Thursday, March 20, 2014

TARIHIN SARAKUNAN FULANIN HADEJIA (Kashi na daya 1)

TARIHIN SARAKUNAN FULANI A HADEJIA...



BISMILLAHIRRAHMANIR'RAHIM.

. Kamar yanda aka sani kasar Hadejia ta koma karkashin mulkin fulani bayan da suka hambarar da mulkin Habawa a karni na goma sha biyar (15). Fulani sun shigo kasar Hadejia ne a farkon karni na goma sha biyar (15), a karkashin jagorancin Ardo Abdure dan Jamdoyji, sun fara zama ne a Jarmari kusa da garin Hadejia, har tsawon wani lokaci. Bayan rasuwar Ardo Abdure a shekarar (1788) sai Dansa Sarkin fulani Umaru ya yanke shawarar su dawo Rinde da zama, yamma da garin Hadejia. kuma Sarkin Hadejia na Habe Abubakar ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia a cikin karni na goma sha takwas (18).

SARKIN FULANI UMARU... Shine sarki na farko a jerin sarakunan fulanin Hadejia, kuma a lokacinsa aka samu labarin jihadin Shehu Usman Danfodiyo. A lokacinda sarkin fulani Umaru yaji labarin jihadin shehu sai yayi shawara da 'yan uwansa da suje suyi Mubaya'a da Da'awar Shehu. Sai ya tashi dan uwansa Sambo yaje ya meka mubaya'arsu ga Shehu da kuma nuna goyon baya ga da'awarsa ta Addinin musulunci.Sambo ya kai chaffarsa ga Shehu a cikin shekarar 1807-1808. A wannan shekara ne jama'a daga garuruwa daban daban sukayi mubaya'a ga shehu, musamman Fulani wadda sune suka taimaka masa wajen jaddada Addinin Musulunci a kasar Hausa.

Bayanda Umaru ya tura Sambo zuwa ga Shehu, sambo ya tafi da  kaninsa Laraima da kuma sauran fulani 'yan uwansa. Shehu ya zabi Sambo da ya zama shine shugaban jaddada jihadi a kasar Hadejia saboda dama Sambo yana daga Dalibansa. Bayan sun dawo Hadejia sukaci gaba da jaddada Addinin Musulunci a ciki da wajen kasar Hadejia.kuma dukda basu samu turjiya da yawa a cikin garin Hadejia ba, Sarkin fulani Umaru da magoya bayansa sun samu turjiya da yawa musamman a yankin Gabas iyakar Hadejia da Nguru da kuma yankin Auyo. Fulanin Hadejia sun fara jaddada jihadinsu ne a Wajen Hadejia, inda suka fara da kauyukan da suke kusa da Rinde kamarsu Akurya da kadime da sauransu


Monday, March 17, 2014

JARMAN HADEJIA ALH. ABBA SAMBO (DAGA NA GABA PART FIVE 5)

TAKAITACCE TARIHIN MAIGIRMA JARMAN HADEJIA ALH. ABBA SAMBO!!

Daga Muhammad Yawale.


An haifi Alh. Abba sambo a shekara ta 1943 a cikin garin hadejia, ya fara karatun allo a matakin karatunsa na farko sannan lokacin ya isa shiga makarantar boko.
Ya fara da hadejia junior elementary school dake dalla wanda a yanzu ake kira
Abdulkadir primary school a shekarar 1953-1957 a garin hadejia.

Bayan ya kammala wannan makarantane ya samu shiga middle school a cikin shekarar 1957-1959, daga nan bayan kammala middle
school ya koma makarantar horan malamai ta wudil/bichi teachers collage a shekarar 1960-1965.

Bayan kammala wannan karatune ya samu zama headmaster a garin gabas primary school a shekara ta 1966-1971, ya koma karin karatu a advance teachers collage zaria a cikin shekara ta 1971-1974 wanda ya samu certificate in education (NCE).

Bayan kamamala (NCE) bai tsaya ba domin samun degree na farko a fannin physical Health Education (PHE) wanda ya kammala a 1975-1978 ABU Zaria.

