Saturday, April 27, 2013

TAURARINMU HADEJIAWA (4)

Image Hosted by ImageTitan.comHadejia A yau! Allahu Akbar!

ALH. ABDUL'AZIZ DANMASAGA :- Hakika Tarihin Hadejia bazai manta da wannan bawan Allah ba, yayi iya kokarinsa wajen taimakon rayuwar mutanen kasar Hadejia, musamman Talakawa Masu karamin karfi da Miskinai.

Yayi Amfani da Arzikin da Allah ya bashi ya kyautatawa Jama-ar kasar Hadejia. Allah ya gafarta masa.

Alh. Abdu Danmasaga Mutum ne mai fara'a da son ci gaban Al'umma, baya so yaga mutane suna zaman banza. Hakan tasa yake daukan mutane ya sanyasu Inda zasu koyi sana'a domin su dogara da kansu. Shine mutuminda duk ranar Juma'a ko Lahdi yake raba kudi ga 'yan makarantar Boarding, saboda yasan basa kusa da Iyayensu.

Ga kadan daga Ayyukansa da yayi na Alheri.

(1) yana sayen itace mota mota ana faskarawa a tarashi kuma a saidashi lokacin da yayi wahala akan kudi kadan.

(2) Ba'a fara sayan Itace ba a Makabarta sai bayan mutuwarsa, saboda ya bada fisabilillah. Allah yasa yana Aljannah.

(3) yana saida kalanzir a kankanin farashi musamman lokacinda watan Azumi ya karato ko kuma lokacin Damina.

(4) yana saida fetur a farashi mai sauki yayinda ake wahalar sa. Ko ya zama babu a gari.

(5) shi yake sakawa ayiwa Mahaukata Aski, ya basu Abinci kuma ya dinka musu sabbin Riguna.

Dama ace masu kudi ko 'yan siyasa zasu koyi hali Irin nasa, da kasa ta kwana lafiya!

Allah ya Gafarta masa, Allah yasa mu koyi Hali Irin nasa. Alh. Abdul'aziz Danmasaga. Hadejia A yau.

Sunday, April 21, 2013

TARIHIN SARKIN HADEJIA UMARU DAN BUHARI DA ZUWAN SARKIN DAMAGARAM HADEJIA..

Image Hosted by ImageTitan.comHADEJIA A YAU!



SARKIN HADEJIA UMARU: A SHEKARAR 1863 allah ya yiwa Sarkin Hadejia Buhari rasuwa a Yakinsu da sukayi da Gogaram (bade). Ko da aka dawo Hadejia aka binne shi sai Manyan fadawan Hadejia wadanda akwai Amana tsakaninsu dashi Buhari. Kamar SARKIN AREWA TATA GANA DA SARKIN YAKI JAJI suka jajirce Sai an Nada UMARU DAN BUHARI SARKIN HADEJIA. kuma hakan Akayi!


SARKIN HADEJIA UMARU NA BIYU an nadashi yana da shekara Goma sha Takwas (18). Kuma manyan fadawan Mahaifinsa sune suke gudanar da Sarautar tunda shi yaro ne. Kuma a zamaninsa Sarkin Damagaram Tanimu ya kawo yaki Hadejia. Kuma yayi sansani a Arewa da Hadejia daga nan har Jigawar Kasim mutanensa ne. saida yayi kwana Arba'in ana yaki amma Hadejiawa basu fasa wasanninsu na dandali ba. Sannan kuma basu fasa duk harkokinsu na kasuwa ba, su kuma mutanen Sarkin Damagaram suna kaiwa farmaki kauyuka suna kwace musu kaya! Sannan sun hana mutanen kauyuka shigowa Hadejia domin saye da sayarwa. A nan kuma sun hana Makiyaya kiwon Dabbobinsu, Sai sarkin Arewa yasa akayi sanarwa a Hadejia cewa: duk mai dabbobi gobe ya sako su za'a kaisu kiwo, kuma hakan sukayi suka saki dabbobinsu Sarkin Arewa da Mutanensa sukaje sukayi kiwon suka dawo. Ta wajen Dan-Rago kusa da Maficin Sarki.

Da Abin ya ishi Mutanen Hadejia sai suka Sanar da Sarkin yakin Hadejia Jaji, sai ya tara Fadawan Hadejia yace Naji ance Sarkin Damagaram yazo, Yau wajen kwana 40, sukace hakane! Sai sarkin Yaki yace so kuke yazo ya koremu daga Garin?

Da safiya tayi sai sarkin yaki Jaji ya hau dokinsa ya dauki Takobinsa ya fita yacewa sarkin Kofa in ya fita ya rufe Kofar Gari, kuma ko an koroshi karya sake ya bude, idan ya bude masa to zai kashe shi. Sarkin yaki Jaji yaje ya fara baza Mayakan sarkin Damagaram yana korasu, saida ya korasu har Rumfar Sarkin Damagaram ya dawo da niyyar Washegari aci gaba da yaki.

