Friday, April 13, 2012

TARIHIN MU'AZU HADEJIA! DAGA TURAKAR SHA'IRAI

Tarihin Malam Mu'azu Hadejia, dan
takaitacce ne. Ya rasu yana da Shekara
38, domin acikin 1958 ya rasu. an haifi
Malam Mu'azu Hadeja a garin Hadeja,
cikin 1920. shine Bahaushe na farko da
ya fara rubuta Wakokinsa da rubutun
Boko. Wannan kuwa ya faru ne, saboda
acikin marubuta mawakan Hausa, shine
wanda ya fara samun cikakken illimin
boko. Dangidan Sarautar Hadejia ne,
shine dalilin da wakokinsa suka fi maida
himma wajen yada aqidun NPC a
madadin NEPU. Kila wannanne ya janyo
takaddama tsakaninsa da Malam Mudi
Spikin. Bayan kammala karatunsa ne, ya
fara aikin koyarwa a birnin Kano, har
kuma ya rasu aikin da yake yi kenan.
Nayi ta kokarin in san ko yabar baya,
amma har yanzu ban samu abin
kamawa ba. Na kuma yi kokarin in san
ko yana da iyali a birnin Kano, shima dai
ban samu abin kamawa ba. Sai dai naji
Shata na yiwa Inuwa Mai mai Kirari da
"Baban Mu'azu, wanne Mu'azu? Mu azun
Hadeja. Haji Inuwa Baban Yahaya" Na
kuwa so hakanne don ko zan sami wasu
wakokinsa da ba'a buga ba. Naji ya kan
yiwa kansa kirari da "V T maineman
albarka". Ga dai wata wakarsa, kafinmu
kawo muku wasu.
Bin Allah shine babban bi
Kuma sai kabi wanda ya haife ka
Ka kiyaye hududulLahi suna
nan amru da nahyu suna kanka
Wallahi Uwa da Uba sune
Hanyarka ta neman albarka
In sun gajiya bisa zamani
Sai ka dau wahalarsu da karfinka
Yi fata kadda ka sabe su
Wata rana Allah zai saka
Abinda ka shuka don ka sani
Shine ka tsirowa gonarka
In hairi, hairi zaka gani
In sharri, sharri zai bi ka
Wa adi'ulLahu fadar Allah
Kuma girmama wanda ya girme ka
Duk wanda ya raina fadar Allah
Shi ya bata ya auka halaka
Duk wanda ya raina fadar Allah
Shine muka cewa Dan Iska
Har shina wa kansa kirari, sau
rara kaji taken dan iska
Dan iska sandan Kuka da sun
gumi nai ba;a yin taki
Dusar buntu ba'a ba dabba
To kaji kirarin dan iska
Dan iska naman Balbela
Ba a cin shi da na Hankaka
Kilishin Jaba sai dan iska
Ba mai ci sai ko mai shirka
Kashin Bera baya taki
Balle kayi dokin ga-na-ka
Kiwon Yimka, kiwon banza
Wata ran zai gallabi yayanka
Ajiyar Bera ajiyar wofi
Bari murna sabon dan iska
Ni zan hore ka abokina
Bari jawo dan iska ajika
In har ka yarda ya rabe ka
Ba'alin jama'a sa tsarge ka
Zai koya ma mugun hali
Watakil a kira ka da dan iska
Da 'wa kullu karinin' duba man
Ta'alimi ka samu zancenka
Kuma ka zama Shaidanil insi
Sai hirzi kai da masoyanka
Kuma ka zama Fattani domin
Allah ma bai son ka
Ka girmama Allah da Ma'aiki
Da iyaye duk da sarakinka
Wa ulul amri minkum duba
Ka kiyaye fadar mahaliccinka
In ka rainawa sarakinka
Ka rainawa mahaliccinka
Bari jin kyashin baiwar Allah
Mai kaskantawa da daukaka
Shi yadda ya so haka nan zai yi
Da yayi su sarakai, kai talaka
Da yaso zai baka duniya
Ba komai ce ba ga Rabbaka
In yaso sai kaga ka gajiya
Har ka gaza amfanin kan ka
Kai dai riki aikin alheri
Kowa kaya nasa zai dauka
Shine sarki mai fifiko
Da kasanka, wadansu ko sun fi ka
Wani na da Jaka zambar Goma
Wani bashi Kwabo balle fataka
Wani kullum mota za shi shiga
Wani kullum kaya zai dauka
Da tuwon Baure da gudun kurna
Wainar shinkafa Annafaka
Ga Alkaki duk da Alkubus
Allah ya baiwa wadansu haka
Wani sai shi tsugunna kan titi
In anci a miko mai sadaka
Wani mata nai hudu ne, kuma ga
Soraye, Benaye, Taska
shimfidu, da kujeru, Darduma
ko ina sai kamshi ke binka
Sai fenti zane iri-iri
Ga lantarki, kuma ga fanka
Wani bin Zaure shi kayi domin
Wani kasuwa zai je shi faka
Suturar wani ganye ko walki
Ba rigarma balle shi saka
Shi kance daurin Allah,
Ya daure bawa nai a daka
Wani ga sutura nan iri da iri
Ya jibge wasu cikin adaka
Kullum sai ya sake tsari
Duk wadda yaso ita za shi saka
A gidan wani guda zaka ji don
A gidan wani kuka za'a saka
Kai ba'awa Allah tilas
Shi yadda yaso haka zai baka
Da abin dariya dana mamaki
Ba sa karewa ba shakka
Wai kura ce aka ce ta tu
ba da sata don tsoron halaka
Makiyayi sai amince har
Ya kafa mata turke cikin maruka
Shi mai hakuri shike dafa du
tse ya sha romo mai albarka
Ya Allah taimaki bayinka
Duk wanda yake son manzonka
Mu'azu Hadejia nan ya tsaya
V T mai neman albarka

20 comments:

  1. Heya i am for the first time here. I found this board and I find It truly useful
    & it helped me out much. I hope to give something back and aid others like you helped me.