Yayi hidimar kasa (NYSC) a federal advance teachers collage dutsinma katsina state daga 1978-1979.

Wasu ayyuka da yayi: (1) mataimakin
shugaban wasannin motsa jiki gwamnatin tarayya (NSSF) 1985-1989 (2) wakili a hukumar ilimi mai zurfi ta jami'ar Ahmadu
bello dake zaria 1988-1991 (3) wakilin tantance jarabawar dalibai na kasashen africa 1995. (4) shugaban wasannin motsa
jiki na makarantun jihar jigawa.

Mukaman da ya rike: (1) shugaban
makarantar primary ta garun gabas.(2) jami'i mai kula da shiyar kudu maso yamma wadda take birnin kudu a jihar kano (3) mataimakin
shugaban kwalejin makarantar horarda malamai dake garin hadejia (4) mataimakin jami'in ilimi na shiyoyin kananan hukumomin gezawa, da minjibir a jihar kano
(5) shugaban makarantar sakandiren jeka ka dawo dake kazaure (6) shugaban kwalejin
horar da malamai ta garki. Da sauransu.

Jarman hadejia ya bar aiki ranar 30th ga watan oktoba, 2001 a matakin aiki na 16/17.
Bayan rasuwar marigayi jarman hadejia Alh. Usman sambo na (2) a ranar Asabat 4 ga watan december 2010, maimartaba sarkin
hadejia Alh. Adamu Abubakar maje Con, ya nada ALH. ABBA SAMBO a matsayin JARMAN HADEJIA na (3) kuma Dan majalisar maimartaba sarki.

HADEJIA A YAU....

Thursday, March 6, 2014

DAGA NA GABA HADEJIAWA (Part four 4)

DAGA MUHAMMAD IDRIS

r;">


FARFESA HARUNA WAKILI...............Farfesa Wakili haifaffen kofar fadar Hadejia ne, kuma kamar yadda sunansa ya nuna mahaifinsa shi ne Wakilin kudun Hadejia [Dandalma] wato mai kula da yankin kudancin garin Hadejia.

Farfesa Wakili shi ne Farfesa na biyu a masarautar Hadejia kuma yana daya daga cikin `yan majalissar dattijai na Jami`ar Bayero ta kano kuma babban Alaramma a tsangayar tarihi ta makarantar, harwayau shi ne Mufti akan harkar tarihi a Arewacin kasar nan dominkafafen watsa labarai da dama na ciki da wajen Nijeriya suna dogara da fatawowinsa wajen warware matsalolin tarihi da suka bujuro musu.Baya da harkokinsa na cikin Jami`a Farfesa Haruna Wakili ya rike Daraktan Cibiyar Nazarin Harkokin Siyasa na Jami`ar wato MUMBAIYA dake Gidan Malam Aminu Kano a Unguwar Gwammajar kano.

" Na zaune bai ga gari ba", wanda bai sanJami`a ba, ba zai san gudunmawar Wakiliba domin a shekaru ashirin da biyar da suka gabata duk dan masarautar Hadejia da ya je Bayero ofishin Wakili ne zangonsa, shi kansa ba zai iya kididdige daliban da ya yi wa hanyar karatu a jami`a ba.

"Mai kamar zuwa kan aika" Yana cikin wannan gwagwarmaya Allah [swt] ya yi masa kwamishinan Ilmi na Jihar Jigawa. wannan mukami nasa duk Bahadeje mai hankali ba zai taba mantawa da shi ba domin baya da ci gaba a gyaran makarantu da samar da aiyuka da matasa da ya yi to kuma a lokacinsa babbar bukatarmu da muka dade muna nema ta neman babbar makaranta ta kai ga biya wato muka samu Jami`ar Kafin Hausa kuma aka gina babbar makarantaraiyukan gona ta Hadejia ta bar lungu ta dawo kan hanya.

Farfesa Haruna Wakili cikakken Bahadeje ne ba ya son raini amma yana da kishin al`ummarsa yana son ci gabansu kuma saboda daga darajar wannan masarauta shi rubutunsa ma na digirinsa na biyu akan wannan Masarauta ya yi.a takaice dai rayuwarsa akan bautawa Ilmi take.Hadejawa suna addu`a Allah Ya ba gwanin yafe gwado.



