Saturday, September 29, 2012

GAMON KAFUR

HADEJIA A YAU!
Bayanda Sarkin Hadejia Buhari da jarumansa suka kare Yakin Takoko inda kuma anan ne Allah yayiwa sarkin Hadejia Ahmadu Rasuwa Inda wani Jarumin Buhari mai suna Barde Risku ya kasheshi. Dukda Umarnin da Buhari ya bayar cewa kar a kasheshi, Buhari da jarumansa sai suka shigo Hadejia wato ya zama shine Sarkin Hadejia. Sarkin Hadejia Buhari ya Rubuta wasika Zuwa ga Sarkin Musulmi, ya masa Ta'aziyyar Sarkin Hadejia Ahmadu, kuma ya nuna cewa yanzu shine Sarkin Hadejia yana neman sarkin Musulmi ya amince dashi. Kuma hakan bata samu ba.


Sarkin Musulmi Alu Bubba
sai ya gayyaci duk sarakunan dake
Karkashin Daular sokoto da su hadu su
yaki Buhari. Ko a kamashi da rai ko a
kashe shi. Wannan kuwa ta faru ne a
shekarar (1853). An hada wannan
rundunar yakin ne karkashin Jagorancin
Galadiman Kano Abdullahi maje Karofi
kafin ya zama Sarkin Kano. An gayyaci
mayaka a Garuruwa daban daban kamar
Kano,zamfara,Bauchi,Katagum,Misau,zaria
da sauran garuruwan Daular Sokoto.


Masana tarihi sunce an tara mutum A kalla
Dubu Ashirin (20,000) Abdullahi Maje
Karofi ya Umarci Sarkin Miga da ya zame
musu Jagoran Tafiya, ganin cewa ya fisu
sanin Kasar Hadejia saboda Iyakarsu daya.
Koda suka shirya sai aka Umarcesu da su
shiga Hadejia ta Kudu Maso Yamma, wato
kar su shiga kai tsaye ta yamma. Akan
Hanyarsu ta zuwa Hadejia ne Sai suka
Yada Zango a Kafur, kusa da Hadejia.
Domin su kwana da safe su shiga Hadejia
su Yaki Sarki Buhari. Sai dai da zuwansu
Kafur Buhari ya samu Labari, Ance wani
makiyayi ne yana kiwo ya Gansu, kuma
Har ya bar gurin baiga Iyakarsu ba. Sai ya
rugo ya sanarda Sarki Buhari Abinda ya
gani. Sai Buhari ya Umarci Mayakansa
cewa "Tunda ance Basu da iyaka kuma ga
Magariba ta shigo, mu shirya muje mu
shiga cikinsu ba tare da sun ganemu ba"
hakan sukayi yace Duk Lokacinda sukaji
Dan fatima ya Buga Ganga to su fara
Bugun mayaka.

Haka akayi Mayakan
Buhari suka shimmace su suka shiga
cikinsu ba tare da sun gane ba,Saboda
Garuruwa da dama ne suka Hadu. Ance
wasu mayakan nasu Dauresu akayi wai
dan kar su shiga Hadejia kafin Gari ya
waye. Ashe Ajali ne ya dauresu.
Koda Sarkin Hadejia Buhari yayi shirinsa
yayi Addu'ah sai ya Daga Kai sama.
Sai Dan-fatima ya zuba Kirari:-

(Fasa maza dan
Sambo, Garba Bakin Tandu da Man Madaci,
wanda ake jira yazo, fasa Maza gagara
gasa, sai ya buga Gangar yaki).

Anan
Mayakan Hadejia suka fara bugun
mayakan Daular Sokoto suna kashewa.
Wadansu duk suka razana suka fita a guje
kowa yana kokarin ya ceci Ransa.
Wadanda aka dauresu dan kar su shiga
Hadejia da wuri, duk anan aka kashesu.
Sauran kuwa suka zubar Makamansu suka
Gudu. Dawakai suka Razana, su kuwa
mayakan Hadejia Suna bi suna kashewa
suna kama Bayi.

2 comments:

  1. Fasa maza dan sambo! Garba bakin tandu da man madachi.

    ReplyDelete
  2. Abubakar magajin Sambo.

    ReplyDelete