Da sarkin Damagaram yaga anyi haka sai ya tara Hakimansa da fadawa yace gobe zamuci Hadejia da yaki. Suka amsa suna Alwashi, bayan an baje sai Chiroman Damagaram ya samu sarki yace masa Shawara nazo in bayar, sarki ya yarda. Chiroma yacewa Sarkin Damagaram duk garin da mukaje musu yaki basu da sukuni saboda suna tsoronmu, Amma yau kwananmu Arba'in (40) Hadejiawa basu fasa duk abinda sukeyi ba! Kuma mun samu Labarin Sarkin Hadejia bai san munzo ba, yacewa sarki Ina ganin ya kamata ko mu shiga mu yakesu ko kuma mu koma Gida!

Wata rana ana yaki Sai aka harbi dokin Sarkin Arewa! Koda ya mutu sai akaje gida aka dauko wani Dokin aka cire kayan wancan Dokin aka sakawa wanda aka kawo. Tata gana ya koma kan doki, kashe gari ana cikin yaki sai Tata gana ya sauko daga Dokinsa yayi alwala ya koma kan Dokin, to ashe Sarkin Damagaram yana kallon su sai yace Lalle Sarkin Hadejia ya Isa ana yaki ka sauko kayi alwala? Jiya ma an kashe masa Doki amma saida akaje aka dauko wani a gari? Sai Zagin Sarkin Damagaram yace ai ba Sarkin Hadejia bane Yaronsa ne! Sai Sarkin Damagaram Tanimu yace to Ina Sarkin Hadejian? Sai zaginsa yace ai ance yana gida tunda aka fara yakin nan bai taba zuwa ba. Sai sarkin Damagarm yace wa fadawansa Gobe zamu bar Hadejia kar mu tsaya ayi ta kashemu. Saboda Sarkin Hadejia ya raina mu kwananmu Arba'in amma bai taba zuwa anyi yaki dashi ba? Wa yasan me zai mana in ya zo? Amma basu san Sarkin Yaro bane. Washe gari suka juya suka koma Damagaram. Kuma lokacinda sukazo Hadejia Da kaka ne! Anyi girbi Manoma basu gama Tare Amfaninsu ba. Shi yasa suka dade a Hadejia saboda akwai abinci da ruwa a kusa dasu.

SARKIN HADEJIA UMARU Mutum ne mai son Nishadi kowane Lokaci yakan fita Bakin kogi ko Gona Domin Debe kewa. Kuma anyi amfani da wannan Damar inda wata rana ya fita sai aka Rufe Masa Kofa. Koda yazo yaga kofa A rufe sai ya juya ya tafi Chamo ya zauna. Aka nada Kanin Mahaifinsa Sarkin Hadejia Wato HARU BUBBA. 1865-1885. Shi kuwa UMARU DAN BUHARI yayi zamansa a Chamo kuma Ya rasu a shekarar 1920. Allah yaji Kansu Ameen.

HADEJIA A YAU.

Friday, April 5, 2013

KHUDUBA DAGA MASALLACIN FANTAI HADEJIA...

Image Hosted by ImageTitan.comHADEJIA A YAU! Daga Yaya Ilallah.


~~~ZUWA WAJEN BOKA~~~


Alhamdulillahi Rabbil Alamin. Muna farawa da sunan Allah wanda da Ikonsa komai ya kasance, da kuma Abinda zai kasance! Tsira da Aminci su tabbata ga Manzonsa Muhammadu s.a.w. Wanda ya aikoshi da zance mafi dadi wato Alqur-ani.


Alhamdulillahi Yau khuduba daga Masallacin Usman Bn Fodio dake cikin makarantar Fantai daga bakin Mal. Bashir Muhd Baima, ta yi magana ne ga hani zuwa wajen:- BOKA ko YAN TSUBBU. Wadda a lokacin yanzu shedan ya kada gangarsa wajen haska zukatan ashararu daga cikin mutane kamar 'yan siyasa, masu mulkin gargajiya da na gwabnati da kuma masu rike da wasu mukamai.


Manzon Allah s.a.w yace: Duk wadda ya je wajen Boka, ba za a amsa masa Sallarsa ta kwana 40 ba. In kuma ya yi imani da abun da ya fada, to ya kafurta da abun da Annabin ya zo da shi. Wani abu mafi muni da takaici, za ka ga matasa maza da mata na neman taimakon Bokaye wai da sunan Farin jini, neman mulki, mallakar miji da kokarin mallakewa zuciyar abokin soyayya ga samari da 'yan mata.


Haka dabi'ar ta kara watsuwa cikin zukatan wasu jahilai ta yadda in wani abu na musiba ya samesu , sai su tafi ga Boka don gano yadda wannan abu ya faru a gareshi. Ya manta da Allah ne ya Qaddara masa. Toh Allah kyauta.


Masu irin wanga dabi'a Allah shiryesu, mu kuma Allah ya karemu. Amen.