FARFESA HARUNA BIRNIWA............kamar yadda sunansa ya nuna Farfesa Haruna Birniwa haifaffen garin Birniwa ne kuma yana cikin haular masu mulkin garin.Birniwa shi ne farfesa na farko a cikin wannan masarauta kuma farfesa nabiyu a fadin Jihar Jigawa.

Gaba daya rayuwar Birniwa a kan bautawa Ilmi take domin ya kasance daya daga cikin dattawan malamai a Jami`ar Danfodiyo dake Sokoto na shekaru masu yawa kuma ya rike 'provost' a kwalejin Ilmi dake Gumel sannan ya rike kwamishinan Ilmi a wannan Jiha.

Farfesa Birniwa ya bayarda gudunmawa a fagen bayarda ilmi a Jihar nan matuka domin daruruwan mutane sun ci moriyarzamansa a sokoto domin shi 'admission' a wurinsa kamar mutum ya mari budurwa ne don haka za a ya ce wa shi ne ya budewa Hadejawa kofa a sokoto kuma bai bar sokoto ba sai da ya yi dashe.

Lokacin yana 'provost' ma masu rabo sun samu aiki a wurin.Birniwa ba harkar ilmin zamani kadai ya tsaya ba domin fakihi ne a fannin addini kuma fahintarsa da addini ta kara sa kyawawan halayensa sun kara kyautata domin mutum ne mai hakuri da gaskiya da rikon amana da saukin kai.wani abun sha`awa ga halayensa mai unguwarsa a Hadejia ya ce in dai yana gari duk yadda za a je neman ci gaba da shi ake yi. munaaddu`a Allah ya albarkaci bayansa.

Saturday, March 1, 2014

DAGA NA GABA! HADEJIAWA (PART TWO 2)


DAGA HASHIM AMAR...
MUHAMMAD (ABBAS SECRETARY)- Tsohon Sakataren kananan hukumomin Hadejia, Malam Maduri, SuleTankarkar da Guri; tsohon jami'in kula dajin dadin jama'a, a halin yanzu Akawun Majalisar dokoki ta Karamar Hukumar Guri(Clerk).

Wannan bawan Allah ya taka rawar gani wurin samar wa matasa da dama aikin yia lokacin da yake mukamin Sakatare musamman a Hadejia da Guri. Na san mutane da dama da wannan mutum ya samawa aikin yi, cikin su kuwa har da ni kaina.

HAJIYA SABUWA SHEHU- Shohuwar jami'ar ilmi, tsohuwar shugabar makarantar firamare, tsohuwar Sakatariyar ilmi ta Karamar Hukumar Hadejia; daya daga cikin mata 'yan boko na farko a Kasar Hadejia. Wannan baiwarAllah ta taimaka matuka wurin ci gaban ilmin mata a wannan yanki, ita ce ta dauki mafi yawanmata Malaman Makaranta a Hadejia.

Ta wani bangaren 'yar kasuwa ce da ta samar da aikin yi ga matasa ta wannan bangaren, ita ta kafa shagon gudanar da harkokin sarrafa na'ura mai kwakwalwa (Bussiness Centre)na farko a Hadejia. A yanzu haka 'yar kwamitin kwararru ce masu kula da aiyukan Bankin Duniya a Hadejia. Kuma ta na cikin kwamitin kula da Makarantun Firamare da Bankin duniya suka gina a Hadejia.

Wani abin sha'awa ita ta samar da filin ginin daya Makarantar (Shagari Community), ta nemi filin a hannun Karamar Hukumar Hadejia a  madadin LEA, filin yana hannun ta fiye da shekaru goma. Hajiya Sabuwa ta bayar da tsohongidan ta kyauta ga hukumar ilmi (LEA Hadejia) don gina Makaranta, gidan na unguwar Chadi. Allah Ya saka mata da alkhairi, ya yawaita mana irin ta.