Friday, September 23, 2016

HADIN GWUIWA DA TAIMAKEKENIYA. Daga Abdullahi Matashi...



A bisa dabi’a kowane mutum yana da wata baiwa da ya kebantu da ita, kuma kowane mutum yana bukatar taimakon sauran mutane domin ya kai ga kamala da ci gaba.

Hadin gwuiwa abu ne da ke da tasiri matuka wajen ci gaba da cin nasara ga daidaikun jama’a da kuma al’umma baki daya. Allah Ya halicci mutum da dabi’ar zaman tare, Saboda haka a bisa dabi’a yana ta kokawar warware mishkiloli ne na rayuwa tare da sauran mutane ‘yan-uwansa.

Dabi’a da kuma bukatun mutum
su kan haifar masa da mishkiloli
dabam-dabam, dan haka shi ko
yaushe karen barar mishkiloli ne
masu tsanani. A cikin wannan hali na tsanani da bala’i ba zai taba koshi daga taimakon wadansu ba. A bisa wannan dabi’a da larura ne ayyukan da suka rataya a wuyan jama’a na kowace suka sha bam- bam. Taimakon da mutum guda
zai ba wa al’umma kome kankantarsa zai taimaka wajen
cigaban al’ummar da kammala
rayuwarta.

Tunda yake halayyar al’umma
ta ginu ne a jikin daidaikun mutane, to muna iya kamanta al’umma da bangarorin jikin mutum. Kamar yadda jikin mutum ya kunshi gabobi
dabam-dabam wadanda ke da alaka da juna wajen dorewar rayuwar mutum. Tilas ne kowace gaba ta gudanar da aikin da aka dora mata ba tare da ketare haddinta ba, haka nan al’umma ma an gina ta ne da
daidaikun mutane kazalika
dorewar al’umma yana bukatar
kowa ya san aikin da ya rataya
a wuyansa kuma ya aikata shi
iyaka karfinsa da iyawarsa.

Lalle ne kowa ya yi amfani da abin da ya mallaka na dukiya da hazaka dan tafiyar da al’umma da kyautata ta da habaka ta tare da tsayawa a kan iyakar aikinsa da aka dora a wuyansa gwargwadon fannin aikinsa da karfinsa. Dukda haka kuma ana iya samun kwanciyar hankali da zaman lafiya da jin dadi, a kuma yi galaba akan mishkilolin rayuwa ne a al’umma idan akwai kaunar hadin gwiwa a tsakanin mutane. Ta hanyar taimakon juna ne kawai rayuwa za tayi zaki, bishiyarta kuma za tayi ‘ya’ya har a samu a ja ragamar rayuwa zuwa gaba.
ABDULLAHI MATASHI...

Tuesday, July 28, 2015

Hadejia A yau.

A satin da ya gabata ne mai girma gwamnan Jihar Jigawa Alh. Badaru Abubakar,  ya sanar da Daga darajar Bubbar Asibitin Hadejia zuwa Specialist Hospital. Sannan ya daga darajar Asibitin Birniwa zuwa General Hospital,  kasar Hadejia tana da kananan hukumomi guda takwas da gundumomin Hakimai Ashirin da biyar,  amma a baya suna  amfani ne Bubbar Asibiti guda daya kafin zuwan gwamnatin Sardauna.

Da yake nasa jawabin mai martaba sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar ya bayyana godiyarsa ga gwamnan Jihar jigawa, a madadin Al'ummar masarautar Hadejia,  kuma ya tabbatar da baiwa gwamnati hadin kai da goyon baya domin yiwa Al'umma aiki.

Da yake maida jawabi Gwamnan. Na jigawa ya bayyana Al'ummar kasar Hadejia da cewa sune silar zammansa gwamna a jigawa, domin sune  wadanda suka bada kaso mafi girma a kuri'ar da ta kaishi ga zama gwamna..  Gwamnan yace gwamnati zata ci gaba da cika Alkawurran da ta dauka lokacin yakin neman zabe.