
Hadejia a yau!
A ci gaba da kawo muku tarihin wadanda suka bada Gudun mawa a Kasar Hadejia, yau Aji kima ya kawo mana Kadan daga Irin Gudunmawar da Alh. Tijjani Dodo yake bayarwa!
Dattijo Alhaji Tijjani Dodo Hadejia.
Dan Baiwa ne.
Wanda ba kowa ya san hakan ba.
Wannan mutumin baya kasa a gwiwa ganin
al'uma sun ci gaba.
Wannan yasa ya wajabtarwa kansa fafatawa
a harkokin rayuwa daban-daban domin
samarwa al'uma mafita.
Duk gun da ka leka zaka hango shi.
1.Dan kasuwa ne,
2.Dan siyasa ne,
3.Ba sarake ne,
4.Dan kungiyar aikin gayya ne,
5.Dan kungiyar Achaba ne,
6.Dan kungiyar matasa ne,
7.Dan kungiyar yan kasuwa ne,
8.Dan kungiyar ma'aikatan gwamnanti ne
9.Dan kungiyar kwallon kasa ne,
10.Dan kwamatin hawan sallah ne,
11.Dan kwamatin gyaran makabirta ne.
12.Dan kwamatin jinga ne,
13.Dan kwatin gayaran masallaci
14.Dan kwamatin gyaran gari.
15.Dan kungiyar raya al'adun Gargajiya.
Yanzu haka shi ne shugaban aikin gayya na
Hadejia,
shi ne kuma shugaban yan Achaba,
haka kuma dogari ne a fadar Hadejia. Lalle Juyi Goma sai Wake Inji masu Iya magana.
A hannu daya kuma dan siyasa,dan kasuwa.
Jama'a ya kamata mu jinjinawa wannan
bawan Allah,Allah ya bamu dubu masu amfani
irinsa.
Wannan hotonsa ne yana bada hannu.
Bai yadda yaga abu bai yi iya bakin kokarinsa
ba.
Idan na magana ne zaiyi idan da karfinsa ne
zaiyi idan da aljihunsa ne sai yayi.
Allah ya saka da alherinsa.