A satin da ya gabata ne mai girma gwamnan Jihar Jigawa Alh. Badaru Abubakar, ya sanar da Daga darajar Bubbar Asibitin Hadejia zuwa Specialist Hospital. Sannan ya daga darajar Asibitin Birniwa zuwa General Hospital, kasar Hadejia tana da kananan hukumomi guda takwas da gundumomin Hakimai Ashirin da biyar, amma a baya suna amfani ne Bubbar Asibiti guda daya kafin zuwan gwamnatin Sardauna.
Da yake nasa jawabin mai martaba sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar ya bayyana godiyarsa ga gwamnan Jihar jigawa, a madadin Al'ummar masarautar Hadejia, kuma ya tabbatar da baiwa gwamnati hadin kai da goyon baya domin yiwa Al'umma aiki.
Da yake maida jawabi Gwamnan. Na jigawa ya bayyana Al'ummar kasar Hadejia da cewa sune silar zammansa gwamna a jigawa, domin sune wadanda suka bada kaso mafi girma a kuri'ar da ta kaishi ga zama gwamna.. Gwamnan yace gwamnati zata ci gaba da cika Alkawurran da ta dauka lokacin yakin neman zabe.