Daga Muhammad Idris..
Wednesday, February 19, 2014
DAGA NA GABA! HADEJIAWA...(part one 1)
*****Ciroman Hadejia Sambo da ne ga Sarkin Hadejia Abdulkadir.Yana daga cikin 'yan boko na farko a Arewa kuma mutum na farko da ya fara zuwa England a Masarautar
Hadejia.Ya rike mukamin Dan Majalissar tarayya a zamaninsa kuma shi ne Babban Dan Majalissar Sarki (senior councillor) a
wannan masarauta.Idan aka yi Tarihin ci gaban kasar Hadejia ba a sanya Ciroma Sambo ba tamkar an yi tuya ba a sa albasa ba ne.
Ciroma Sambo dan ajinsu Sardauna
ne Sir Ahmadu Bello kuma amininsa ne don
haka Sardauna ya yi masa tayin mukamin
minista amma ya ki saboda ya ce "idan na
bar Hadejia to ba za ta ci gaba ba"A takaice
dai ciroman Sambo shi ne kashin bayan ci
gaban Hadejia, a zamaninsa ne aka yi
gagarumin fashin layi wanda ya zama
sanadin titunan da muke gani a cikin gari a
yau kuma zamaninsa ne aka fara ginin
rumfunan kasuwa na bulo.
Zamaninsa aka
fara gina asibiti aka ofisosin gudanarwa da
muke da su,a dai lokacin aka kawo wayar
tangaraho a Hadejia da Malam Madori kuma
Saboda hangen nesa da sanin muhinancin
ilmi ciroma ya tursasawa jama'a su sa
'ya'yansu makaranta wanda wannan ce ta sa
wannan gari ya yi fice a fagen ilmi har a
yau.Wato ba za mu iya kididdigewa aiyukan
marigayi ciroma sambo ba saboda aiyukansa
ya hade masarautar baki daya.
Ciroma
sambo shi ne ya koyawa Sarkin Kano Sunusi
Turanci saboda zamani. Allah ya albarkanci
bayansa domin har yau Hadejia tana cin
gajiyar 'ya'yansa da jikokinsa.Marigayi
ciroma sambo masanin ilmin addini ne da
na zamani,rumfa sha shirgi,mai hannun
kyauta,mai dimancaccen tunani, mai kishin
Hadejia na farko.An haifi marigayi a 1909 Ya
rasu a 1958 wato yana da shekaru arba'in
da tara a duniya kenan. Allah ya sa jannatil
firdausi ce makomarsa.
Amin.
FARFESA MUHAMMAD IBRAHIM YAKASAI
*************** Farfesa Muhammad
Ibrahim Yakasai haifaffan kasar Garin Gabas
ne ta karamar Hukumar Malam Madorin
Hadejia.Ya samu lakabin Yakasai saboda ya
yi karatunsa a gaban yayarsa da ke aure a
unguwar Yakasai ta kano.
Muhammad
Ibrahim yana daya daga cikin manyan 'yan
boko na wannan Masarauta kuma shi ne
Bafulatani na farko da ya samu darajar
farfesa a wannan masarauta.Yakasai ya fara
malamin makaranta a sakandiren wunti da
ke Hadejia na gajeren lokaci sannan ya samu
koyarwa a Jami'ar Bayero da ke kano.
Allah
ya yi masa nasibi a harkar karatu domin ya
kammala karatuttukansa a cikin lokaci
takaitacce.Yakasai yana cikin malamai dake
taimakawa 'yan wannan masarauta da ma
jihar jigawa baki daya wajen samun shiga
jami'a.Baya da daukansu kuma yakan dauki
al'alar taimakawa wajen warware matsalar
da duk wani dalibi ya shiga cikin
jami'a.Yakasai mutum ne mai fara'a,mai
saukin kai,mai sanin yakamata,Karatunsa
bai sa ya dauki duniya da zafi ba.Muna
masa addu'ar zama vice chancellor nan
gaba. Hadejia A yau...
Wednesday, February 5, 2014
EMIRE OF HADEJIA ALH.HARUNA ABDULKADIR.
But while previously, during colonial period, the Tafida administered Kafin Hausa as district head, until more recently when it was given to Chiroma, a son to the Emir. Fallowing Chiroma’s appointment as a chairman of the Kano state local government service commission he was unfortunately obliged to reside at Kano city, leaving Kafin Hausa to be administered by his deputy while he retain the title.
The old emirate council from 1971 – 1975meet more frequently under the chairmanship of the Galadima Yusuf and Adamu, the major responsibilities of that administration rested firmly with Dan’iya,M. abdulkadir Maidugu, himself a grandson a grand of the Emir Abdulkadir and formally Sarkin Auyo and district head of Auyo, he represented HADEJIA inthe Federal House of Assembly. In his return after the abolition of a civilian rule, he was appointed Senior Executive Councillor of the Emirate council in charge of finance, the native administration,works, rural water supplyand community development.
TheTafida alh. Abdulkadir Maigari, another grandson of the emir Abdulkadir was appointed a councillor in charge of Agric and Natural resourses.The Danburan muhammadu Hurdi……………….
.(Culled from “Local Government at Hadejiia 1977” By M. G. Smith)
By Ma'aji I Abubakar.