    My webpage; christianlouboutinoutletshopx.com

    ReplyDelete
  2. I relish, lead to I discovered exactly what I
    was taking a look for. You have ended my 4 day lengthy hunt!
    God Bless you man. Have a great day. Bye

    Feel free to visit my homepage - サングラス オークリー

    ReplyDelete
  3. Yes! Finally someone writes about オークリー ゴーグル レディース.


    Here is my page :: oakley サングラス

    ReplyDelete
  4. スタイルの外に出るこ
    とはないデザインと色で夜
    の靴を選択してください

    my blog post :: ミュウミュウ アウトレット

    ReplyDelete
  5. Thank you for the auspicious writeup. It in fact was a amusement account it.
    Look advanced to far added agreeable from you!
    However, how could we communicate?

    Also visit my weblog :: monster beats

    ReplyDelete
  6. Incredible points. Great arguments. Keep up the great work.


    Take a look at my blog post :: ジョーダン スニーカー

    ReplyDelete
  7. Outstanding story there. What occurred after?
    Good luck!

    My page - monster beats

    ReplyDelete
  8. アイメイクは色が少し眉の中央
    下の領域のみを照
    らすまぶたの表面上のすべてに適
    用されなければならない


    My web site - ミュウミュウ 財布 メンズ

    ReplyDelete
  9. Those were the The air jordan shoes that established it all.
    Where would you appraise the quality of any electronic kit?
    Until recently, girl's golf apparel comprised mainly of boxy polos and ill-fitting shorts. An EKG routine gives a non marking the traction. http://wiki.prepadees.fr/index.php/Utilisateur:CyrusQ86

    ReplyDelete
  10. Between I-J, one can see patterns even with the naked eye.
    Picture used in fashion logos should express the style of a brand.
    Tennis and women's fashion for too long has been deemed an oxymoron. It capabilities a silicone outsole for right behind the knee and durability. http://www.russtroy.infoloadwww.spearheadlrp.co.uk/boards/profile.php?mode=viewprofile&u=267575&sid=27e8c5196bd634b999827cbbe0ed26d7

    ReplyDelete
  11. Companies engage in co-branding to leverage impressive brand.

    This store furnishes its customers on a best price level than other merchants.
    Leon Levin offers them in fat white, we to be honest as, other varying colors.
    Sponsorship can carry with ample selections. http://www.flppp.
    org/user.php?login=louannebu&

    ReplyDelete
  12. Nike has the actual Nike Zoom Advanced, very nice black-jack shoe with all the exact features
    Nike has to present. Focus on a person want to exist when the difference is complete.
    One is inclusions (present within our item),
    blemishes (external). Ralph Lauren, Burberry and Liz Claiborne,
    have added golf lines. http://42.121.236.157/message/index.
    php/dixiefenn

    ReplyDelete
  13. It is however of the an element that determines the way in which valuable it is often.
    Nevertheless a family feud, led these four brothers to divided up,
    and Puma was born. It capabilities a rubber outsole for specific
    tissue traction and speedy legal moves. One is inclusions (present within our
    item), blemishes (external). http://www.gpstuner.com/5.
    4/forum/profile.php?mode=viewprofile&u=35128

    ReplyDelete
  14. Hello there, You have done a great job. I will certainly digg it and personally
    recommend to my friends. I'm sure they will be benefited from this site.

    my web blog ルブタン

    ReplyDelete
  15. Remarkable! Its really amazing post, I have got much clear idea on
    the topic of from this post.

    My site; モンスタービート

    ReplyDelete
  16. Thanks for one's marvelous posting! I definitely enjoyed reading it, you might be a great author.I will make sure to bookmark your blog and may come back from now on. I want to encourage you continue your great work, have a nice weekend!

    My webpage クリスチャンルブタン

    ReplyDelete
  17. Peculiar article, just what I wanted to find.

    Here is my weblog :: http://www.christianlouboutinoutletshop2013.com/

    ReplyDelete
  18. I could not refrain from commenting. Well written!



    Check out my homepage; オークリー サングラス

    ReplyDelete
  19. Its like you read my thoughts! You appear to understand a lot about this, such as you wrote the ebook in it or
    something. I feel that you just can do with a few p.
    c. to pressure the message home a bit, however other than
    that, that is great blog. A fantastic read.
    I will certainly be back.

    my blog post ... クロエバッグ

    ReplyDelete
  20. Among these, the most popular project even now, may be the simple digital recordings player.
    These types of people now come with a wide quantity of colors.
    Cocchia makes the breast coverage low and emphasizes a sporting womanliness.
    The price is the actual staggering $50.00 even more compared to Nike's equivalent, a whopping $249.00. http://kesper.org/wissenswertes/wiki/mediawiki-1.6.7/index.php?title=Benutzer_Diskussion:CindyKirk

    ReplyDelete