A yau ne ake rantsar da sabuwar majalissar dokoki a Jihar Jigawa, bayan da aka rantsar da 'yan majalissar kuma sun gabatar da zaben kakakin Majalissar da mataimakinsa, Wanda aka zaba din dai a Matsayin Kakakin Majalissar shine.... Hon. Idris Garba Kareka daga karamar hukumar Jahun. Dan majalissar dokoki ta jiha mai wakiltar Karamar hukumar Gumel Hon. Sani Isyaku Abubakar ne, ya gabatar da Sunan Idris Garba a matsayin wanda yake goyon baya ya shugabanci majalissar, yayinda kuma ya samu goyon baya ga Dan majalissa mai wakiltar Kiri kasamma Hon. Aliyu Muhammad Aliyu, sai sauran 'yan Majalissar suka Amince da hakan ba tare da hamayya ba.
Haka kuma An zabi Hon. Ahmed Garba (MK) mai wakiltar Hadejia, a matsayin mataimakin kakakin majalissar Jiha, shima dan majalissa daga mazabar Birnin kudu ne ya gabatar da sunansa, daga bisani ya samu Amincewar sauran 'yan majalissar. Allah ya basu ikon sauke nauyin da aka dora musu.