Monday, September 29, 2014

TARIHIN RAYUWAR GALADIMAN KANO A TAKAICE! Alhaji Tijjani Hashim.

Hadejia A yau!<p>An haifi Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim a cikin garin Kano, a shekarar 1932. Mahaifinsa shine Turakin kano Hashim dan sarkin kano Abbas jikan sarkin Kano Ibrahim Dabo. Ya fara karatun Elementary  a garin Bebeji a cikin shekarar 1944. sannan ya shiga makarantar Middile ta Kano inda ya kammala a  shekarar 1951.

A shekarar 1952 Galadiman kano ya fara aiki a  hukumar N. A. (Native Authority) ta Kano a matsayin Malamin Dabbobi, mai kula da tsafta da lafiyar dabbobi. A 1956 aka zabe shi  a matsayin dan majalissa mai wakiltar Sumaila a majalisar dokoki ta Arewa dake kaduna.

A zaman sa a wannan majalisa ne ya rike mukamai da dama ciki har da shugaban hukumar bada kwangila ta Kaduna sannan ya rike shugaban kwamitin tabbatar da jamiyyar NPC ta lashe zabe a lardin Sardauna. Sannan ya rike mukamin Ministan Ayyukan cikin gida na Jihar Arewa. Yayi Kwamishinan lardi mai kula Lardin Kabba wandda yana kan wannan mukamin ne sojoji suka yi juyin mulki.

Bayan ya dawo gida sai  Sarkin Kano Ado Bayero ya nada shi sarautar Dan-isan Kano kuma kansila mai kula da ayyukan gayya da taimakon kai da kai.

A cikin shekarar 1976 ne ya samu karin girma zuwa sarautar Turakin Kano da bashi kulawa da gundumar Kumbotso. sannan A 1980, ya sami canji zuwa kansila marar ofis saboda yawan  harkokinsa na kasuwanci. A shekarar 1989, ya samu karin girma zuwa sarautar Dan-iyan Kano, kuma ya ci gaba rike mukamin kansila marar ofis.

A shekarar 1992, ya samu karin girma a sarauta inda aka nadashi Galadiman Kano kuma shugaban kwamitin kudi na majalisar Sarki. A shekarar 2012 Sarki ya kara masa aikin hakimcin birnin Kano. Wannan aiki ya ke rike dashi har Allah ya masa rasuwa.

Galadiman Kano Tijjani mutum ne mai hakuri da juriya da Alkairi. Kuma yana da daraja a Idanun mtane sakamakon amfani da yayi da damarsa ya kafa mutane a Gwamnati. kuma babu inda zai nemi Alfarma a gwamnati bai samu ba, wannan tasa ake masa Laqabi da GAJERE WAN GWAMNATI.

A ranar28/september/2014, Allah ya yiwa Galadiman kano rasuwa ya rasu ya bar 'ya'ya da Matan Aure da 'yan-uwa da dama. Muna Addu'a Allah ya gafarta masa.