HADEJIA A YAU! Sallar Mauludi ko Gani a Hadejia ya samo asali ne shekara 90 da suka gabata, wato 1910-1925. A lokacin Sarkin Hadejia Abdulkadir aka fara hawan Mauludi ko Gani a Hadejia, kuma ya kirkiro wannan hawa na Gani ne daidai sabuwar shekarar Musulunci, a Inda yake Ganawa da Hakimansa na waje (District heads) domin suyi jawabin Nasarori da Matsalolinda suka samu a kasarsu a shekararda ta gabata.
Saboda bikin yazo daidai da shekarar Mauludin Manzon Allah (s.a.w.) Sarkin Hadejia Abdulkadir sai yakan hau da Yamma tare da Hakimansa kamar yanda abin yake har yanzu. Kuma a ranar da safe akan gudanarda bukukuwa na Nadin sarautar Hakimi idan ta kama. Sarkin Hadejia Abdulkadir yakan yi hawa da hakimansa inda ake zagaya gari kuma a lokacin yakan bi ne ta Unguwanninda suke da Tsangaya domin ya taya Malaman murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (s.a.w.).
Kamar yanda Abin yake har yanzu Sarki zai fito daga fadarsa da yamma, zai bi ta Tudun mabudi ta Kasuwar kuda sannan yabi ta Kasgayama zuwa Kwarin madaki, sai ya fito ta bayi zuwa Magama hudu zuwa Unguwar Dukawa zuwa Hudu, sannan zai wuce ta Tagurza zuwa Majema zuwa bakin kasuwa, sannan sai ya biyo ta Makwallah zuwa Baderi zuwa Kofar Liman. Sannan ya koma fadarsa. Hadejia A yau.