Thursday, October 6, 2016

(15) SARKIN HAƊEJIA ABUBAKAR MAJE HARUNA




Bayan rasuwar Sarkin Haɗejiya Alhaji Haruna sai aka naɗa Ɗansa Alhaji Abubakar Maje Haruna a matsayin Sarkin Haɗejiya na goma sha biyar (15), A jerin sarakunan Fulani, an naɗashi ranar Alhamis 30/august/1984. Sai akayi Sarki mai farin jini da hakuri da son mutane, a wajen kyauta kuwa ya kasance mai Alheri tun yana ƙaraminsa. Sarkin Haɗejiya Abubakar kafin zamansa sarki yayi Ayyuka da dama, sannan ya kasance Ɗan kasuwa. 

A zamaninsa an samu sauye sauye da dama a ƙasar Haɗejiya, musamman Ɓangaren Ilmin Addini dana zamani Kasuwanci da siyasa. Sarkin Haɗejiya Abubakar Maje ya halarci makarantu da dama inda ya fara halartar makarantar Elementary dake Unguwar Dallah a shekarar 1945, sannan ya tafi makarantar Middle School dake Unguwar fantai a shekarar 1949 zuwa 1952. Haɗejia A yau.

Sarkin Haɗejiya Abubakar ya tafi makarantar T.T.C. Maru dake a Lardin Sokoto a wancan lokacin, ya fara a cikin shekarar 1953 zuwa 1956. Sarkin Haɗejia Abubakar ya koma makarantar horar da ma’aikata dake Potiskum ta jihar Borno, wadda yanzu take a jihar Yobe. Kuma ya fara aikin gwamnati a matsayin Malamin Hakimi a Gundumar Bulangu, sannan ya riƙe muƙamin Magatakarda a majalissar Sarki. Saboda iya mu’amala da son jama’a sai yazama duk inda ka ganshi bazaka ganshi shi kaɗai ba sai da jama’a, hakan ya bashi nasarar gogewa wajen tafiyar da shugabancin jama’a. Haɗejia A yau.

A zamaninsa an samu ci gaba da yawa a ƙasar Haɗejia ta kowane fanni na rayuwa, musamman zaman lafiya da Kwanciyar hankali, sannan an samu bunƙasar garin Haɗejia wajen gine ginen zamani da gina sabin Unguwanni. A zamaninsa aka rushe ƙofar Garin Yamma da ta Arewa aka Gina sabi domin dacewa da zamani sannan aka sake gina Sabi guda uku, an gina ɗaya a Kusa da Kadime ɗaya kuma an ginata a hanyar Gumel da kuma hanyar Nguru. A zamaninsa an gina sha tale-tale (Round about) guda biyu ɗaya a yamma da kofar garin yamma, ɗaya kuma a Titin Tashar mota tsohuwa, sannan anyi sababbin hanyoyin mota a ciki da wajen Haɗejia. A zamaninsa....... Hadejia A yau! A duba littafin Fulani da mulkinsu na Ismaila A Sabo.

HADEJIA A YAU!

Friday, September 23, 2016

HADIN GWUIWA DA TAIMAKEKENIYA. Daga Abdullahi Matashi...



A bisa dabi’a kowane mutum yana da wata baiwa da ya kebantu da ita, kuma kowane mutum yana bukatar taimakon sauran mutane domin ya kai ga kamala da ci gaba.

Hadin gwuiwa abu ne da ke da tasiri matuka wajen ci gaba da cin nasara ga daidaikun jama’a da kuma al’umma baki daya. Allah Ya halicci mutum da dabi’ar zaman tare, Saboda haka a bisa dabi’a yana ta kokawar warware mishkiloli ne na rayuwa tare da sauran mutane ‘yan-uwansa.

Dabi’a da kuma bukatun mutum
su kan haifar masa da mishkiloli
dabam-dabam, dan haka shi ko
yaushe karen barar mishkiloli ne
masu tsanani. A cikin wannan hali na tsanani da bala’i ba zai taba koshi daga taimakon wadansu ba. A bisa wannan dabi’a da larura ne ayyukan da suka rataya a wuyan jama’a na kowace suka sha bam- bam. Taimakon da mutum guda
zai ba wa al’umma kome kankantarsa zai taimaka wajen
cigaban al’ummar da kammala
rayuwarta.

Tunda yake halayyar al’umma
ta ginu ne a jikin daidaikun mutane, to muna iya kamanta al’umma da bangarorin jikin mutum. Kamar yadda jikin mutum ya kunshi gabobi
dabam-dabam wadanda ke da alaka da juna wajen dorewar rayuwar mutum. Tilas ne kowace gaba ta gudanar da aikin da aka dora mata ba tare da ketare haddinta ba, haka nan al’umma ma an gina ta ne da
daidaikun mutane kazalika
dorewar al’umma yana bukatar
kowa ya san aikin da ya rataya
a wuyansa kuma ya aikata shi
iyaka karfinsa da iyawarsa.

Lalle ne kowa ya yi amfani da abin da ya mallaka na dukiya da hazaka dan tafiyar da al’umma da kyautata ta da habaka ta tare da tsayawa a kan iyakar aikinsa da aka dora a wuyansa gwargwadon fannin aikinsa da karfinsa. Dukda haka kuma ana iya samun kwanciyar hankali da zaman lafiya da jin dadi, a kuma yi galaba akan mishkilolin rayuwa ne a al’umma idan akwai kaunar hadin gwiwa a tsakanin mutane. Ta hanyar taimakon juna ne kawai rayuwa za tayi zaki, bishiyarta kuma za tayi ‘ya’ya har a samu a ja ragamar rayuwa zuwa gaba.
ABDULLAHI MATASHI...