinin mutanen Hadejia sai dai dan abinda ba'a rasa ba. Kafin a jaddada addinin Musulunci lokacin shehu dan fodiyo sarakunan Habe ne suke Sarautar Hadejia, kuma anyi sarakuna da dama kamar (1)Baude(2)Musa(3)Abubakar. Bayan Malam Sambo ya karbo tuta karkashin jagorancin Sarkin fulani Umaru sai Hadejia ta koma Karkashin mulkin Fulani.
HADEJIA A YAU! A yau Hadejia ta zama wata fuskar kasuwanci a jihar Jigawa, domin duk abinda ka sani na sayarwa zaka samu a wannan gari. A shekaru Hamsin baya In ba ranar Kasuwar Garin ba wani abin bazaka samu ba. Allah ya albarkaci Hadejia da kayan Lambu Irinsu Tumatir, Tattasai, Attaruhu, da sauransu. Wadannan ana yinsu ko wane lokaci a Hadejia ba sai da damana ba. Saboda Albarkar kogi da Allah ya bamu. Haka kuma fannin kayan Abinci kamar shinkafa,Alkama,Masara. Duk ba sai da damina akeyinsu ba a Hadejia. Saboda Albarkar da Allah ya bamu ta kasar Noma mai kyau. Idan muka koma batun Amfanin Abinda ke cikin Ruwa Hadejia A kullum Tana Fidda kifi kimanin Na Naira milyan Biyu a takaice! Wani abu da yake shine Kalu bale a garemu shine.........